@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IDAN AKA SAMI SHAHIDAI BIYU CIKIN DANGINKU KUN RABAUTA
Shahada wani matsayi ne wanda Allah (T) kan kebe wasu tsarkaka daga bayinsa da ita, duk wanda kaga yayi shahada to, wani bawa ne amintacce cikin bayin Allah.
Wannan dalili yasa Allah (T) ya fifita Annaba da A'immah (A. S) ta hanyar samun shahadarsu domin su bambanta a matsayi ranar alqiyama.
Duk da cewa an kawo cikin riwaya me cewa shahidai biyar ne, wato :-
-WANDA YA MUTU TA HANYAR ANNOBA.
-WANDA YA MUTU TA HANYAR CIWON CIKI.
-WANDA GINI YA RUSU MASA.
-WANDA YA HALAKA A RUWA da kuma
-WANDA AKA KASHE SHI A HANYAR ALLAH.
To, cikin wadannan biyar din babu wanda aka fifita a cikinsu da ceton danginsa sai wanda aka kashe a hanyar Allah.
SHAHIDI NA CETON MUTANE 70 DAGA DANGINSA
Ya zo cikin riwaya daga Manzon Allah (S. A. W. W) inda yake yin nuni da hakan, ga riwayar nan biye;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
باب في الشَّهِيدِ يُشَفَّعُ:
2524- حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ صَالِحٍ حَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ حَسَّانَ حَدَّثَنَا الْوَلِيدُ بْنُ رَبَاحٍ الذِّمَارِيُّ حَدَّثَنِي عَمِّي: نِمْرَانُ بْنُ عُتْبَةَ الذِّمَارِيُّ قَالَ: دَخَلْنَا عَلَى أُمِّ الدَّرْدَاءِ وَنَحْنُ أَيْتَامٌ فَقَالَتْ: أَبْشِرُوا فَإِنِّي سَمِعْتُ أَبَا الدَّرْدَاءِ يَقُولُ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((يُشَفَّعُ الشَّهِيدُ فِي سَبْعِينَ مِنْ أَهْلِ بَيْتِهِ)). قَالَ أَبُو دَاوُدَ: صَوَابُهُ رَبَاحُ بْنُ الْوَلِيدِ.
Ahmad Bn Salihu ya bamu labari, Yahya Bn Hassan ya bamu labari, Walid Bn Rabaahi Az-Zamaariyyu ya bamu labari, Baffana ya bani labari , Imrana Bn Utbata Az-Zammariyyu yace : " Mun shiga wajen Ummu Darda'i lokacin muna marayu (orphans), sai tace : Kuyi bushara, lalle ni na ji Baban Darda'i yana cewa : Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa;
" SHAHIDI YANA CETON MUTANE SABA'IN (70) DAGA CIKIN IYALAN GIDANSA (danginsa). "
Abu Dawud yace : Rabaahu Bn Walid ya kyautata shi (inganta shi).
(SUNAN ABU DAWUD, KITABUL-JIHAD, BABIN SHAHIDI NA YIN CETO, HADISI MAI LAMBA : 2524)
Saboda haka mafi yawan 'yan Shi'ah za mu sami ceto ranar lahira, domin cikinsu ne ake dibar shahidai marar adadi. Kuma maganar Manzon Allah (S. A. W. W) gaskiya ce .
YAA ALLAH KA AZURTAMU DA SHAHADA KO KA AZURTA WASU DAGA CIKIN DANGINMU DON MU SAMI CETONSU 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
24th June, 2021/ 14th Zuk-Qadah, 1442