@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA AJALI NE MAI GAGGAUTA KAI MUTUM LAHIRA DA YANZU SAYYID ZAKZAKY (H) YA ZAMA TARIHI
Magana ce ta ilimi ba wai jahilci ba, ba zai taba zama hujja kayi saurin yankewa mutum hukunci kawai daga fara jin maganarsa ba tare da ka saurare shi zuwa qarshe maganar tasa ba.
Irin wannan gaggawar ce tasa Ibn Khaddab zartar da hukuncin kashe wata mata wacce aka Kama ta tana zina a wata mashaya, amma ta hanyar Imam Ali (A. S) ta kubuta da ranta saboda tayi zinar ne bisa tilas ba wai don son ranta ba.
Sanin kowa ne abinda Buhari ya yiwa Sayyid Zakzaky (H) na zalunci ya isa ya sanya shi cikin kwandon tarihi a yanzu, amma kuma sai ya zamana har yanzu yana nan da ransa kuma yana amfanar damu.
Ya zo cikin Alqur'ani inda Allah (T) ke cewa;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
قُل لَّآ أَمۡلِكُ لِنَفۡسِي ضَرّٗا وَلَا نَفۡعًا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۗ لِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌۚ إِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ فَلَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ (٩٤)
" KACE, " NI BAN MALLAKARWA KAINA WATA CUTA BA KO KUMA AMFANI BA FACE ABINDA ALLAH YASO . GA KOWACCE AL'UMMA TANA DA AJALI, IDAN AJALINSU YAZO BA ZA JINKIRTA KO DA SA'A (guda ba) KUMA BA ZA A GAGGAUTAR (da zuwan ba) ."
(SURATUL-YUNUS:49)
Abinda wannan aya ke nuna mana shine, zuwan ajali shi ke kawo kowanne abu ko kuma kawar dashi, domin idan yazo ba a yin wani jinkiri, sa'annan ba za a gaggauta zuwan abu ba in dai har ajalinsa bai zo ba.
To, dangane da haqiqanin fassarar ma'anar wannan aya aka samu daga gidan Manzon Allah (S. A. W. W) da kuma shi kansa (S. A. W. W) yadda suka fayyace mana komai bisa ma'ana ta haqiqa.
Ya zo cikin DA'AWATUL-RAWANDIY daga Imam Sadiq (A. S) cewa;
دَعَوَاتُ الرَّاوَنْدِيِّ، قَالَ الصَّادِقُ ع يَعِيشُ النَّاسُ بِإِحْسَانِهِمْ أَكْثَرَ مِمَّا يَعِيشُونَ بِأَعْمَارِهِمْ وَ يَمُوتُونَ
بِذُنُوبِهِمْ أَكْثَرَ مِمَّا يَمُوتُونَ بِآجَالِهِمْ."
Imam Sadiq (A. S) yace;
" MUTANE SUNA RAYUWA NE (mai tsaho ta hanyar) KYAUTATAWARSU FIYE DA YADDA SUKE RAYUWA DA SHEKARUNSU, KUMA SUNA MUTUWA NE (ta hanyar) ZUNUBANSU FIYE DA YADDA SUKE MUTUWA DA AJALINSU. "
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج5، ص: 141
Ma'anar wannan hadisi shine, yawanci idan kaga mutane na rayuwa mai tsaho to, kyawawan ayyukansu ne ke kaisu haka ba wai nisan kwana na ajali ba. Kuma mutane sunfi yawan mutuwa sakamakon ayyukansu na zunubi fiye da zuwan ajali.
Wato kyawawan ayyuka na tsawaita rayuwar mutum, kuma yawan zunubansa na rage masa tsahon kwana.
Idan ka kasa fahintar wannan magana ka biyo mu cikin hadisin dake biye daga Manzon Allah (S. A. W. W). Ga shi kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
تفسير العياشي عَنِ الْحُسَيْنِ بْنِ زَيْدٍ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص إِنَّ
الْمَرْءَ لَيَصِلُ رَحِمَهُ وَ مَا بَقِيَ مِنْ عُمُرِهِ إِلَّا ثَلَاثُ سِنِينَ
فَيَمُدُّهَا اللَّهُ إِلَى ثَلَاثٍ وَ ثَلَاثِينَ سَنَةً وَ إِنَّ الْمَرْءَ لَيَقْطَعُ رَحِمَهُ وَ قَدْ بَقِيَ مِنْ عُمُرِهِ ثَلَاثٌ وَ ثَلَاثُونَ سَنَةً فَيَقْصِرُهَا اللَّهُ إِلَى ثَلَاثِ سِنِينَ أَوْ أَدْنَى قَالَ الْحُسَيْنُ وَ كَانَ جَعْفَرٌ ع يَتْلُو هَذِهِ الْآيَةَ يَمْحُوا اللَّهُ
ما يَشاءُ وَ يُثْبِتُ وَ عِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ
Ya zo cikin Tafsir na Ayashi, daga Hussaini Bn Zaid, daga Ja'afar Bn Muhammad, daga babansa (A. S) yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" LALLE MUTUM ZAI RIQA SADA ZUMUNCINSA WANDA ABINDA ZAI RAGE DAGA RAYUWARSA BAI WUCE SHEKARU UKU BA, SAI ALLAH YA TSAWAITA SU ZUWA SHEKARU TALATIN DA UKU (33). KUMA LALLE MUTUM ZAI YANKE ZUMUNCINSA WANDA ABINDA YA RAGE DAGA RAYUWARSA SHINE SHEKARU TALATIN DA UKU (33), SAI ALLAH YA TAQAITA (gajarta) SU ZUWA SHEKARU UKU (3) KO KUMA QASA DA HAKA. "
Hussaini yace, Ja'afar (A. S) ya kasance yana karanta wannan aya;
" ALLAH NA SHAFE ABINDA YASO KUMA YANA TABBATARWA, KUMA A WAJENSA UMMUL-KITAB YAKE ."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج5، ص: 143
Cikin wannan hadisi na Ma'aiki (S. A. W. W) na tabbatar mana ne cewa sada zumunci yana tsawaita rayuwa, kuma yanke zumunci yana rage tsahon rayuwa. Idan kuwa hakane tabbas za mu iya cewa Sayyid Zakzaky (H) ya sami kyakkyawar shaida wajen kyautatawa da kuma sada zumunci. Wannan dabi'u nasa ne ma suka yi tasirin da yakai har yanzu da yake gidan yari (prison) bai bar wannan kyautatawar tasa ba.
Sannan kuma ayar da aka kawo a qarshe hadisi na tabbatar mana ne cewa hadisai biyun da aka kawo ba suci karo da ayar da muka kawo a farko ba, domin kuwa Allah yana iya canza abinda yaso bisa ganin damarsa saboda wasu dalilai, kuma ya tabbatar da abinda tun farko baiyi nufin hakan a kansa ba. Shi kuwa Allah ba a tambayarsa dalilin da yasa yayi abinda yaso da ransa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
11th June, 2021/ 1st Zul-Qada , 1442.