@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MUMINI SHINE WANDA YABI ALLAH DA MANZONSA KUMA YA MUTU KAN HAKA
A dabi'a irin ta Bahaushe shine duk wani wanda ba musulmi ba shi ake kira qabila. Wannan dalili yasa da zarar wani yaga Igbo ko Bayarbe sai kaji yana kiransa qabila domin cikinsu ne aka fi yawan samun kiristoci fiye da yadda ake samunsu cikin Hausa-Fulani.
Ita Qabila a wajen Allah ita ce dukkan wani yare wanda wasu gungun mutane suka kebanta dashi suna yin magana ta yadda babu mai iya fahintar maganar tasu in ba wanda ya koyi yaren nasu ba.
Balarabe kake ko Banasare ko kuma Bayahude sunanka Qabila matuqar kana da yare wanda wani ba ya jinsa in ba koyonsa yayi ba.
Shine Allah (T) ke cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن ذَكَرٖ وَأُنثَىٰ وَجَعَلۡنَٰكُمۡ شُعُوبٗا وَقَبَآئِلَ لِتَعَارَفُوٓاْۚ إِنَّ أَكۡرَمَكُمۡ عِندَ ٱللَّهِ أَتۡقَىٰكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٞ ٣١ ۞
" YAA KU MUTANE ! LALLE MUN HALICCE KU DAGA NAMIJI DA MACE, KUMA MUKA SANYA KU DANGOGI DA QABILU DOMIN KUSAN JUNA. LALLE MAFIFICINKU A WAJEN ALLAH SHINE MAFI TSORONSA DAGA CIKINKU ."
Ashe anan ana nuna mana ne cewa kowa ma Qabila ce ba wai kalmar Qabila ta kebanta da wasu na dabam bane. Saboda haka ba a raina Qabilar da mutum ya fito komai qanqantarta, haka kuma ba a fifita wata Qabila saboda yawanta, ta hanyar tsoron Allah kadai ake gane fifiko.
BAMBANCI TSAKANIN DANGI DA QABILA
وأخرج عبد بن حميد وابن جرير عن مجاهد {وجعلناكم شعوباً} قال: النسب البعيد، {وقبائل} قال: دون ذلك جعلنا هذا لتعرفوا فلان ابن فلان من كذا وكذا.
Abdu Bn Humaid da Ibn Jareer sun fitar daga Mujaheed cewa;
" KUMA MUKA SANYA KU DANGOGI. " Yace, " Ita ce Nasaba mai nisa ."
" DA KUMA QABILU. " Yace, " Koma bayan haka, an sanya wannan (Dangogi da Qabilu) ne domin asan wane 'Dan wane 'Dan wane daga kaza da kaza ."
قَالَتِ ٱلۡأَعۡرَابُ ءَامَنَّاۖ قُل لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ وَلَٰكِن قُولُوٓاْ أَسۡلَمۡنَا وَلَمَّا يَدۡخُلِ ٱلۡإِيمَٰنُ فِي قُلُوبِكُمۡۖ وَإِن تُطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَا يَلِتۡكُم مِّنۡ أَعۡمَٰلِكُمۡ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ ٤١
" QAUYAWA SUKA CE; " MUNYI IMANI !" KACE (musu yaa Muhammad); " BA KUYI IMANI BA (har yanzu), SAI DAI KUCE; " MUN SALLAMA. " AMMA IMANI BAI SHIGA CIKIN ZUKATANKU BA (tunda har za ayi muku umarni amma ku bijire) . IDAN (har) KUKA YIWA ALLAH BIYAYYA DA MANZONSA (cikin dukkan umarni da haninsu), TO, (Allah) BA ZAI TAUYE MUKU WANI ABU BA (daga cikin kyawawan) AYYUKANKU. LALLE ALLAH MAI GAFARA NE (bisa abinda muka aikata kuma kuka nemi gafararSa) KUMA MAI JIN QAI NE (ga bayinSa muminai. "
وأخرج ابن ماجة وابن مردويه والطبراني والبيهقي في شعب الإِيمان عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «الايمان معرفة بالقلب وإقرار باللسان وعمل بالأركان».
Ibn Majah da Ibn Mardawihi da 'Dabarani da Baihaqi sun fitar cikin Sha'abil Imaan, daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (R. A) yace; Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" SHI IMANI SHINE QUDIRI A ZUCIYA DA KUMA IQIRARI DA HARSHE, DA KUMA AIKI DA GABOBI ."
Wato cikakken imani shine ka tsarkake qudirinka cikin zuciyarka, kuma ya zamana ka furta shi da harshenka wanda yazo daidai da abinda ka qudirce shi cikin zuciyar taka, sannan kuma a gani a aikace kan gabobinka.
إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ لَمۡ يَرۡتَابُواْ وَجَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّٰدِقُونَ ٥١
" MUMINAN QWARAI SUNE WANDANDA SUKA YI IMANI DA ALLAH DA MANZONSA, SA'AN NAN BA SUYI SHAKKU (cikin wannan imanin nasu ba), KUMA SUKA YI JIHADI DA DUKIYOYINSU DA RAYUKANSU DOMIN ALLAH (ba don neman suna ko gudun zargi ba), TO, WADANNAN SUNE MASU GASKIYA (cikin imanin nasu) ."
يقول تعالى ذكره للأعراب الذين قالوا آمنا ولما يدخل الإيمان في قلوبهم: إنما المؤمنون أيها القوم الذين صدقوا الله ورسوله، ثم لم يرتابوا، يقول: ثم لم يشكوا في وحدانية الله، ولا في نبوة نبيه صلى الله عليه وسلم، وألزم نفسه طاعة الله وطاعة رسوله، والعمل بما وجب عليه من فرائض الله بغير شك منه في وجوب ذلك عليه
Allah (T) yana fada cikin ambatonsa ga Qauyawan nan da suka ce, " Munyi imani. " Alhali imanin bai shiga cikin zukatansu ba (illa kawai iyakar harsunansu) . Abin sani muminai kawai sune mutanen da suka gaskata Allah da Manzonsa, sa'an nan ba suyi kokonto ba. Yana cewa;
" Sa'an nan kuma ba suyi shakku cikin kadaituwar Allah ba, haka kuma cikin Annabtar AnnabinSa (S. A. W. W). Kuma ya lazimtawa kansa yin biyayya ga Allah da yin biyayya ga ManzonSa (ba wai yayi biyayya cikin abinda yazo daidai da son ransa ba, kuma ya saba masa cikin abinda ya saba son ransa). Da kuma yin aiki da abinda aka wajabta masa daga cikin farilla Allah ba tare da yin shakku daga gare shi ba wajen wajibcin hakan a kansa. "
(SURATUL-HUJRAAT, AYA TA 13-15)
Kenan idan ya zama mutum zai iya sabawa umarnin Allah da Manzonsa (S. A. W. W) don ganin ba ya raye, to, wannan asalan ba mumini bane.
YAA ALLAH KA TSARE MANA IMANINMU 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
2nd June, 2021/ 22nd Shawwal, 1442.