@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RASHIN FAHINTAR MAGANA CE IN JI UMMUL-MUMININA A'ISHA
Abu ne daga cikin mafi muhimmanci ga mutum ya kasance yana sauraron dukkan maganar da yaji kuma ji na fahinta don gudun kada ya isar da ita ga wasu ba haqiqanin yadda ya ji ta ba.
Sau da yawa ana samun irin wadannan matsaloli na faruwa, walau bisa wata mummuniyar manufa ko kuma dai rashin fahintar magana. Irin hakane ta faru har yazo gare mu cewa wai Annabi (S. A. W. W) yace yin kuka ga mamaci na qara masa azaba. Saboda haka kake ji ana tsannanta hani ga kuka idan ya zamana anyi rashi na wani cikin dangi ko zuriya.
Riwayoyi ne mabambanta cikin SUNAN -NASA'I wadanda suka yi magana game da masu yin kuka in sun rasa wani nasu.
Ga riwayoyin nan kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
1866- أخبرنا محمد بن آدم عن عبدة عن هشام عن أبيه عن ابن عمر قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((إن الميت ليعذب ببكاء أهله عليه)). فذكر ذلك لعائشة فقالت وهل إنما مر النبي صلى الله عليه وسلم على قبر فقال: ((إن صاحب القبر ليعذب وإن أهله يبكون عليه)). ثم قرأت: {ولا تزر وازرة وزر أخرى}.
Muhammad Bn Adamu ya bamu labari, daga Abdata daga Hishaam, daga babansa daga Ibn Umar yace; " Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" LALLE SHI MAMACI ANA YI MASA AZABA SAKAMAKON KUKAN DA IYALANSA KE YI A KANSA. "
Sai aka ambaci hakan wajen Ummul-muminina A'isha, sai tace, " A'a, abinda dai ya faru shine, Annabi (S. A. W. W) ya wuce ne kan wani qabarinta, sai yace,
" LALLE SHI MA'ABOCIN QABARI ANA YI MASA AZABA, SU KUWA IYALANSA SUNA TA KUKA A KANSA. "
Sa'an nan ta karanta :
" KUMA RAI MAI 'DAUKAR WANI LAIFI BA ZA TA 'DAU LAIFIN WANI NA DABAM BA. "
Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, laifin wani na iya shafar wani ko da kuwa ba shi ya aikata. Wannan abu kuwa ya ci karo da ayar Allah kamar yadda Ummul-muminina A'isha ta kawo.
Cikin wani hadisi na gaba an kawo kamar haka;
1867- أخبرنا قتيبة عن مالك بن أنس عن عبد الله بن أبي بكر عن أبيه عن عمرة أنها أخبرته أنها سمعت عائشة وذكر لها أن عبد الله بن عمر يقول: إن الميت ليعذب ببكاء الحي عليه. قالت عائشة يغفر الله لأبي عبد الرحمن أما إنه لم يكذب ولكن نسي أو أخطأ إنما مر رسول الله صلى الله عليه وسلم على يهودية يبكى عليها فقال: ((إنهم ليبكون عليها وإنها لتعذب)).
Qutaibata ya bamu labari daga Malik Bn Anas, daga Abdullahi Bn Abubakar, daga babansa daga wata mata, cewa ita ta ba shi labari cewa ta ji A'isha ana bata labari cewa lalle Abdullahi Bn Umar yana cewa; " Lalle shi mamaci ana yi masa azaba sakamakon kukan da rayayyu suke yi musu. "
Sai A'isha tace; " ALLAH YA GAFARTAWA ABU ABDURRAHMAN, AMMA DAI CEWA SHI BA QARYA YAYI BA, SAI DAI MANTAWA YAYI KO KUMA DAI YAYI KUSKURE. ABIN SANI DAI ANNABI (S. A. W. W) YA SHUDE NE KAN QABARIN WATA BAYAHUDIYA WACCE AKE TA FAMAN YI MATA KUKA, SAI YACE;
" LALLE ITA ANA TA YIN KUKA A KANTA (na baqin cikin rabuwa da ita), ITA KUWA ANA TA YI MATA AZABA. " (saboda ba tayi imani da Allah).
1868- أخبرنا عبد الجبار بن العلاء بن عبد الجبار عن سفيان قال قصه لنا عمرو بن دينار قال: سمعت ابن أبي مليكة يقول: قال ابن عباس قالت عائشة إنما قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((إن الله عز وجل يزيد الكافر عذابا ببعض بكاء أهله عليه)).
A riwaya ta uku wacce muke son qarqare a kanta kuma tana cewa :
Abdul-Jabbar Bn Alla'a Bn Abdul-Jabbar ya bamu labari daga Safiyyata yace; Amru Bn Dinaar ya bamu labari yace : " Na ji Ibn Abiy Mulaikata yana cewa : Ibn Abbas yace, A'ishatu tace, abin sani kawai Manzon Allah (S. A. W.W) ya ce;
" LALLE ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YANA QARAWA KAFIRI AZABA SABODA SASHEN KUKAN DA SASHEN IYALANSA KE YI A KANSA. "
(SUNAN -NISAA'I)
Saboda haka batun cewa wai ana yiwa wani musulmi azaba sakamakon kukan iyalan da ya bari a bayansa ya zama tamkar tatsuniyar GIZO da QOQI ce wacce yinta ba shi da amfani ga wanda ake yiwa in har ka cire nishadi.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
8th June, 2021/ 28th Shawwal , 1442.