Shin, Auren Mutu'a na halatta matar da aka yi mata saki 3 ??


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

WANKAN JANABA BA YA KUBUCEWA DON ANYI TAIMAMA

Yana daga cikin adalcin Allah ya tsara komai ya zama daidai don maslahar bayinsa. Daga cikin abinda ya tsara musu akwai :-

-UMARNI:- Umarni shine dukkan abinda Allah (T) ya wajabta maka shi, kuma saba wannan umarni zai iya kai mutum wuta.

-HANI:- Hani shine dukkan wani aiki ko furuci wanda Allah ya hane mu aikatawa , kuma aikata shi zai iya kai mutum zuwa wuta.

- LALURA :- Lalura kuwa wata aba ce wacce ake samunta cikin haram/hani, amma wani yanayi zai iya bawa mutum damar aikata shi ba tare da ya fada cikin fushin Allah ba. 

Ya zo cikin riwaya kamar haka; 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

 كتاب حسين بن سعيد و النوادر ابْنُ أَبِي عُمَيْرٍ عَنْ حَمَّادٍ عَنِ الْحَلَبِيِّ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع‏

أَنَّهُ سُئِلَ عَنِ الرَّجُلِ يُطَلِّقُ امْرَأَتَهُ عَلَى السُّنَّةِ فَيَتَمَتَّعُ مِنْهَا رَجُلٌ أَ تَحِلُّ لِزَوْجِهَا الْأَوَّلِ قَالَ لَا حَتَّى يَدْخُلَ فِي مِثْلِ الَّذِي خَرَجَتْ مِنْهُ‏[22

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏101، ص: 140

Littafin Hussain Bn Sa'eed da kuma Nawadir na Ibn Abiy Umair, daga Hammad, daga Halabiyyi, daga Abu Abdullahi (A. S) cewa an tambaye shi game da mutumin da ya saki matarsa akan Sunnah, sai kuma wani mutum yayi Mutu'ah da ita (bayan sakin). To, shin ta halatta ga mijinta na farko (saboda ta auri wani namijin ta hanyar auren Mutu'ah)? Yace; 

" A'A, HAR SAI TAYI DUKULI DA MISALIN WANDA TA FITO DAGA GARE SHI. "

Abin nufi dole sai tayi aure na Sunnah kuma mijin yayi dukuli da ita kafin ta halatta ga mijinta na baya. 

                ABIN LURA

              ---------------------

Shi wannan hukunci ba wai yana nuna cewa auren Mutu'ah haramun bane, a'a, saboda shi aure ne wanda aka faro shi bisa lalura, kuma lalurar ce ta halasta yinsa. Irin wannan hukunci ana fitar dashi ne cikin abubuwa wadanda asalinsu sunzo zo cikin umarni ba wai wadanda suka zo saboda lalura ba. Kun san shi auren Mutu'ah bai zo ba har sai da Sahabbai suka sami kansu cikin lalurar sha'awar mata, shine aka fitar musu da wannan hukunci ga mai sha'awa don kada ya fada cikin halaka. 

Wannan hukunci kuwa ya zo daidai da hukuncin haramcin yin sallah ce da janaba. Domin haramun ne mutum yayi sallah da janaba a jikinsa. Amma lalura sai ta halasta masa yin sallar tare da janaba matuqar yayi taimama.

Amma ita wannan taimaka da mutum yayi ta halasta masa yin wani aiki ne a daidai wannan lokaci. Sai dai kuma ba wai yin taimamar ya dauke masa yin wanka bane, wajibi ne a kansa yayi wanka kafin wata sallah. 

DA FATAN AN FAHINTA 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

       (08137925034)

23rd June, 2021/ 13th Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post