Ranar Farko Wacce Annabi (S.A.W.W) Ya Fara Nasabta Imam Ali (A.S) Matsayin Khalifah !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


WANENE DAGA CIKINKU ZAI TAIMAKENI YA ZAMA WAZIRINA A BAYANA 


Farkon aiko Annabi (S. A. W. W) a matsayin dan saqo ba a umarce shi da ya kira kowa daga cikin al'ummarsa ba, makusantarsa ne ko kuma sauran al'ummun da yake cikinsu. 


Bayan wani lokaci ne kuma sai Allah (T) ya umarce shi kan cewa ya tashi yayi kira, kuma wannan kira nasa zai fara shi ne cikin danginsa kafin ya fadada shi zuwa sauran mutane gaba daya (AMM). 


Wannan umarni kuwa shine inda Allah (T) cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" وَأَنذِرۡ عَشِيرَتَكَ ٱلۡأَقۡرَبِينَ."( ٤١٢ )


" KUMA KA GARGADI DANGINKA NA KUSA. "


(Suratul-Shu'arah, aya ta 214)


Hikimar wannan shine, shi gyara akan faro shi ne daga cikin gida kafin a fita waje zuwa ga wasu. Idan ya zamana an bar gida a lalace, to, da zarar mutum yayi nufin kawo gyara a waje abinda zai fara fitowa daga bakin mutane shine, shi wannan mai neman kawo gyaran yaya gidansa yake ?


Saboda haka a lokacin da Allah yayi masa umarni sai ya tattara dukkan danginsa na kusa domin ya isar musu da wannan saqo. Ga dai yadda ganawar tasu ta kasance. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


وأخرج ابن إسحاق وابن جرير وابن أبي حاتم وابن مردويه وأبو نعيم والبيهقي في الدلائل من طرق عن علي رضي الله عنه قال: لما نزلت هذه الآية على رسول الله صلى الله عليه وسلم 


{وأنذر عشيرتك الأقربين} 


دعاني رسول الله صلى الله عليه وسلم، فقال: «يا علي ان الله أمرني أن أنذر عشيرتي الاقربين فضقت ذرعاً، وعرفت أني مهما أبادؤهم بهذا الامر أرى منهم ما أكره.

 فصمت عليها حتى جاء جبريل فقال: يا محمد إنك إن لم تفعل ما تؤمر به يعذبك ربك، فاصنع لي صاعاً من طعام، واجعل عليه رجل شاة، واجعل لنا عسا من لبن، ثم اجمع لي بني عبد المطلب حتى أكلمهم وأبلغ ما أمرت به، ففعلت ما أمرني به ثم دعوتهم له وهم يومئذ أربعون رجلاً يزيدون رجلاً أو ينقصونه، فيهم أعمامه أبو طالب، وحمزة، والعباس، وأبو لهب.

 فلما اجتمعوا إليه دعاني بالطعام الذي صنعت لهم فجئت به، فلما وضعته تناول النبي صلى الله عليه وسلم بضعة من اللحم فشقها باسنانه ثم ألقاها في نواحي الصحفة ثم قال: كلوا بسم الله.

 فأكل القوم حتى تهلوا عنه ما ترى إلا آثار أصابعهم.

 والله إن كان الرجل الواحد ليأكل ما قدمت لجميعهم.

 ثم قال: اسق القوم يا علي، فجئتهم بذلك العس فشربوا منه حتى رووا جميعاً.

 وايم الله إن كان الرجل منهم ليشرب مثله.

 فلما أراد النبي صلى الله عليه وسلم أن يكلمهم بدره أبو لهب إلى الكلام فقال: لقد سحركم صاحبكم.

 فتفرق القوم ولم يكلمهم النبي صلى الله عليه وسلم.

 فلما كان الغد قال: يا علي ان هذا الرجل قد سبقني إلى ما سمعت من القول، فتفرق القوم قبل أن أكلمهم، فعد لنا بمثل الذي صنعت بالأمس من الطعام والشراب ثم اجمعهم لي.

 ففعلت، ثم جمعتهم، ثم دعاني بالطعام فقربته، ففعل كما فعل بالأمس فأكلوا وشربوا حتى نهلوا، ثم تكلم النبي صلى الله عليه وسلم فقال: يا بني عبد المطلب إني والله ما أعلم أحداً في العرب جاء قومه بافضل مما جئتكم به، إني قد جئتكم بخير الدنيا والآخرة، وقد أمرني الله ان أدعوكم إليه فأيكم يؤازرني على أمري هذا فقلت وأنا احدثهم سناً: إنه أنا.

 فقام القوم يضحكون».


Ibn Ishaq ya fitar da Ibn Jareer da Ibn Abiy Haateem da Ibn Mardawihi da Abu Na'eem da Baihaqiy cikin DALA'ILI daga hanyoyi daban-dabam daga Aliyu (R. A) yace: 


" Yayin da aka saukar da wannan aya akan Manzon Allah (S. A. W. W) " KA GARGADI DANGINKA NA KUSA ."


Sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya kiraye ni yace min; 


" YAA ALIYU ! LALLE ALLAH YA UMARCENI DANA KIRAYI DANGINA NA KUSA, SAI ABIN YAYI MIN QUNCI, DOMIN NI NA SAN IDAN HAR NA KIRAYE SU NA BIJIRO MUSU DA WANNAN AL'AMARI LALLE ZANGA ABINDA BANA SO. SAI NAYI SHIRU AKAN HAKA HAR SAI DA JIBRILU YAZO YACE; 


" YAA MUHAMMAD ! LALLE KAI IDAN HAR BAKA AIKATA ABINDA AKE UMARTARKA DASHI BA UBANGIJINKA ZAI AZABTAR DA KAI. "


" SABODA HAKA KA SANA'ANTA MIN ABINCI NA SA'I 'DAYA (1) , KUMA KA SANYA QAFAR AKUYA A KANSA. MU KUMA KA SANYA WANI ABINCIN DAGA NONO, SA'AN NAN KA TATTARO MIN BANU ABDUL-MUDALLIB HAR SAI NAYI MAGANA DASU KUMA NA ISAR DA ABINDA AKA YI MIN UMARNI DASHI. "


Sai na aikata abinda aka umarceni dashi, sa'an nan na kiraye su gare shi. A wannan rana mutanen sun kai arba'in (40), suna qaruwa da mutum guda ko kuma raguwa da mutum guda, (abin nufi ko dai su 39 ne ko 41). Cikinsu akwai Ammominsa Abu 'Dalib, da Hamza, da Abbas, da kuma Abu Lahabin. 


A yayin da suka taru gare shi sai ya kirani nazo masa da abincin da ya umarce ni nayi , sai yazo da shi. To, yayin dana ajiye shi sai Annabi (S. A. W. W) ya dau wani abu daga cikin naman ya yayyaga shi da haqoransa (mai albarka), sa'an nan ya jefa shi cikin mazubinsa. Sa'an nan yace; 


" KU AMBACI SUNAN ALLAH KU CI. "


Sai jama'ar suka ci har kowa ya qoshi, amma babu abinda kake gani na ruguwar abincin face gurbin yatsunsu kawai (alamar inda suka sanya hannayenku cikin abincin). 


Na rantse da Allah babu wani mutum daya da zai iya cin (gwargwadon) abinda ya rage daga gabadayansu. Sa'an nan yace; 


" KA SHAYAR DA MUTANEN YAA ALIYU !"


Sai nazo musu da wannan abin shan, suka sha daga gare shi har sai da kowa ya qoshi. Na rantse da Allah ko da ace misalinsu ne (a yawansu) kowa zai qara sha (ba tare da ya qare ba) .


Yayin da Annabi (S. A. W. W) yayi nufin yayi musu magana (da abinda aka umarce shi) sai Abu Jahal ya bijiro masa da wata magana yace; 


" LALLE WANNAN MUTUMIN NAKU YA SIHIRCE KU (ta hanyar wannan abinci da abin sha wanda aka kasa cinyewa ko shanyewa). "


Daga nan sai jama'ar ta watse ba tare da Annabi (S. A. W. W) yayi musu wannan maganar ba. Yayin da gari ya waye sai yace; 


" YAA ALIYU ! LALLE WANNAN MUTUMI YA GABACE NI DA MAGANA KAMAR YADDA KAJI, SAI MUTANE SUKA WATSE KAFIN NAYI MUSU MAGANA . SABODA HAKA KA MAIMAITA MANA IRIN ABINDA KA SA'ANATA MANA DA MARAICE NA ABINCI DA ABIN SHA , SA'AN NAN KA (qara) TARO MIN SU. "


Sai na aikata kuma na qara taro su, sa'an nan ya kiraye ni nazo da abincin, sai na kusanto dashi na aikata kamar yadda na aikata da maraice (yamma). Suka ci suka sha har kowa ya qoshi, sa'an nan Annabi (S. A. W. W) yayi musu magana yace; 


" YAA 'YA'YAN ABDULMUDALLIB, LALLE NI WALLAHI BAN SAN WANI MUTUM DAGA CIKIN LARABAWA WANDA YA ZOWA MUTANENSA DA MAFIFICIN ABINDA NAZO MUKU DASHI BA. LALLE NI NA ZO MUKU DA ABINDA YAFI DUNIYA DA LAHIRA ALKHAIRI . HAQIQA ALLAH YA UMARCE NI DANA KIRAYE KU ZUWA GARE SHI. TO, WANENE DAGA CIKINKU ZAI TAIMAKE NI AKAN WANNAN AL'AMARI? "


Nine na fi su qarancin shekaru, sai nace masa Ni (zan taimake ka). Sai mutane suka tashi suka tafi dariya. "



(TAFSIR DURRUL-MANSUR NA SUYUDI)


'Dabari ma ya kawo irin wannan doguwar riwaya cikin Tafsir nasa, sai dai shi ga abinda ya kawo a qarshen maganar tasa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



...................................... ثم تكلم رسول الله صلى الله عليه وسلم، فقال: "يا بني عبد المطلب، إني والله ما أعلم شابا في العرب جاء قومه بأفضل مما جئتكم به، إني قد جئتكم بخير الدنيا والآخرة، وقد أمرني الله أن أدعوكم إليه، فأيكم يؤازرني على هذا الأمر، على أن يكون أخي " وكذا وكذا؟ قال: فأحجم القوم عنها جميعا، وقلت - وإني لأحدثهم سنا، وأرمصهم عينا، وأعظمهم بطنا، وأخمشهم ساقا. أنا يا نبي الله أكون وزيرك، فأخذ برقبتي، ثم قال: "إنهذا أخي " وكذا وكذا، "فاسمعوا له وأطيعوا " ، قال: فقام القوم يضحكون، ويقولون لأبي طالب: قد أمرك أن تسمع لابنك وتطيع


................Sa'an nan Manzon Allah (S. A. W. W) yayi magana yace; 


" YAA 'YA'YAN ABDULMUDALLIB , LALLE NI WALLAHI BAN SAN WANI MATASHI CIKIN LARABAWA WANDA YAZOWA MUTANENSA DA ABINDA YAFI WANDA NAZO MUKU DASHI BA. LALLE NI NAZO MUKU DA MAFI AKKHAIRIN DUNIYA DA LAHIRA, HAQIQA ALLAH YA UMARCENI DANA KIRAYE KU ZUWA GARE SHI. TO, WANENE DAGA CIKINKU WANDA ZAI TAIMAKE NI KAN WANNAN AL'AMARI? YA KASANCE 'DAN'UWANA, DA KAZA-DA-KAZA (ya ambato abubuwa da yawa wadanda nasu riwayar suka boye basu bayyanar dasu ba)?"


Yace, sai mutane gaba dayansu suka yi masa shiru (babu wanda ya amsa masa), sai nace; " Nine mafi qarancin shekarun cikinsu, kuma mafi kyawun idanuwansu, kuma wanda ya fi su qaton ciki, kuma wanda ya fisu kaurin qwabri (leg). Ni yaa Annabin Allah ! Zan kasance mataimakinka. Sai ya riqe wuyana sa'an nan yace; 


" LALLE WANNAN SHINE 'DAN'UWANA " DA KAZA DA KAZA. KUJI DAGA GARE SHI KUMA KUYI MASA BIYAYYA. "


Yace, sai mutane suka tashi suna ta dariya, suna fadawa Abu 'Dalib (A. S), " TO, LALLE AN UMARCE KA DA KA JI DAGA 'DANKA KUMA KAYI MASA BIYAYYA! "


(TAFSIRUL-'DABARI)


Cikin wannan magana kowa zai fahinci cewa Annabi (S. A. W. W) yayi umarni ne da cewa kowa Al zai bi kuma ya ji daga gare shi, domin su Babu Abdulmudallib sun fahinci hakan har ma sun fada. 


Idan kun kasa fahintar kalmar WAZIRI na nufin wanda zai tsaya a bayan wani ne in ba ya nan, to, ku nazarci wadannan ayoyi .


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


Annabi Musa (A. S) ne yake roqar Ubangijinsa da cewa; 


وَٱجۡعَل لِّي وَزِيرٗا مِّنۡ أَهۡلِي ٩٢ 


هَٰرُونَ أَخِي ٠٣ ٱشۡدُدۡ بِهِۦٓ أَزۡرِي ١٣ 


وَأَشۡرِكۡهُ فِيٓ أَمۡرِي ٢٣


" KUMA KA SANYA MIN WAZIRI DAGA IYALAINA. "


" HARUNA 'DAN'UWANA ."


" KA QARFAFI BAYANA DASHI. "


" KUMA KA SHIGAR DASHI (tarayya) CIKIN AL'AMARNA. "


(Suratul-'Daha, aya ta 29-32)


A lokacin da Annabi Musa (A. S) ya kauce Haruna (A. S) ne ya tsaya a matsayinsa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


         (08137925034)


31st May, 2021/ 20th Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post