Ka ji tsoron Allah ya Muhammad, cikin martani da wani yayi wa Annabi (S.A.W.W)


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @


MARTANIN DA WANI SAHABI YA YIWA MANZON ALLAH (S. A. W. W)


Ko da guri daya (1) ba a taba samun wani malami wanda yace ba Sahabi bane wanda yayi wannan kakkausan martani mafi muni ga Manzon Allah (S. A. W. W) ba. 


Ko da ace an boye sunansa hakan bai hana a gane zuriyarsa cikin wannan al'umma da muke raye cikinta ba, domin kuwa ayyukansu ya fito qarara ya bayyana a idon duniya. 


Wadannan mutane kuwa sun fi kama da 'yan Izala na kowanne bangare, da kuma sauran wasu rubabbu daga sauran jama'ar musulmi. 


Ku biyo mu cikin wannan hadisi wanda muka tsamo muku shi daga cikin SUNAN ABU DAWUD.


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


4766- حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ كَثِيرٍ أَخْبَرَنَا سُفْيَانُ عَنْ أَبِيهِ عَنِ ابْنِ أَبِي نُعْمٍ عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ قَالَ: بَعَثَ عَلِيٌّ عَلَيْهِ السَّلاَمُ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِذُهَيْبَةٍ فِي تُرْبَتِهَا فَقَسَّمَهَا بَيْنَ أَرْبَعَةٍ بَيْنَ: الأَقْرَعِ بْنِ حَابِسٍ الْحَنْظَلِيِّ ثُمَّ الْمُجَاشِعِيِّ وَبَيْنَ عُيَيْنَةَ بْنِ بَدْرٍ الْفَزَارِيِّ وَبَيْنَ زَيْدِ الْخَيْلِ الطَّائِيِّ ثُمَّ أَحَدِ بَنِي نَبْهَانَ وَبَيْنَ عَلْقَمَةَ بْنِ عُلاَثَةَ الْعَامِرِيِّ ثُمَّ أَحَدِ بَنِي كِلاَبٍ قَالَ فَغَضِبَتْ قُرَيْشٌ وَالأَنْصَارُ وَقَالَتْ: يُعْطِي صَنَادِيدَ أَهْلِ نَجْدٍ وَيَدَعُنَا. فَقَالَ: ((إِنَّمَا أَتَأَلَّفُهُمْ)). قَالَ: فَأَقْبَلَ رَجُلٌ غَائِرُ الْعَيْنَيْنِ مُشْرِفُ الْوَجْنَتَيْنِ نَاتِئُ الْجَبِينِ كَثُّ اللِّحْيَةِ مَحْلُوقٌ قَالَ: اتَّقِ اللَّهَ يَا مُحَمَّدُ. فَقَالَ: ((مَنْ يُطِعِ اللَّهَ إِذَا عَصَيْتُهُ أَيَأْمَنُنِي اللَّهُ عَلَى أَهْلِ الأَرْضِ وَلاَ تَأْمَنُونِي)). قَالَ: فَسَأَلَ رَجُلٌ قَتْلَهُ أَحْسِبُهُ خَالِدَ بْنَ الْوَلِيدِ- قَالَ- فَمَنَعَهُ. قَالَ: فَلَمَّا وَلَّى قَالَ: ((إِنَّ مِنْ ضِئْضِئِ هَذَا أَوْ فِي عَقِبِ هَذَا قَوْمًا يَقْرَءُونَ الْقُرْآنَ لاَ يُجَاوِزُ حَنَاجِرَهُمْ يَمْرُقُونَ مِنَ الإِسْلاَمِ مُرُوقَ السَّهْمِ مِنَ الرَّمِيَّةِ يَقْتُلُونَ أَهْلَ الإِسْلاَمِ وَيَدَعُونَ أَهْلَ الأَوْثَانِ لَئِنْ أَنَا أَدْرَكْتُهُمْ قَتَلْتُهُمْ قَتْلَ عَادٍ)). 

Muhammad Bn Katheer ya bamu labari, Safyanu ya bamu labari daga babansa daga Ibn Abiy Nu'umi, daga Abu Sa'eedul-Khudriy yace :


" An aiki Aliyu (A. S) zuwa ga Manzon Allah (S. A. W. W) da wata Zinari, sai (Annabi) ya raba ta tsakanin mutane hudu (4):


Aqra'a Bn Habis Al-Hanzaliy, sa'an nan Mujashi'iyyi, da kuma tsakanin Ubaidata Bn Badrin Al-Fazari'iy, da kuma tsakanin Zaidul-Khailiy Ad-Da'iyyi, sa'an nan dayan Bani Nabhaan da tsakanin Alqamata Bn Ulaathata Al-Amiriy, sa'an nan dayan iyalan Kilab ."


Yace : " Sai Quraishawa da Ansaar suka fusata (da abinda Annabi (S. A. W. W) yayi), suka ce :


" An bawa qasqantattu daga mutanen Najdi kuma aka barmu !" Said (S. A. W. W) yace; 


" AI MUNA RARRASHIN ZUKATANSU NE (ta wannan hanya don kada suyi ridda). "


Yace : " Sai wani mutum mai zurfin idanuwa, mai fadin kumatu, mai tudun goshi, mai kaurin Gemu mai sudadden kai (ball head) ya fuskanto yace :


" Kaji tsohon Allah yaa Muhammad (cikin wannan rabo naka na rashin adalci)! " Sai (Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" WANENE KUMA ZAI YIWA ALLAH BIYAYYA IN HAR NI NA SABA MASA ? ALLAH YA AMINTAR DANI AKAN MUTANEN QASA AMMA KAI BA ZA KA AMINCE MIN BA (cikin abinda na aikata) ?"


Yace : Sai wani mutum ya roqi a ba shi damar kashe shi, ana tsammanin Khalid Bn Walid ne . yace: Sai aka hana shi .Yace : Yayin da (mutumin) ya juya sai (Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" LALLE DAGA CIKIN TSATSON WANNAN KO A QARSHEN WANNAN AKWAI WASU MUTANE (da za su fito) SUNA KARANTA QUR'ANI AMMA BA ZAI WUCE MAQOGORONSU BA, SUNA FITA DAGA MUSLIMCI KAMAR YADDA KIBIYA KE FITA . ZA SU RIQA YAQAR MA'ABOTA MUSLIMCI (ta kowacce hanya, makami ne ko harsunansu), KUMA SU RIQA KIRAN MA'ABOTA GUMAKA (Yahudawa da nasara a matsayin iyayen gidansu masu basu umarni da oda). DA ACE NI ZAN RISKE SU (a wannan zamanin da za su fito) DA NA KASHE SU IRIN KISAN ADAWA !"


(SUNAN ABU DAWUD, BABIN YAQAR KHAWARIJAWA, HADISI MAI LAMBA 4766)


Yaa Allah ka raba mu da yin koyi da irin wadannan mutane masu cin zarafin Manzon Allah (S. A. W. W). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


11th June, 2021/ 1st Zul-Qada 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post