Ashe mafi yawan matan Ahlus-Sunnah Zina suke yi a rashin sani!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


JAHILCI GA MAZAJENSU KO KUMA BIN SON ZUCIYA 


Kamar yadda malamai ne ke cewa ita zina kala-kala ce, akwai wacce ake yinta ta hanyar takar mace kuma akwai wacce ake yinta ta hanyar kallo.


To, ita wannan wacce muke son yin magana a kanta bata daga cikin biyun nan da muka ambata. Ita sha shafi wani abu ne daga nau'in ado ga mata Khass. 


Bari mu shiga kai tsaye cikin hadisin Ma'aiki (A. A. W. W) don ji daga bakinsa.


Wannan hadisi ya zo ne cikin Sunan-Nisa'i a babi wanda yazo da karhamcin sanya turare ga mata. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


باب مَا يُكْرَهُ لِلنِّسَاءِ مِنَ الطِّيبِ: 


5143- أَخْبَرَنَا إِسْمَاعِيلُ بْنُ مَسْعُودٍ قَالَ: حَدَّثَنَا خَالِدٌ قَالَ: حَدَّثَنَا ثَابِتٌ- وَهُوَ ابْنُ عُمَارَةَ- عَنْ غُنَيْمِ بْنِ قَيْسٍ عَنِ الأَشْعَرِيِّ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((أَيُّمَا امْرَأَةٍ اسْتَعْطَرَتْ فَمَرَّتْ عَلَى قَوْمٍ لِيَجِدُوا مِنْ رِيحِهَا فَهِيَ زَانِيَةٌ)). 


Isma'il Bn Mas'ud ya bamu labari yace :Khalid ya bamu labari yace : Thaabit ya bamu labari, shine Ibn Umarata, daga Ghunaim Bn Qais, daga Ash-Ariyyi yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" DA DAI MACE ZA TA SANYA TURARE SANNAN TA WUCE TAKAN MUTANE DON SU JI QAMSHINTA, TO, ITA MAZINACIYA CE !"


(SUNAN -NISA'I, HADISI MAI LAMBA 5143)


Yanzu sanya Turare ga matan Sunniy ya zama wani abin alfahari kamar yadda maza ke sayen Turare suna sanyawa a jikinsu. 


Hakan kuwa yafi faruwa ne gare su idan za su fito daga gidajensu zuwa gidan biki ko wajen aiki . Kai ! Ko zuwa asibiti ne dubiya in kaga basu sanya Turare ba, to, basu dashi ne amma ba zai taba yiwuwa ace sun manta bane, domin wajen irin wannan abu na Shaidanci mata basu da mantuwa. 


Shi malamin ya kawo maganar ce a babin karhamci, amma kamata yayi ya kawo shi cikin babin haramci. Domin qarya ne ace wai mace ta sanya Turare ta fito amma ba wai ta sanya ne da nufin wasu suji ba.


Mafi girman laifin na kan mazajensu ce da suke barinsu suna sanyawa, domin barin nasu taimaka musu ne wajen sabawa Ubangiji. 


SUKHRAN LAH FAKRAH 


Zai yi wuya ace ka sami irin wannan na faruwa cikin 90% na matan 'yan Shi'ah, domin su malaminsu ya karantar dasu haramcin irin wadannan abubuwa, saboda haka 'yan qalilan ne kawai za ka iya samu suna aikatawa, domin komai tsabtar hanya sai wataran iska ta kado da datti a kanta (hanyar). 


Saboda haka muke gargadinku da ku kiyaye ku guji fushin Allah tun kafin lokaci ya qure muku.


Ku kuma sisters ku godewa Allah da ya hada ku da jagora wanda ke bambance muku tsakanin haram da halas. 


YAA ALLAH KA QARAWA SAYYID LAFIYA DA IYALINSA, KUMA KA FITO MANA DASHI CIKIN LAFIYA DA KUZARI 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


13th June, 2021/ 3rd Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post