Ba a lissafin sakin Aure har sai anyi shi sau Uku a jere


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DUK MATAR DA TAYI AURE BAYAN SAKI BA A SANYA SHI CIKIN JERIN SAKI UKU 

Sakin aure na da qa'ida a muslimci kamar yadda komai ke da qa'idojinsa. Dole ya zamana anyi saki ne bayan kafin ya inganta, kuma ba a lissafa saki uku cikin kalma daya a matsayin uku. Duk sakin da akayi shi sau uku ko fiye da haka cikin kalma daya ko tsarki daya yana madadin saki daya (1) ne. 

Sakin da ake yin komansa shine sau daya ko sau biyu, amma da zarar ya kai uku ba zai taba halatta ba dole sai an auri sabon miji kuma yayi Dukhuli da ita kamar yadda yazo cikin Alqur'ani. 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

ٱلطَّلَٰقُ مَرَّتَانِۖ فَإِمۡسَاكُۢ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ تَسۡرِيحُۢ بِإِحۡسَٰنٖۗ 

" SAKI SAU BIYU YAKE, KO DAI A RIQE DA ALKHAIRI KO KUMA A SALLAMA BISA KYAUTATAWA....... "

       (BAQARA:229)

Wannan aya na nuna mana ne adadin saki wanda ya halatta. Idan haka ta faru akwai zabi biyu : Ko dai a riqeta da alkhairi ba tare da anyi na uku ba don cigaban zamantakewa. Ko kuma a sallameta da kyautatawa kamar yadda Allah ya umarce mu.

Sai kuma Ya qara da cewa; 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدُ حَتَّىٰ تَنكِحَ زَوۡجًا غَيۡرَهُۥۗ فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَآ أَن يَتَرَاجَعَآ إِن ظَنَّآ أَن يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِۗ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ ٠٣٢

" IDAN KUMA YA (qara) SAKINTA (na uku), TO, BA TA HALATTA GARE SHI (ya qara mayar da ita don cigaba da sabon zama) BAYAN HAKA HAR SAI TA AURI WANI MIJIN KOMA BAYANSA. IDAN (shi sabon mijin) YA SAKE TA BABU KAIFI SU KOMAWA JUNA IN HAR SUNYI ZATON ZA SU TSAYAR DA DOKOKIN ALLAH. WANDAN CAN DOKOKIN ALLAH NE YAKE BAYYANAR DASU GA MUTANE WADANDA SUKE SANI. "

             (BAQARA:230)

To, domin sanin yadda wannan lissafi na saki yake sai mu leqa wannan hadisi dake tafe. 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

 ين، كتاب حسين بن سعيد و النوادر الْحَسَنُ بْنُ مَحْبُوبٍ عَنْ إِسْحَاقَ بْنِ جَرِيرٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: سَأَلَهُ بَعْضُ أَصْحَابِنَا وَ أَنَا حَاضِرٌ عَنْ رَجُلٍ طَلَّقَ امْرَأَتَهُ تَطْلِيقَةً وَاحِدَةً ثُمَّ تَرَكَهَا حَتَّى بَانَتْ مِنْهُ ثُمَّ تَزَوَّجَهَا الزَّوْجُ الْأَوَّلُ قَالَ فَقَالَ نِكَاحٌ جَدِيدٌ وَ طَلَاقٌ جَدِيدٌ لَيْسَ التَّطْلِيقَةُ الْأُولَى بِشَيْ‏ءٍ هِيَ عِنْدَهُ عَلَى ثَلَاثِ تَطْلِيقَاتٍ مُتَتَابِعَاتٍ وَ إِنْ كَانَ الْأَخِيرُ لَمْ يَدْخُلْ بِهَا ثُمَّ تَزَوَّجَهَا الْأَوَّلُ فَهِيَ عِنْدَهُ عَلَى تَطْلِيقَةٍ مَاضِيَةٍ وَ بَقِيَتِ اثْنَتَانِ‏[24].

Ya zo cikin littafin Hussain Bn Sa'eed da kuma Nawadir na Hassan Bn Mahbuub, daga Ishaqa Bn Jareer, daga Abu Abdullahi (A. S) yace:

Sashen Sahabbansa sun tambaye shi yayin da nake gurin (a zaune) game da mutumin da ya saki matarsa saki daya (1), sa'annan ya barta har aka take ta daga wannan sakin (ta hanyar auren wani sabon miji), sannan mijin farko ya aure ta (ya mayar da ita gidansa ta hanyar sake aurenta). Yace : Sai (Imam) yace; 

" AURE NE SABO KUMA SAKI SABO (a tsakaninsu), SHI WANNAN SAKI NA FARKO DA YAYI MATA BA A BAKIN KOMAI YAKE BA A WAJENSA AKAN SAKI UKU A JERE. DA KUMA ACE SHI NA QARSHEN (sabon mijin da ya aure ta) BAI TAKE TA BA, SA'AN NAN KUMA MIJIN FARKO YA AURE TA (a matsayin kome), TO, ITA A WAJENSA TANA KAN SAKIN DA YA GABATA (saki daya), KUMA YA RAGE BIYU (a tsakaninsu). "

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏101، ص: 141

Wannan na qara tabbatar mana ne cewa dole sai saki ya kasance a jere ba tare da samun sabon aure da wani mijin ba sannan ake gina adadin sakin har zuwa uku. Amma da ace mutum zai saki matarsa sau biyu ya rage saura daya kenan sannan wani miji na dabam ya aure ta, to, idan ta dawo gare shi bayan saki ya zama tamkar wannan lokaci ne ya fara aurenta. 

Da kuma ace za tayi aure goma (10) bayan sakin da mijinta na baya yayi mata amma babu wanda yayi Dukhuli da ita daga cikinsu bisa wani dalili, to, idan ta dawo wajen mijinta na farko za su doru ne kan adadin sakin da ya auku tsakaninsu. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

       (08137925034)

23rd June, 2021/ 13th Zul-Qadah, 1442.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Meyehukunchin matar da akasaka saki 1 bayan tayi aure akadawoda ita kuma akakara saketa saubiyu shin zasu koma koko auren yaharamta

    ReplyDelete
Previous Post Next Post