A matsayin ka na Musulmi, wacce tafi burgeka cikin wadannan Mata?



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


HIJABI MUTUNCIN 'YA MACE 


Ba wai wayewa bane kaga 'ya mace ta girma ta zama Mukallifa sannan kuma ace tana barin wani bangare na jikinta a waje koma bayan fuskarta da tafukan hannayenta.



Ba ma bangaren jikinta ba, hatta bayyanar da ado ga wanda ba muharrami ba ya zama haram a gare ta. Saboda haka wajibi ne ga musulma ta kasance tana yin shiga irin ta muslimci yadda duk wanda ya ganta zai yi mata kallon mutunci.


Laifukansu kadan ne in ka kwatanta dana iyayensu, domin su suke barinsu suna yin shiga ta fitsara a gabansu ba tare da tunanin cewa su fa musulmai ne masu doka cikin addininsu. 



Allah (T) na umartar Manzonsa (S. A. W. W) da cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّأَزۡوَٰجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَآءِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ يُدۡنِينَ عَلَيۡهِنَّ مِن جَلَٰبِيبِهِنَّۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن يُعۡرَفۡنَ فَلَا يُؤۡذَيۡنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا (٩٥)


" YAA KAI ANNABI ! KA FADAWA MATANKA DA 'YA'YANKA (mata) DA KUMA (sauran) MATAN MUMINAI CEWA SU KUSANTAR DA QASA DAGA MANYAN TUFAFINSU (Hijab), HAKAN SHI YAFI SAUQI DA A GANE SU (cewa su matan kirki ne), BA ZA A CUTAR DASU BA (ta hanyar kallon sha'awa ko yi musu maganar baza), KUMA ALLAH YA KASANCE MAI GAFARA NE (kan abinda suka aikata kafin wa'azi yazo musu ) KUMA MAI JIN QAI NE (a ranar gobe Qiyama) ."


(AHZAB, AYA TA 59)


Saboda haka Annabi (S. A. W. W) shine na farko wajen aikata wannan umarni ga matansa da 'ya'yansa mata kafin ma wani daga cikin Sahabbansa yasan matsayin sanya Hijabi ga matarsa.


Idan har ka kasance kai musulmin kirki ne mai koyi ga Manzon rahma Muhammad (S. A. W. W) dole ka umarci 'ya'yanka mata da subi wannan umarni na Ma'aiki (S. A. W. W).


Hakama in har ke mumina ce dole kiyi koyi da matan Annabi (S. A. W. W) da kuma 'ya'yansa (A. S) wajen sanya Hijabi don ki boye abinda Allah yace ki boye .



Allah (T) na cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَٰتِ يَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِنَّ وَيَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ وَلۡيَضۡرِبۡنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّۖ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوۡ ءَابَآئِهِنَّ أَوۡ ءَابَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآئِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ أَخَوَٰتِهِنَّ أَوۡ نِسَآئِهِنَّ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّ أَوِ ٱلتَّٰبِعِينَ غَيۡرِ أُوْلِي ٱلۡإِرۡبَةِ مِنَ ٱلرِّجَالِ أَوِ ٱلطِّفۡلِ ٱلَّذِينَ لَمۡ يَظۡهَرُواْ عَلَىٰ عَوۡرَٰتِ ٱلنِّسَآءِۖ وَلَا يَضۡرِبۡنَ بِأَرۡجُلِهِنَّ لِيُعۡلَمَ مَا يُخۡفِينَ مِن زِينَتِهِنَّۚ وَتُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُون( ١٣)



" KUMA KA FADAWA MUMINAI MATA DA SU RINTSE IDANUWANSU (daga kallon dukkan abinda aka haramta musu kallonsa) KUMA SU TSARE FARJOJINSU (daga zina), KUMA KADA SU BAYYANAR DA ADON SU FACE ABINDA YA BAYYANA DAGA GARE SHI (fuska da tafukan hannaye). SANNAN KUMA SU SANYA KIMAR NASU AKAN KAFADUNSU (ya hade da wannan babban tufafi da aka ce su sanya cikin suratul Ahzab), KUMA KADA KU BAYYANAR DA ADONSU (na tufafi) FACE GA MAZAJENSU KO IYAYENSU KO KUMA IYAYEN MAZAJENSU, KO 'YA'YAYENSU (na cikinsu) KO 'YA'YAN MAZAJENSU (ta bangaren kishiyoyinsu), KO 'YAN'UWANSU KO 'YA'YAN 'YAN'UWANSU (maza) KO 'YA'YAN 'YAN'UWANSU (mata), KO KUMA MATANSU (na mu'amala) KO KUMA ABINDA HANNAYENSU YA MALLAKA (na bayi). KO KUMA WADANNAN WADANDA BASU DA SHA'AWA DAGA MAZA (saboda tsufa) , KO KUMA QANANAN YARA (maza) WADANDA BASU KAI GA TSINKAYEN AL'AURAR MATA BA. KUMA KADA SUYI DUKA DA QAFAFUNSU DOMIN KADA ASAN ABINDA SUKE BOYEWA DAGA ADONSU (na tsiraici). KUMA KU TUBA ZUWA GA ALLAH GABA 'DAYA YAA KU MUMINAI KO ZA KU RABAUTA. "



(SURATUL-NURR, AYA TA 31)


Cikin ayar an bayyanar mana da ado kala biyu ne, wato ado na tsiraici wanda aka cire fuska da tafukan hannu a matsayin wadanda suka bayyana ba a boye su. 


Sai kuma ado na tufafi (dress) wanda ba a yarda wani ya gani ba in ba cikin jerin wadanda aka ambata cikin ayar ba. 


Saboda haka yin ado (fashion) ga mace ba laifi bane, sai dai idan yayi sai ta zauna dashi cikin gidanta ta yadda wani ba zai gani ba in ba muharraminta ba. Idan kuma ya kama za su fito sai suyi fita irin ta muslimci ba irin ta jahilan farko ba. Shine Allah ya qara da cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


وَقَرۡنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجۡنَ تَبَرُّجَ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِ ٱلۡأُولَىٰۖ..............


" KUMA KU ZAUNA CIKIN GIDAJENKU (a mutunce), KUMA KADA KU FITA IRIN FITAR JAHILAN FARKO (idan har buqata ko lalurar fitar ta kama ku) ............."


        (AHZAB, AYA TA 33)


YANZU DAN ALLAH A MATSAYINKA NA MUSULMI WACCECE TAFI BURGE KA CIKIN WADANNAN MATAN ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)

17th June, 2021/ 7th Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post