Hani game da zagin Sahabbai (R.A)


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DA ACE 'DAYANKU ZAI CIYAR DA ZINARI GWARGWADON DUTSIN UHUDU BA ZAI KAISU A DARAJA BA 

Nasan ko wanda bai yi karatu ba yana ji daga bakin maluma cewa zagin musulmi fasiqanci in ji Manzon Allah (S. A. W. W), kuma ya qara da cewa kashe su kuma kafirci ne.

Saboda haka na san zai yi wuya ace a sami mutum musulmi ya riqa zagin dan'uwansa musulmi ko ya kashe shi, sai dai in dama shi ba mumini bane. To, ina kuma ga zagin Sahabbai (R. A)? 

Zai zama qaton kuskure ka bude baki kana zagin wani Sahabi wanda yayi biyayya ga Annabi (S. A. W. W) kuma kace wai hakan daidai ne. Shi yasa ban yarda cewa akwai mai imani wanda zai iya bude baki ya zagi Sahabi ba, ko da shike dai tarihi ya kawo cewa an sami wasu daga cikin Sahabban da suke zagin Imam Ali da Iyalan gidansa (A. S) akan Mimbari . Saboda haka dan an sami masu koyi dasu yanzu ba zai zama abin mamaki ba. 

Ya zo cikin Sunan na Abu Dawud game da wannan hani na zagin Sahabbai. Ga shi kamar haka; 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

اب في النَّهْيِ عَنْ سَبِّ أَصْحَابِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: 

4660- حَدَّثَنَا مُسَدَّدٌ حَدَّثَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ عَنِ الأَعْمَشِ عَنْ أَبِي صَالِحٍ عَنْ أَبِي سَعِيدٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((لاَ تَسُبُّوا أَصْحَابِي فَوَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ لَوْ أَنْفَقَ أَحَدُكُمْ مِثْلَ أُحُدٍ ذَهَبًا مَا بَلَغَ مُدَّ أَحَدِهِمْ وَلاَ نَصِيفَهُ)).

Musassadu ya bamu labari, baban Mu'awiyata ya bamu labari daga A'amashu, daga baban Salihu, daga Abu Sa'eed yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 

" KADA KU ZAGI SAHABBAINA ! NA RANTSE DA WANDA RAINA KE HANNUNSA , DA ACE 'DAYANKU ZAI CIYAR DA ZINARI (a hanyar Allah) MISALIN DUTSEN UHUDU (a girma), TO, BA ZAI KAI MUDUN 'DAYANSU BA, KO KUMA KWATANKWACINSA. "

(SUNAN ABU DAWUD, BABIN HANI GAME DA ZAGIN SAHABBAN ANNABI, HADISI MAI LAMBA 4660)

              ABIN LURA 

          -------------------------

Ya kamata mutum yasan bambanci tsakanin zagi da fadar laifin mutum, shi zagi shine aibata mutum da wani abu na laifi ko muni wanda bai aikata ba. Fadar laifi kuwa shine ambaton abinda mutum ya aikata na laifi don ya zama na baya sun kiyaye don kada su fada cikin halaka. 

Irin wannan ambaton laifi bai zama baqon abu wajen ma'abota karatu ba, domin munji kuma mun gani cikin Alqur'ani inda aka ambaci kafircin Fir'auna da kuma laifin wasu mata daga cikin matan Annabawa (A. S). 

Allah ya kawo mana irin wannan misali inda yake cewa; 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

 ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱمۡرَأَتَ نُوحٖ وَٱمۡرَأَتَ لُوطٖۖ كَانَتَا تَحۡتَ عَبۡدَيۡنِ مِنۡ عِبَادِنَا صَٰلِحَيۡنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمۡ يُغۡنِيَا عَنۡهُمَا مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَقِيلَ ٱدۡخُلَا ٱلنَّارَ مَعَ ٱلدَّٰخِلِينَ ٠١

" ALLAH YA BUGA MISALI DOMIN WADANDA SUKA KAFIRTA, MATAR NUHU DA MATAR LUTU. SUN KASANCE A QARQASHIN WASU BAYI BIYU DAGA CIKIN BAYINMU SALIHAI, SAI SUKA HA'INCE SU, (saboda haka zamantakewarsu) BATA WADATAR DASU DA KOMAI BA WAJEN ALLAH. KUMA AKA CE, " KU SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGA. "

      (SURATUL-TAHRIM:10)

Idan ya zamana ambaton laifi shine zagi, to, za mu iya cewa Allah ne ya fara zagin wasu mutane cikin Alqur'ani kamar yadda na ambata. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

         (08137925034)

9th June, 2021, 29th Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post