@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A ma'ana ta Luga idan aka ce Sunnah ana nufin dukkan wani abu ne wanda wani ya aikata shi a aikace cikin ayyukansa. Zai iya kasancewa mummuniyar sunnah ko kyakkyawuya, kuma dukkan wanda yayi koyi dashi yakan iya samun sakamakon irin wannan aiki nasa.
Ita kuma Shi'a a Luga tana nufin mabiya ne, wannan biyayya kuwa ko da wa ake bi, mutumin kirki ne ko Shaidan ne, duk wanda yayi jagoranci akan kowanne irin abu, to, wadanda suka bi shi sun zama Shi'arsa.
A ma'ana ta shari'a kuwa idan kaji ance Sunneey, to, ana nufin wanda ya yarda da jagorancin Abubakar ne a matsayin Khalifa bayan Manzon Allah (S. A. W. W) kuma ya yarda cewa shiryayyun Khalifofi hudu (4) a bayan Annabi (S. A. W. W).
Ita kuwa kalmar Shi'eey a shari'a ta muslimci tana nufin wanda ya yarda da cewa Imam Ali (A. S) shine wasiyyin Manzon Allah (S. A. W. W) na farko daga cikin Khalifofi goma sha (12) shiryayyu a bayansa (S. A. W. W).
MA'ANAR KALMAR AHLUS-SUNNAH
Ita ma'anar Ahlus-Sunnah tana nufin wanda yake yin koyi ne da Manzon Allah (S. A. W. W) cikin dukkan ayyukansa, kuma yabi umarninsa a bayansa, sannan ya nisanci abin yayi hani a kansa.
Duk wanda ya kasance yana bin sunnar Manzon Allah (S. A. W. W) kuma ya yarda cewa Annabi (S. A. W. W) yace Khalifofi a bayansa goma sha biyu (12) ne, to, wannan mutumin sunansa Shi'eey .
Wannan dalili yasa ake samun Shi'eey daga cikin Sunnah, amma ba a samun Sunneey cikin Shi'eey.
Bisa ma'anar da muka kawo ta Ahlus-Sunnah za mu iya fahintar cewa dukkan Shi'eey Ahlus-Sunnah ne , sannan kuma ana samun Shi'eey cikin sunnah, sai dai ba a taba samun Shi'eey daga cikin Sunney, domin su babu yarda cewa Imam Ali (A. S) ne Halifan farko bayan Annabi (S. A. W. W) ba.
DA FATAN AN FAHINCI WANNAN GAJEREN RUBUTU NAWA.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
15th June, 2021/ 5th Zul-Qadah, 1442.