@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KYAKKYAWAR FASSARA DAGA IMAM HASSAN (A. S)
Allah (T) ya halicci duniya ce domin ta zama gidan jarrabawa wacce ake jarraba ayyukan bayi aga wannene daga cikinsu zai kyautata aikinsa domin Allah, sai dai kuma bai sanya ta ta zama gidan sakamako ba. Saboda haka komai zai iya samunka a cikinta, walau ta hanya mai kyau ko mummuniya.
Ita duniya Allah kan bada ita ga kowa cikin bayinsa, shi yasa muke ganinta a hannun muminai da kafirai. Wannan kuwa ya ci karo da irin fassarar da wasu ke yiwa wannan hadisi na qasa wanda yazo daga Manzon Allah (S. A. W. W).
Hadisin yana cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
2494» حدثنا قتيبة حدثنا عبد العزيز بن محمد عن العلاء بن عبد الرحمن عن أبيه عن أبي هريرة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((الدنيا سجن المؤمن وجنة الكافر)). وفي الباب عن عبد الله بن عمرو.
قال أبو عيسى: هذا حديث حسن صحيح
Qutaibata ya bamu labari, Abdul-Azeez Bn Muhammad ya bamu labari daga Alaa'a Bn Abdurrahman, daga babansa, daga Abu Hurairata yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" ITA DUNIYA KURKUKUN MUMINI CE KUMA ALJANNAR KAFIRI. "
A wani babin kuma daga Abdullahi Bn Umar.
Abu Isah (Al-Tirmidhi) yace : " Wannan hadisi kyakkyawa ne ingantacce. "
(SUNAN TIRMIDHI, HADISI MAI LAMBA 2494)
Jin wannan hadisi sai yasa wasu ke yi masa mummuniyar fassara da cewa in dai mutum mumini ne dole ya takura a duniya ta hanyoyi daban-dabam. Wai bai kamata ace ana ganinsa yana hawa manyan Motoci ko sanya tufafi na alfarma ba, ko kuma a gan shi cikin gida na alfarmar.
A fahintarsu shine, kafirai ne kadai ya kamata su kasance cikin wannan siffa a duniya domin ita ce Aljannarsu. Su kuma muminai su zauna cikin qunci da takura wanda hakan ne zai nuna cewa su masu tsoron Allah ne.
Lalle wannan mummuniyar fahinta ce, domin kuwa ba haka Annabi (S. A. W. W) ke nufi cikin hadisin ba. Za mu iya fahintar haqiqanin ma'anarsa cikin maganar Imam Hassan (A. S).
Wata rana wani kafiri dake cikin quncin rayuwa ya ga Imam Hassan (A. S) cikin sutura ta alfarma sai yake qalubalantarsa da cewa ai bai kamata ace yayi shiga (dress) irin wannan ba, wannan shigar tasa irin ta Kafirai ce, domin Annabi (S. A. W. W) yace ita duniya kurkuku ce ga mumini kuma Aljannah ga kafiri.
Sai ya qara da cewa : " Ni kuwa bana ganinta face Aljannah gare ku, kuma Kurkuku gare mu (in ji kafirin). "
Sai Imam Hassan (A. S) yace masa;
" AI DA ACE KA SAN TANADIN DA AKA YI MIN A ALJANNAH DA KUWA KA SAN CEWA NAN KURKUKU CE GARE NI. KUMA DA ACE KA SAN ABINDA AKAYI MAKA TANADINSA CIKIN WUTA NA AZABA, TO, DA KUWA KA SAN CEWA NAN (duniya) ALJANNAH CE GARE KA. "
Abinda Imam Hassan (A. S) ke nufi da wannan magana taka shine, duk wani jin dadi da mumini zai samu anan duniya in har ya kwatanta shi dana lahira zai ji tamkar yana cikin kurkuku ne.
Shi kuwa kafiri duk irin halin qunci da zai shiga anan duniya in ya kwatanta shi dana lahirarsa, to, zai ce ai wannan rayuwar tasa ta duniya Aljannah ne gare shi.
Wannan dalili yasa nake ganin daqiqancin 'yan zuhudu masu ganin cin nama da Kifi da shinkafa da qwai da kuma hawa mota ko gina gida a matsayin rashin gudun duniya. Abinda ake kiran wannan shine godiya ga ni'imar Allah wacce ya hore masa abin yin su.
Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa;
" DUK WANDA ALLAH YA BA SHI WATA NI'IMA, TO, AGA GURBIN WANNAN NI'IMA TARE DA SHI. "
Kenan idan Allah ya hore maka abinda za ka sanya sutura ta alfarma ko shiga mota da gida na alfarma, sai kuma ka kasance kana barin iyalinka cikin quncin abinci ko qarancin sutura ko kuma rashin gyara musu muhalli mai kyau da sunan gudun duniya (Zuhudu ), to, wallahi butulci kake yiwa Allah ba wai muna godiya da tsoro gare shi ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
18th June, 2021/ 8th Zul-Qadah, 1442.