Ku guji yin zagi ko suka ga bayin Allah muminai !



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KA ZAMA MAI AMBATON WANI DA MAFI KYAWUN ABINDA KAKE SO A AMBACE KA DASHI


Rashin adalci da rashin tunani shine yayi yawa cikin zukatan mutane wanda yayi sanadin suna aikata abinda zai jawo musu fushin Allah.


Zagi, cin zarafi, suka ko qazafi ga wani ba addini bane, saboda haka bai kamata ga musulmin kirki ya riqa yin irin wadannan abubuwa ba. 


Ya zo cikin riwaya daga Imam Baqir (A. S) yana cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" KU FADA (magana) GA MUTANE DA MAFI KYAWUN ABINDA KUKE SO A FADA A KANKU, DOMIN ALLAH YANA FUSHI DA MAI ZAGI MAI YIN SUKA GA MUMINAI ."


Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, idan ka tashi yin magana ga dan'uwanka ka fadi magana mai kyau a kansa fiye da yadda kake so mutane su fadi kyakkyawuyar maganar a kanka. Wato ka fadi magana akan wani da irin maganar da in an ambace ta a kanka za kaji dadi da farin ciki.


Sannan kuma yana nuna mana cewa yin zagi ga wani ko suka gare shi don a baqanta shi cikin jama'a ko a cire qaunarsa cikin zukatan mutane haramun ne, domin yana jawowa mutum fadawa cikin fushin Allah.


Saboda haka babu alkhairi cikin zagi ko sukar bayin Allah muminai. Da fatan ka a kiyaye don gujewa fadawa cikin fushin Ubangiji. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


16th June, 2021/ 6th Zul-Qadah, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post