Shafin Ma'asumah Ya Sami Yardar Sayyidah Fatimah (S.A)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ALLAH YIWA SHAFIN BAIWA DA SAMUN FITACCIYAR MAWAQIYAR SAYYIDAH ZAHRAH (A. S) 


Babban hadafin sanyawa wannan shafi suna MA'ASUMAH shine domin ma'aikatan shafin su sami yardarta cikin dukkan wani motsi nasu da sunan yiwa Allah da Manzonsa (S. A. W. W) aiki. 


Allah (T) na yarda da yardar Sayyidah Fatimah Ma'asumah kamar yadda yake fushi da fushinta (S. A). Duk wanda ya sami yardarta haqiqa yardar Allah ya samu, kuma wanda tayi fushi dashi ya fada cikin fushin Allah (S. W. A) !


Wakilai da yawa masu aiki qalilan, dama haka Allah ya fada da 'yan qalilan yake aiki, kuma dasu ne za ayi nasara. 


Babu mai kokonton cewa an sami masu hazaqa ta kowanne fanni cikin ma'aikatan wannan shafi maza da mata wadanda kowanne daga cikinsu yayi aiki za kaga akwai ilimi da hazaqa da kuma fasaha da qwarewa akan wannan abinda yayi.


Bangare daya (1) kawai muke da matsalarsa cikin ma'aikatan wannan shafi, wato samun mawaqa sisters daga cikin ma'aikatanta, amma maza (brothers) muna dasu masu hazaqa. 


Bisa yarjewar da Sayyidah MA'ASUMAH ta yiwa wannan shafi saboda ganin aikin da ake yi cikinsa wajen isar da saqon Ahlul-Bait (A. S) sai ta nuna yardarta da shafin ta hanyar fito mana da wata sister wacce ta kasance mai hazaqa wajen rera yabo gareta (S. A). 


Wannan sister kuwa ita ce RAMLAT (Hauwa'u ta Fatimah) Potiskum wacce ta kasance daidai wannan lokaci take fito da waqoqi tamkar wacce aka yiwa wahayi daga MIN INDIL-LAHI !


Fatanmu shine muma mu sami irin wannan yarda yadda za mu riqa yin abubuwan da zasu riqa amfanar da al'umma daga Ilimomin Iyalan gidan Manzon Allah (S. A. W. W). 


KU SANYA WANNAN BAIWAR ALLAH CIKIN ADDU'AH !


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


1st June, 2021/ 21st Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post