Idan ka cire Annabi (S.A.W.W) babu wanda yakai Imam Ali Ilimi duk cikin hallittun Allah !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


DAGA KHUDUBAR IMAM HASSAN (A. S) 


Saboda matsayi na ilimi sai Allah (T) ya fifita Manzanninsa (A. S) dashi kan dukkan al'ummunsu. Babu wani Annabi (A. S) wanda Allah ya tayar sannan kuma ace an sami wani wanda ya fi shi ilimi. 


Kamar haka yake cikin Imamai (A. S), babu halitta daga cikin halittun Allah (T) yanda ya rayu qarqashin wani Imami sannan ace wai wannan halitta tafi Imamin wannan zamani ilimi. 


Da ace haka na kasancewa da kuwa zai zama aiko wani a matsayin Manzo ba shi da fa'ida cikin al'ummarsa, domin kuwa zai zama sanin wasu hukunce-hukunce zai riqa jinsu ne daga gare su.


Idan kuwa ya zamana cewa na qasa da kai ya fi ka sanin ilimin hukunci, to, shi yafi cancanta da jagoranci a kanka, ba wai kai ka zama jagora a kansa ba.


Saboda haka Allah (T) yasa Annabi Muhammad (S. A. W. W) ne kadai cikin Manzanni (A. S) wanda ya zama yakan san hukuncin abinda za a fada masa kafin akai qarshe yayi saukar masa da shi, domin shi (S. A. W. W) special ne. 


Kada kayi mamaki don na fadi haka. Tambayi malamai masu karantarwa a makarantu za kaji suna baka labarin wasu daga cikin dalibansu masu hazaqa, domin a duk lokacin da malami ya bude baki zai sanar da dalibai wani ilimi, to, wallahi sai ka tarar a wajen wani dalibi ya riqa ya san wannan abinda za a gaya masa. Kuma a ladabi dole shi wannan dalibi ya zama yana sauraron malaminsa ko da kuwa ya san abinda zai fada. 


Allah (T) ya bamu misali kan wannan game da Manzon Allah (S. A. W. W) inda yake cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۗ وَلَا تَعۡجَلۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مِن قَبۡلِ أَن يُقۡضَىٰٓ إِلَيۡكَ وَحۡيُهُۥۖ وَقُل رَّبِّ زِدۡنِي عِلۡمٗا ( ٤١١)


" SANNAN KUMA ALLAH MAMALLAKI NA GASKIYA YA 'DAUKAKA. KUMA KADA KAYI GAGGAWA GA QUR'ANI GABANIN A QARE YIN WAHAYINSA GARE KA. KUMA KACE, " YAA UBANGIJI KA QARAMIN ILIMI. "


    (SURATUL-'DAHA :114)


Wannan na nuna mana ne cewa Annabi (S. A. W. W) na sanin hukuncin komai bisa qudirar UbangijinSa, sai dai ba ya yin hukunci kan komai ba tare da ya jira ya ji daga Allah ba. 



Saboda haka ilimi shine fifiko, duk wanda ya fi ka ilimi ya fi ka matsayi da daraja wajen Allah. Wato ana nufin ilimi wanda ake aiki dashi. 


Allah (T) na cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَكُمۡ تَفَسَّحُواْ فِي ٱلۡمَجَٰلِسِ فَٱفۡسَحُواْ يَفۡسَحِ ٱللَّهُ لَكُمۡۖ وَإِذَا قِيلَ ٱنشُزُواْ فَٱنشُزُواْ يَرۡفَعِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ دَرَجَٰتٖۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ (١١)


" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! IDAN AKA CE MUKU, " KU YALWATA CIKIN MAJALISAI, " TO, KU YALWATA, SAI ALLAH YA YALWATA MUKU. KUMA IDAN AKA CE MUKU, " KU TASHI ," TO, KU TASHI. ALLAH NA 'DAUKAKA WADANDA SUKA YI IMANI DAGA CIKINKU DA WADANDA AKA BAIWA ILIMI DA WASU DARAJOJI. KUMA ALLAH (masani) MAI BADA LABARI NE GAME DA ABINDA KUKE AIKATAWA. "


(SURATUL-MUJADALAT:11)


Ya zo cikin wata riwaya wacce ke nuna cewa Imam Ali (A. S) shine mafi sani (ilimi) cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) kamar yadda Imam Hassan Bn Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S) ya fada. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


1651- حَدَّثَنَا وَكِيعٌ ، عَنْ شَرِيكٍ ، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ ، عَنْ هُبَيْرَةَ , خَطَبَنَا الْحَسَنُ بْنُ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، فَقَالَ : لَقَدْ فَارَقَكُمْ رَجُلٌ بِالْأَمْسِ لَمْ يَسْبِقْهُ الْأَوَّلُونَ بِعِلْمٍ ، وَلَا يُدْرِكُهُ الْآخِرُونَ ، كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ " يَبْعَثُهُ بِالرَّايَةِ : جِبْرِيلُ عَنْ يَمِينِهِ ، وَمِيكَائِيلُ عَنْ شِمَالِهِ ، لَا يَنْصَرِفُ حَتَّى يُفْتَحَ لَهُ " .


Waki'i ya bamu labari, daga Sharik, daga baban Ishaq, daga Hubairata cewa , " Hassan Bn Aliyu yayi mana Khuduba yace,


  " HAQIQA WANI MUTUM YA BARKU DA YAMMACI, WA FARKO BASU GABACE SHI A ILIMI BA, SANNAN KUMA NA QARSHE BA ZA SU RISKE SHI (a ilimin) BA. MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA KASANCE YA AIKE SHI DA TUTA (ranar Khaibar) : JIBRILU NA (tsaye) A DAMANSA KUMA MIKA'ILU NA BARIN HAGUNSA, (sannan kuma) BA ZAI JUYA BA HAR SAI ANYI MASA BUDI ."


 (Musnad Ahmad :1651)


Wannan hadisi na nuna mana ne cewa lalle anyi hasara sakamakon qin yin riqo da wanda yafi kowa ilimi a bayan Annabi (S. A. W. W). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


            (08137925034)


15th June, 2021/ 5th Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post