Wallahi dabba tafi Buhari hankali da tunani, Martanin wani matsahi kan mulkin Buhari


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MASU MULKI KU 'DAU DARASI DAGA MULKIN ANNABI SULAIMAN (A. S) 


Cikin halittun Allah (T) wadanda yayi musu qafafu kuma masu motsawa daga wannan guri zuwa wannan guri masu ci da sha da kuma haihuwa bai yi wata halitta marar hankali da tunani kamar Dabba ba. Sai dai kuma duk da irin wannan rashin hankali da tunani na Dabbobi bai hana Allah fitar da wasu daga cikinsu wadanda suka fi 'Dan Adam hankali ba, domin suna iya kaucewa abinda suka san zai iya cutar dasu kuma sukan bada kariya ga 'ya'yansu da kuma 'yan'uwansu. 


Shi kuwa 'Dan Adam shine halitta wacce Allah ya halitta kuma ya fifitata akan dukkan wata halitta mai iya motsi daga wannan guri zuwa wannan guri. Sannan kuma ya fifita su ta bangaren hankali, tunani da ilimi. Sai dai kuma duk da wannan fifiko da yayi musu sai ya fitar wasu daga cikinsu wadanda Dabbobi 🐮 🐴 🐐 suka fi su ilimi, hankali, tunani da kuma hangen nesa. 


Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda Dabbobi suka fi su hankali, tausayi da sanin muhimmancin rai a gangar jiki. Kowa zai iya sanin haka tare da gaskata ni idan ya nazarci rayuwar wata Dabba ko qwaro 🐜 ya kuma auna ta da rayuwar Muhammadu Buhari. 


TURURUWA 🐜 A MATSAYIN ABIN MISALI 


Anyi wani zamani wanda Allah ya tayar da Annabi Sulaiman (A. S) kuma ya maida shi wani Sarki mai mulki wanda ba a taba samun mai qarfin mulki irinsa ba, domin shi kadai ne ya taba mulkar 'yan Adam, Aljannu da kuma Dabbobi baki daya masu gudanar da komai a qarqashinsa kuma bisa umarninsa. 


Wata rana Annabi Sulaiman (A. S) ya fito da rundunarsa ta mutane da Aljannu sai wata Tururuwa 🐜 ta hango su daga nesa, nan take tayi kiran gaggawa ga 'yan'uwanta kan cewa maza su gaggauta shiga cikin gidajensu don kada wannan runduna subi ta kansu su karkashe su ba tare da saninsu ba. Shine Allah (T) ya bamu labari da cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



وَحُشِرَ لِسُلَيۡمَٰنَ جُنُودُهُۥ مِنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ وَٱلطَّيۡرِ فَهُمۡ يُوزَعُونَ (٧١) 


" KUMA AKA TATTARA GA SULAIMANU RUNDUNA DAGA ALJANNU DA MUTANE DA KUMA TSUNTSAYE SUNA BASHI KARIYA. "


حَتَّىٰٓ إِذَآ أَتَوۡاْ عَلَىٰ وَادِ ٱلنَّمۡلِ قَالَتۡ نَمۡلَةٞ يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّمۡلُ ٱدۡخُلُواْ مَسَٰكِنَكُمۡ لَا يَحۡطِمَنَّكُمۡ سُلَيۡمَٰنُ وَجُنُودُهُۥ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ ٨١

 

" HAR YAYIN DA SUKA JE AKAN TAFKIN (ramukan) TURURUWA SAI (wata) TURURUWA TACE, " YAA KU TARON TURURUWA ! KU SHIGA CIKIN GIDAJENKU DON KADA SULAIMAN DA RUNDUNARSA SU TATTAKE KU ALHALI BASU SANI BA. "


Wannan ita ce Tururuwa 🐜 wacce take da hankali da tausayi da imani wacce ta bawa 'yan'uwanta kariya daga cutuwa ta hanyar umartarsu da su shiga cikin gidajensu. Kuma hakan suka yi har ya zama kariya gare su. 


       MUHAMMADU BUHARI 


Mutum kenan wanda Dabba ta fi shi hankali da tunani. Shi ke mulkar al'ummar Nigeria amma kuma ya zama maimakon ya bada kariya ga rayukansu sai ya kasance shi yake karkashe wadanda yake mulka da hannunsa, abinda ya faru a Zaria babban abin misali ne. Sannan kuma sauran al'ummar da ake karkashewa da sunan Boko Haram ko Kidnapping a jihohin Zamfara, Borno da sauran dukkan sassa na wannan qasa ba tare da ya dau mataki ba ya tabbatar mana cewa Dabba ta fi shi hankali. 


Wanda ke musu kan wannan magana sai ya fada mana wanne irin mataki ya dauka na kare lafiya da rayukan al'umman Nigeria wanda aka shafe aqalla shekaru shida (6) ana yi a mulkinsa. 


ANNABI SULAIMAN (A. S) A MATSAYIN ABIN MISALI 


Annabi Sulaiman (A. S) ya koyar damu yadda ake mulki na adalci ta hanyar bibiyar kowa akan matsayin da yake dashi cikin mulkinsa. Duk wanda bai siffantu da yadda yayi mulkinsa ba sunansa azzalumi ko da kuwa duniya za ta taru ta ba shi lambar shaidar adalci. 


A lokacin da Al-Huda-Huda ya faku daga ganin Annabi Sulaiman (A. S) sai yayi tambaya game dashi don yasan dalilin fakuwar tasa. Har ma yayi Alqawarin azabtar da shi ko yanka shi matuqar bai zo masa da qwaqqwarar hujja kan abinda ya aikata ba. 


Allah (S. W. A) ya bamu wannan qissar da cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


وَتَفَقَّدَ ٱلطَّيۡرَ فَقَالَ مَالِيَ لَآ أَرَى ٱلۡهُدۡهُدَ أَمۡ كَانَ مِنَ ٱلۡغَآئِبِينَ ٠٢ 


" KUMA YA BINCIKI TSUNTSAYE YACE, " ME YA FARU NE BANGA HUDA-HUDA BA KO DAI YA KASANCE NE DAGA CIKIN MASU FAKUWA ?"


لَأُعَذِّبَنَّهُۥ عَذَابٗا شَدِيدًا أَوۡ لَأَاْذۡبَحَنَّهُۥٓ أَوۡ لَيَأۡتِيَنِّي بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ ١٢


" LALLE ZAN AZABTAR DA SHI DA AZABA MAI TSANANI KO KUMA NA YANKA SHI KO KUMA DAI YA ZO MIN DA HUJJOJI BAYYANANNU. "


          (SURATUL-NAMLI)


Wannan na nuna mana iya mulki da adalci na Annabi Sulaimanu ta hanyar bibiya (monitoring ) . Idan mutum ya aikata wani abu wanda ake zarginsa, to, dole ya zamana cewa ya kare kansa ta hanyar hujjoji gamsassu, ko kuma a hukunta shi gwargwadon abinda ya aikata ko kuma a kashe shi idan abinda ya aikata ya kai ga hukuncin kisa. 


BUHARI BAI CANCANCI ZAMA SHUGABA BA 


Da yawa mutane na yin mulki ko shugabanci ba tare da sun iya ba, shi yasa ake ganin babu cigaba ta kowanne fanni a mulkinsa. 


Kafin hawa mulkin Buhari an zaci cewa shi yafi kowa cancanta da iyawa, har ake ganin mafita na hannunsa, zaman lafiya da walwala za a same su cikin gaggawa. Amma hawan mulkin nasa sai ya bayyanar da cewa shi wanene, domin bai iya komai wajen gudanar da mulki ba, ya zama kasau cikin dukkan wadanda suka taba yin mulki gabaninsa. 



Ba a taba samun wani shugaba wanda bai damu da halin da talakawansa ke ciki ba kamarsa, shi kadai ne wanda ya zabi cimmawa wasu buqatunsu ta hanyar karkashe al'ummarsa. 


Babu wanda ya isa ya rantse ko ya nuna wani mutum guda (1) wanda aka ce Buhari ya bibiye shi kuma ya hukunta shi cikin mulkinsa, in akwai kuma a kawo mana !


Mulkinsa kawai ya zama wasu ne ke gudanarwa ba shi ba, domin bai san komai na yadda zai iya gudanar da shi ba ballantana ya iya kare rayukan wadanda ya doru a kansu.


Wannan dalili yasa muka ce Dabba 🐑 ta fi shi hankali da ilimi !


FREE SAYYID ZAKZAKY (H) !!!


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


          (08137925034)


3rd June, 2021/ 23rd Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post