Wallahi Ni ban ma yarda Abubakar ya ja Sallah a zamanin Annabi (S.A.W.W) ba; wanda yafi mutane karatun littafin Allah ne yake jagirantar su !



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Ba zai zama abin mamaki ba idan ya zama a wannan zamani ana gabatar da mai qarancin sanin littafin Allah akan wanda ya fi shi, amma abu ne mawuyaci ace Sahabban Annabi (S. A. W. W) su dora mutum jagorancin sallah alhali akwai wanda ya fi shi a gurin. 

To, ina kuma ga Manzon Allah (S. A. W. W) ace ya gabatar da wani akan wanda suka fi shi sanin littafin Allah ? Idan kuwa ya zama haka, to, fassarar da za a yiwa Annabi (S. A. W. W) ita ce yana yiwa mutane umarni da aikhairi shi kuma ya manta da kansa. Wannan kuwa ba zai taba yiwuwa gare shi ba (S. A. W. W). 

Ya zo cikin Sunan na Abu Dawud a qarqashin Babin wanda yafi cancanta da limanci cewa wanda yafi kowa sanin littafin Allah ne zai jagorance su. 

Ga riwayar nan kamar haka :

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

باب مَنْ أَحَقُّ بِالإِمَامَةِ: 

582- حَدَّثَنَا أَبُو الْوَلِيدِ الطَّيَالِسِيُّ حَدَّثَنَا شُعْبَةُ أَخْبَرَنِي إِسْمَاعِيلُ بْنُ رَجَاءٍ سَمِعْتُ أَوْسَ بْنَ ضَمْعَجٍ يُحَدِّثُ عَنْ أَبِي مَسْعُودٍ الْبَدْرِيِّ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((يَؤُمُّ الْقَوْمَ أَقْرَؤُهُمْ لِكِتَابِ اللَّهِ وَأَقْدَمُهُمْ قِرَاءَةً فَإِنْ كَانُوا فِي الْقِرَاءَةِ سَوَاءً فَلْيَؤُمَّهُمْ أَقْدَمُهُمْ هِجْرَةً فَإِنْ كَانُوا فِي الْهِجْرَةِ سَوَاءً فَلْيَؤُمَّهُمْ أَكْبَرُهُمْ سِنًّا وَلاَ يُؤَمُّ الرَّجُلُ فِي بَيْتِهِ وَلاَ فِي سُلْطَانِهِ وَلاَ يُجْلَسُ عَلَى تَكْرِمَتِهِ إِلاَّ بِإِذْنِهِ)). قَالَ شُعْبَةُ فَقُلْتُ لإِسْمَاعِيلَ مَا تَكْرِمَتُهُ قَالَ فِرَاشُهُ.

Baban Walid Ad-'Dayalisiyyi ya bamu labari, Shu'ubatu ya bamu labari, Ismael Bn Rajaa'i ya bani labari cewa ya ji Ausa Bn 'Dam'aji yana bada labari daga baban Mas'ud Al-Badriy yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace :

" WANDA YAFI MUTANE SANIN LITTAFIN ALLAH KUMA YA FI SU DADEWA DA SANIN KARATU YA JAGORANCE SU (sallah). IDAN YA ZAMANA SUNZO DAIDAI A KARATU, TO, YANDA YA RIGAYE SU HIJRA YA JAGORANCE SU. IDAN KUMA YA ZAMA SUNZO DAIDAI A HIJRA, TO, WANDA YA FI SU YAWAN SHEKARU YA JAGORANCE SU. KUMA KADA A JAGORANCI MUTUM (sallah) A GIDANSA, KO A GURIN DA YAKE DA IKO. KUMA KADA A ZAUNA A GURINSA MAI ALFARMA HAR SAI DA IZNINSA. "

Shu'ubatu yace, sai na cewa Isma'ila; " Menene wajen alfarmarsa ?" yace, " SHIMFIDARSA ."

(SUNAN ABU DAWUD, HADISI NA 582)

Bisa wannan umarni na hadisi sai ya zamana Sahabban Annabi (S. A. W. W) suna gabatar da wanda suka san ya fi su sanin littafin Allah ne cikin sallolinsu yayin da Annabin ke raye. 

Ga misali nan kamar haka cikin Sahihul-Bukhari. 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

استقضاء الموالي واستعمالهم

(7175) - حدثنا عثمان بن صالح: حدثنا عبد الله بن وهب: أخبرني ابن جريج: أن نافعاً أخبره: أن ابن عمر رضي الله عنهما أخبره قال: 

كان سالم مولى أبي حذيفة يؤم المهاجرين الأولين وأصحاب النبي صلى الله عليه وسلم في مسجد قباء، فيهم أبو بكر وعمر وأبو سلمة وزيد وعامر بن ربيعة ."

Usmana Bn Salih ya bamu labari, Abdullahi Bn Wahbin ya bamu labari, Ibn Juraij ya bani labari cewa , lalle Nafi'an ya ba shi labari cewa Ibn Umar ya ba shi labari yace : 

" SALEEM BARARREN BAWAN BABAN HUZAIFATA YA KASANCE YANA JAGORANTAR MASU HIJRAR FARKO DA SAHABBAN ANNABI (S. A. W. W) A MASALLACIN QUBAH. KUMA A CIKINSU (wadanda yake jagorantar) AKWAI ABUBAKAR DA UMAR DA BABAN SALAMATA DA ZAID DA KUMA AMEER BN RABEE'ATA. "

(SAHIHUL-BUKHARI, HADISI NA 7175)

Domin sanin dalilin da yasa Saleem ya riqa jan su Abubakar sallah sai ku biyo mu cikin wannan hadisi, 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

           إمامة العبد والمولى

( 692) - حدثنا إبراهيم بن المنذر قال: حدثنا أنس بن عياض، عن عبيد الله، عن نافع، عن ابن عمر قال: 

لما قدم المهاجرون الأولون العصبة، موضع بقباء، قبل مقدم رسول الله صلى الله عليه وسلم، كان يؤمهم سالم، مولى أبي حذيفة، وكان أكثرهم قرآنا."

Ibrahim Bn Munziri ya bamu labari, Anas Bn Iyaadh ya bamu labari, daga Ubaidullahi, daga Nafi'i, daga Ibn Umar yace :

" YAYIN DA MASU HIJRAR FARKO SUKA ISA USBAH, WANI GURI A QUBAH KAFIN ISOWAR MANZON ALLAH (S. A. W. W), YA KASANCE SALEEM BARARREN BAWAN BABAN HUZAIFATA NE KE JAGIRANTARSU (sallah), YA KASANCE YA FI SU SANIN ALQUR'ANI. "

(SAHIHUL-BUKHARI, HADISI NA 692)

Kunga dalilin da yasa Saleem ya riqa jansu sallah shine saboda ya fi su sanin Qur'ani. Shi yasa Sahabban suka gabatar dashi ya riqa yi musu sallah. 

Idan muka koma hadisin farko wanda Imam Abu Dawud ya kawo za muga cewa Umarnin Annabi (S. A. W. W) wanda yayi kan cewa a gabatar da mafifici wajen sanin littafin Allah kuma wanda ya fisu dadewa da sanin littafin. 

Idan kuwa hakane sai muce Imam Ali (A. S) mafidicinsu wajen sanin littafin Allah kuma mafi dacewarsu a sanin littafin Allah, domin kuwa sai da yayi shekara bakwai yana muslimci kafin a sami wanda daga cikin Sahabbai ya muslimta.

             TAMBAYA 

Yanzu dan Allah akwai mai tunanin cewa Annabi (S. A. W. W) zai yi umarni da cewa a shugabantar da mafi sanin littafin Allah har Sahabban su aikata sannan kuma shi yazo ya saba wannan umarni nasa da kansa?

Ko kuma akwai inda aka kawo ne cewa shi Saleem bararren bawan Abu Huzaifata ya rasu ne kafin wannan lokaci, ko kuma akwai inda aka kawo ne cewa daga baya Abubakar yayi karatu har ya zo ya wuce Saleem ?

Na bar batun Imam Ali (A. S) saboda ba a kawo shi cikin wadanda aka ce Abubakar ya ja su sallah ba, saboda a lokacin Imam Ali (A. S) yana tare da Manzon Allah (S. A. W. W) wajen jinyarsa. 

Wadannan hujjoji yasa nace WALLAHI NI BAN MA YARDA CEWA ABUBAKAR YA TABA JAN SALLAH YAYIN DA ANNABI (S. A. W. W) KE RAYE BA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

        (08137925034)

15th June, 2021/ 5th Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post