An gudanar da Taron tunawa da Hazikin Shahidin nan wato Shahid Humaid Ibraheem Zakzaky (H) a garin Dambo-Zaria, jihar Kaduna
Da farko dai an fara gudanar da saukar Al-qur'ani mai girma da km addu'o'i na musamman a muhallin taron, daka bisani aka cigaba da gudanar da taron.
Yara 'Yan Jaishu Humaid sun gudanar da wasan Chess domin nuna tasu kalar murnar ta zagayowar ranar haihuwar Shahidin. Taron da ya sami halartar yan uwa daka sassa daban- daban hadi da Malamai, Iyaye da kuma matasa.
Malam Taheer Ibraheem shine ya gabatar da jawabin farko akan rayuwar Shahidin, Yayinda Malamin yake fadin baiwa da karamomin da Allah(SWT) yayima wannan Hazikin Shahidin.
Malamin ya bayyana karamar Shahidin ta wajen bayayyarshi ga Allah(SWT) da kuma sallamawarshi ga Jagoran shiriya.
Malami mai jawabi na biyu kuma yayi magana ne akan darasi daga rayuwar Shahidin, Yayin da ya bayyana cewa shi Shahid Humaid gaba daya rayuwarshi ta xama abar koyi ga dukkan mutumin da ya kasance dan gwagwarmaya duk da cewa ba wani shekarune da shi ba.Mai jawabin yana cewa shi Shahid Humaid ya tafiyar da likacinshi wajen bawa jagora kariya da kuma tinanin yadda Za'a cigabantar da harkar gwagwarmaya kuma hakan shine abinda ya kamata ace ko wanne dan gwagwarmaya ya kasance
Malamin yayi jan hankali gameda hakkokin jagora akan yan'uwa
Bayan ya kammala jawabin sai kuma yaran wato yan Jaishu Humaid suka gudanar da Display, Daga bisani kuma aka yanka Alkaki(cake) aka rufe taron da addu'a.
Ga wasu daga Hotunan da muka dauka
Anyi lafiya an tashi lafiya
16\06\2021