Sayyid (H) zai zama abin zargi ga wasu a duk ranar da bai zargi wadanda ake zargi ba – Inji Sheikh Ahmad Yusuf Yashi


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UUPDATED @


DAGA JAWABIN KHATAMA NA MU'UTAMAR KHASS NA DA'IRAR BAUCHI A GARIN NINGI 



Mu'utamar wanda aka shiga ranar juma'ah 11-6-2021/ 1-11-1442 aka gama yau lahadi 13-6-2021 ya sami halartar jama'a maza da mata da kuma babban baqo mai jawabi shine Sheikh Ahmad Yusuf Yashi, wakilan 'yan'uwa na da'irar Bauchi .


Ba kamar yadda aka saba gabatar da jawabin Khatama wanda ake yin tsokaci kan maudu'an da aka gabatar na tsahon wannan lokaci cikin Mu'utamar ba, wannan karo Shehin malamin ya fito da wani sabon salo ne yadda ya juyar da akalar jawabin nasa kan wani abu da ake kira (YAQI CIKIN RUWAN SANYI ).


Bayan yabo ga Allah da kuma salati ga Manzonsa (S. A. W. W) da iyalan gidansa (A. S) sai malamin yayi bayani da cewa shi dai wannan yaqi wani salo ne wanda maqiya ke amfani dashi wajen rusa gaskiya da ma'abotanta. Kuma wannan salo /hanya ana amfani da ita tun Sayyid (H) na cikin mu da kuma bayan baya cikinmu. 


Sai malamin yace amma sakamakon Sayyid (H) na cikinmu sai ya zamana shi ne yake tunkude mana ta hanyar bayyanar da dukkan wasu makirce-makirce da suke qullawa, amma sakamakon yadda yanzu ba ya cikinmu sai abubuwan suka yi muni.


Wannan matsala kuwa ita ce salon da maqiya /jahiliyya ke amfani da ita wajen rarraba kan 'yan'uwa da nuna musu rashin mutunci ko rashin ganin matsayin na gaba dasu. Yace, wannan abu yayi nisa cikin 'yan'uwa yadda takai har doke-doke ake samu cikinsu alhali da ba a san da irin wannan ba. 


Shehin malamin ya qara da cewa, insha Allahu komai za su gyaru idan su Sayyid (H) sun dawo cikinmu, sai dai kuma a lokacin wasu an riga an tafi dasu !


Babbar fitinar da 'yan'uwa za su fada cikinta idan su Sayyid (H) suka dawo cikinmu shine;

Fitinar da ya uwa zasu fada in su Sayyid suka dawo shine; Sayyid (H) zai zama abin zargi ga wasu a duk ranar da bai zargi wadanda zargi ba

" SAYYID (H) ZAI ZAMA ABIN ZAGI GA WASU A DUK RANAR DA BAI ZARGI WADANDA AKE ZARGI BA !" (In ji Shehin malamin). 


Dalili kuwa shine, yanzu 'yan'uwa sun rabawa kawukansu ayyuka na gani ko tantance wane shine akan gaskiya, wane kuma ba akan gaskiya yake ba, alhali ba wannan ne aikin dake wuyanka ba a daidai wannan lokaci. 


Shine malamin yayi kira ga 'yan'uwa kan cewa kowa yayi haquri da wannan aikin Shaidan din, mu saurara har zuwa lokacin da su Sayyid (H) za su fito muji daga bakinsu. Har ya kawo ayar nan da ke cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ


يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ (١)


" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! KADA KU GABACI ALLAH DA MANZONSA (cikin yanke hukunci kan dukkan wasu al'amranku), KUJI TSORON ALLAH. LALLE ALLAH MAI JI NE (kuma) MASANI. "


 (SURATUL-HUJRAAT:1)


Yace kada mu zama kamar mutanen Annabi Musa (A. S) yayin da ya bar musu Haruna (A. S) a matsayin jagoransu, su kuma suka ga hakan ba daidai bane. Sai suka riqi 'Dan Maraqi maimakon su saurara har Musa (A. S) ya dawo suji daga bakinsa. 


Cikin jawabin nasa mai ratsa zukata sai da ya gargadi mahalarta da su guji zama suna yi da junansu wanda hakan bai dace ga mumini ba. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


......وَلَا تَجَسَّسُواْ وَلَا يَغۡتَب بَّعۡضُكُم بَعۡضًاۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمۡ أَن يَأۡكُلَ لَحۡمَ أَخِيهِ مَيۡتٗا فَكَرِهۡتُمُوهُۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ......"


"......KUMA KADA KU ZAMA 'YAN RAHOTU, KUMA KADA SASHENKU YA RIQA GIBAR SASHE . YANZU 'DAYANKU SO YAKE YACI NAMAN 'DAN'UWANSA YANA MATACCE ? KU QI CI KUMA KUJI TSORON ALLAH ........"


      (SURATUL-HUJRAT:12)


Yace, wannan ba qaramin zunubi bane ace mutum zai zauna yana yi da wani dan'uwansa musulmi. 


Ya qara da cewa, " WANNAN KENAN (giba), AMMA KUMA YIN QAZAFI GA WANI YA FI MUNI FIYE DA WANDA YAKE CIN NAMAN DAN'UWANSA. "


A qarshe yayi addu'ar Allah ya gaggauta qwato mana jagoranmu tare da yin addu'a Khaas ga 'yar'uwa malama A'ishatu Adamu matar wakilin 'yan'uwa na garin Ningi wacce Allah ya karbi ranta ranar juma'ah da daddare. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


13th June, 2021/ 3rd Zul-Qada, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post