Saurayin ki ba Mahaifinki bane Sister !!!

 

Ma'asumah Nigeria News Update

Bazanga laifin maza ba ko kadan a wannan bangaren, suna yawan korafi akan mu mata cewa, da zaran saurayi yace yana sonki, to ke shikenan kakarki ta yanke saka, kin samu wurin barje gumenki na duk wasu bukatunki,  SAUYARINKI BA MAHAIFINKI BANE'YAR UWA, kar ki manta da wannan, ba wajibinsa bane biyan dukkan bukatunki na rayuwa, kafin ki hadu dashi mahaifanki ne suke yi miki, amma da kinga kin sameshi shikenan ke yanzu kin zama babbar yarinya, duk wani dawainiyanki ya koma kansa, shine anko, shine dinkin sallah, shine kaiki wurin hidimarki idan zaki ko kuma ya biya maki kudin napep, shine Ramadan basket, shine dinkin maulud, shine komi naki, saboda tsabar samun wuri har waya sai wacce take so zaya siya mata, wallahi maza da yawan sukan rike keypad 'yan matansu ka gansu da manyan wayoyin da wlh sunfi karfinsu.


A matsayinki na yar talaka, bai kamata ki rika dora guri irin na manyan yara ba, kar kice dole sai ya maki irin na kawarki, bayan kinsan kawarki ta cancanci hakan.


Tukunna ma, waye yace maki saurayi ne keda alhakin yi maki duk wa'yannan abubuwan?, Waye yace maki sai idan saurayinki yana maki hakan shine yake nuna cewa yana sonki?, Waye yace maki shidin bawanki ne?, Bari na tuna maki 'yar uwa, ko mata da miji idan aka cika bani bani wallahi suna fita ran juna ne, to bare ke da bama ki kai ga shiga gidanba, amma tun a waje kinaso ki saka mata su fita ransa.


Ki tausayawa yawan hidimar dake kansa mana, shine fa zaya yi maki lefe, shine zaya gina miki gidan da zaku zauna, shine zaya baki abinda zaki ci, sannan shine zaya rika kula dake da kuma lafiyar ki, idan baki tausaya masa tun a wajeba, wallahi hakan zaya da kinje gidan dama kin gama karar dashi tun waje, sai kiga abinda yake maki a wajenma ya saka miki ko rabinsa a gidan, kuma kece zaki fi kowa complain da hakan.


SAURAKINKI BA MAHAIFINKI BANE, kar kawaye su rudeki da abinda kikaga ana musu, kowa da irin halinsa da yanayin samunsa.   Sannan ba don nace hakan yake nuna ba abinda za ayi mata din, A'a idan ka samu hali akwai dan ihsani wanda ba haramun bane, sannan ba wajibi bane, amma yana kara kaunar juna da gyara alakarku, kar kace ba abinda zaka mata tunda baka Kai ga aurenta ba, ke kuma kar kice shine zai maki komi, ba wajibinsa bane na iyayenki ne, shi duk abinda kikaga yayi maki to ihsani ne, bawai wajibi ba.


Dayawan mata sune suke taimakawa maza wurin yaudararsu, da ya ganki ya nuna yanaso, ke ba kowan kowa ba amma ki rika nuna sai yayi maki abinda yafi karfinsa, shi kuma saboda yana sonki sai yayi duk yanda zayayi ya samo miki, da anyi aure saiya fito maki a true colour nashi, kuma sai kice ya yaudareki, ya miki karya bayan kece kika sakashi aikata hakan, da karan kanki, ina kara tuna maki duk wa'yancan abubuwan da kike ganin kamar dole ne yayi maki, to ba wajibinsa bane hakkin iyayenki ne ba nasa ba. 


Fatan zamu kula da wannan, Allah ya hada kowa da abokin rayuwa na gari.


✍️_ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post