Mumini baya qin Imam Ali (A.S), kuma munafiki baya sonSa !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SON IMAM ALI (A. S) MA'AUNI NA GANE IMANIN MUTUM

Soyayya da qiyayya ma'auni ne na gane matsayin mutum wajen wanda ake son yin magana a kansa. A duk lokacin da aka ambaci wata falala ko halayyar wani sai kaga wani abu ya bayyana na rashin jin dadi a fuskar wani, to, wannan mutumin za ka iya sanya shi cikin maqiya wanda aka kawo magana a kansa. 

Haka kuma da za a ambaci wani abu na sharri wanda ya faru ga wani, sai kuma kaga farin ciki ya bayyana ga wani mutum na dabam, to, dole ka sanya wannan mutumi cikin maqiyan wanda aka kawo magana a kansa. 

Na'am, akwai abubuwan dake sa aso mutum ko a qi shi. Wani akan so ne saboda halin kirki nasa ko a qi shi saboda halin banza nasa. Wani kuma qiyayya ce kawai take sa a qi shi ba wai saboda wani hali nasa na muni ba, yayin da wani ake sonsa saboda wata manufa don cimma wani muradi. 

     IMAM ALI (A. S) 

Idan muka dawo kan wanda muke magana a kansa wato Imam Ali (A. S) za mu iya cewa, shi bai fada cikin masu mummunan aiki wanda hakan zai za a qi shi ba. Sannan shi ba a sonsa don cimma wata manufa ko buqata ta qashin kai. Idan kaga mutum na sonsa, to, wannan mutumin mumini ne, haka kuma duk wanda kaga yana qinsa to, munafuki ne. 

Yazo cikin hadisin Manzon Allah (S. A. W. W) wanda Ummus-Salamata ta bada labarin abinda taji daga Manzon Allah (S. A. W. W). Ga riwayar kamar haka; 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

25909- حَدَّثَنَا عُثْمَانُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ أَبِي شَيْبَةَ , قال عبد الله : وَسَمِعْتُهُ أَنَا مِنْ عُثْمَانَ بْنِ مُحَمَّدٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ فُضَيْلٍ ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ أَبِي نَصْرٍ ، قَالَ : حَدَّثَنِي مُسَاوِرٌ الْحِمْيَرِيُّ ، عَنْ أُمِّهِ ، قَالَتْ : سَمِعْتُ أُمَّ سَلَمَة َ , تَقُولُ : سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ لِعَلِيٍّ : " لَا يُبْغِضُكَ مُؤْمِنٌ ، وَلَا يُحِبُّكَ مُنَافِقٌ "

Usman Bn Muhammad Bn Abiy Shaibata ya bamu labari, Abdullahi yace: Muhammad Bn Fudhail ya bamu labari daga Abdullahi Bn Abdurrahman baban Nadhari yace : Misaawiru Al-Himyariy ya bani labari, daga mahaifiyarsa tace :

" Na ji Ummus-Salamata tana cewa ta ji Manzon Allah (S. A. W. W) yana fada (magana) game da Aliyu :

" MUMINI BA ZAI TABA QINKA BA, KUMA MUNAFUKI BA ZAI SO KA BA !"

(Musnad na Imam Ahmad, qarqashin Musnadin-Nisa'i, Musnad Ummus-Salamata, hadisi mai lamba 25,909)

Saboda haka duk wanda kaga yana baqin ciki ko nuna rashin jin dadi in an ambaci wata falala ta Imam Ali (A. S), to, wannan mutumin munafuki ne. 

Idan kuma har kaga farin ciki ya bayyana ga mutum a fuskarsa in an ambaci sunan Imam Ali (A. S) ko kuma aka ambaci wata falala tasa, to, idan ana neman inda muminai suke sai kayi musu nuni zuwa ga wannan mutumin. 

YA ALLAH KADA KA JARRABCE MU DA JIN WANI QUNCI CIKIN ZUKATANMU IN AN AMBACI SUNAN IMAM ALI (A. S) .

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post