Asibitin Imam Zainul-Abideen dake Iraqi sun yiwa mutane aiki na kimanin Dinari biliyan 1 kyauta


 

Hukumar gudanarwa na Asibitin Kwararru na Zainul Abidin (AS) wacce take mallakin Haramin Imam Husain ne ta bayyana Adadin Kuɗaɗe da aka kashe kan Ayyukan kiwon lafiya kyauta da aka bayar a farkon shekara 2021 wanda ya kai sama da biliyan daya da dubu (200) na dinarin Iraq. 

A wata hira da akayi da Yanar gizon Hukumar Asibitin ta ce ayyukan da Asibitin suka gudanar kyauta a rabin farkon shekarar 2021 sun nunka ayyuka sama da (2025), kuma jimillar kudin da aka kashe sama da (1,231,972,000) ne na Dinarin Irak.

Ta bayyana cewa wadannan ayyukan da suka ƙunshi galibin kwararrun likitoci a Asibitin, har da hadi da likitoci dashen ƙoda da na ƙashi baya hadi da bude idon yara da manya, Sannan kuma ga ayyukan kyauta da na sauki da Asibitin ya bullo dasu. 

Ta kara da cewa ayyukan sun hada da bangarorin da dama hadi da wadanda aka zalunta da kuma wadanda suka ji rauni a zanga_zanga, Jami'an tsaro da Iyalan Shahidai da suke dukkan Garuruwan Iraki. 

Ta kara da cewa asibitin ta kunshi kwararrun Likitoci cikin Gida da kuma wajen Iraki, tare da amfani da sabbin kayan aiki da ya dace da fasahar Duniya a fanni likitanci. 

Abin lura a nan shi ne, Haramin Imam Husain (as) ta hanyar Irshadin wakilin babban malamin Addinin ƙasar wato Samahatu Shaikh Abdul Mahdi Karbala'i, yana aitawar da ayyuka musamman a bangaren kiwon lafiya, tare da yin aikin kula da yan ƙasa musamman ma dangin shahidai da Talakawa da wadanda ke da ƙarancin abubuwan Rayuwa .

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post