Daga Birnin Najaf
A rana juma'a 18/06/2021 A ka yiwa yan uwa mabiya Sayyid Zakzaky Hafizahullahu Rawani tare da yi masu izinin fara wa'azi da isar da saƙon Ahlulbaiti AS.
Da kuma aiki da karatun.
Limamin Juma'a na Birnin Najaf mai tsarki wato Mufakkir Islam Assayyid Sadruddeen Qubanchi shine ya albarkaci sanyawa Daliban rawani wato 1.Shaikh Abba Yusuf Garba Kano
2. Shaikh Nazifi Musa Jigawa.
Dalibai ne su a Makaranta mai suna *Jami'atu Imamul Mahdy Namuzujiyya*
Wadda shi Limamin Najaf din ya assasa ta kuma dan sa Sayyid Muhammad ke shugaban ta. Kuma mutum ne dan thaura Islamiyya shiyasa suka sawa Maktabar su sunan Makhtibar Sayyid Qa'id Khamenei.
Wani abu da zai faranta ran duk wani dan uwa shine su wadan nan Daliban kananan yara ne yan kasa da shekaru 30 saboda an haifi Shaikh Abba ne 04/04/1995 kuma Mahaifin sa wani dattijo ne bawan Allah mai yawan zuri'a saboda yaran sa kawai sun kai 40 jikoki kuwa sama da 70. Alh. Garba shi kadai ya isa wata Da'irar Kuma mutum mai Sadaukarwa a harkar musulunchi.
Yau Allah ya albarkaci yaron shi da zama cikin Malaman mu a harka Islamiyya.
Abba mai laqabi da Zainabiyya yaro ne mai kokarin gaske lokacin da Dalibai ke gudun makarantar saboda Wahalar ta shi lokacin ya bar wadda yake ya dawo.
Shi kuwa Shaikh Nazifi Musa an haife shi ne a garin Sara dake karamar hukumar Gwaram jihar jigawa ranar 28/08/1997.
Yana daga cikin yara yan baiwa dana sani a rayuwa ta (Gifted) don yana cikin Daliban mu na Daurah da mukayi a 2018 a Suleja.
Su 8 muka je dasu makarantar Nida Sayyid Shu'aibu Amma shi kadai ya samu nasarar shiga wannan ajin da a dokar makarantar daga marhala ta 3 dole suyi maka rawani tare da alkawarin zaka rika yawo dashi duk inda zaka je sai dai da lalura.
Allah yayi masu albarka ya sanya su zama Malamai da Allamah Sayyid Zakzaky zai yi alfahari da su wurin samun murshidai a harka.
Allah ka taimaki dukkan Dalibai na harka Islamiyya a duk inda suke a fadin duniya.
Mu da duk mai fafutikar samar da makarantu da Mallamai cikin harkar musulunchi Allah ka tsare mu daga sharrin maƙiya munafukai na kusa dana nesa da azzalumai.
Kayi amfani damu wurin faranta ran Jagora wurin samar da makarantu a kasar nan da sai dai azo ayi karatu daga waje.
Allah ka amsa don tsarkin zuciyar Annabi Muhammadu saww
Shehu Al-ja'afaree Kaduna
18/06 /2021