Sidi Munir Wakilin Yan Uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), Na Yankin Sokoto Ya Kai Ziyarar Jaje Bisa ibtila'in Gobara Kasuwar Daji Da Karan Shanu


 

A yau juma'a 4 ga watan Yuni, 2021. Wakilin yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na yankin Sokoto da kewaye wato Shaikh Sidi Munir Mai Nasara, ya kai ziyarar jaje a kasuwar Daji da Karan Dabbobi dake cikin jihar Sokoto domin jajantawa yan kasuwa akan ibtilain gobara da ya shafesu.

Malam ya sami rakiyar yan uwa makusanta da suka hada da Malam Sirajo Nufawa da Alhaji Bature yayan Shahid Kasim Umar Sokoto




Inda yan kasuwar suka karbi su Malam hannu bibbiyu da nuna farin cikin su akan kulawar da suka samu daga ɓangaren yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky, inda suka yi godiya da addu'a bisa wannan jaje da aka zo masu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post