Yin Lecture A Maqabarta Ko Dai Qirqiro Sabuwar Bid'ah ??


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


QUR'ANI DA MUTUWA A MATSAYIN MANYAN WA'AZOZIN DA AKA BAR MANA 


Yana daga cikin hadisin da malaman Izala suka dogara dashi wajen hange da tantance wasu ayyukan da ake aikatawa cikin muslimci suna ambatonsu a matsayin bid'ah, har ma suka daukarwa kansu aikin kawar da ita. Sai dai cikin wannan qoqari nasu sun manta babbar bid'ar da Umar Bn Khaddab ya qirqirota na yin sallar Tarawihi cikin jam'i har ya kirata da cewa, " NI'IMA BI BID'ATU HAAZIHI. " Cikin Muwadda-Malik.


Hadisin da suke kawowa shine wai Annabi (S. A. W. W) yace; 


" NA HANE KU DA WASU FARARRUN AL'AMRA, DOMIN KOWACCE BID'AH 'BATA CE, KUMA KOWACCE BATA NA CIKIN WUTA ." 


Kafin wannan lokaci anyi wani zamani wanda da zarar anyi jana'izar mutum aka binne shi sai 'yan Izala su juya cikin gaggawa tamkar wadanda dama a dole suke tare da wannan gawa. Su kuma sauran al'ummar musulmi sukan tsaya suyi ta yin addu'o'in neman gafara ga wannan mamaci da ma sauran wadanda aka tarar a wannan guri.


Lokacin da suka soma karatu ta hanyar hujjojin da masu tsayawa suna yin wannan addu'a suke ba su cikin littafan dake hannayensu wadanda ba sa karatu ballantana su san su, sai suka soma qoqarin nunawa mutane cewa kowa zai iya tsayawa yayi addu'ah amma ba cikin jam'i ba, suna yi cikin hikima don kada a gano su cewa su yanzu suka soma sanin haka.


Yanzu kuma sun fito da wata sabuwar bid'ah mafi muni wacce tarihi bai taba hakaito irinta ba, ita ce yin lecture yayin da aka gama bisne mamaci. 


Sukan dau lokaci mai tsaho suna yin wannan lecture wacce babu ita cikin sunnar Annabi (S. A. W. W) ko wasu magabata, amma su a fahintarsu aikin alkhairi suke yi, alhali shine mafi muni cikin bid'o'i qirqirarru. 


Sunce wai Annabi (S. A. W. W) yace; 


" NA BAR MUKU WA'AZOZI GUDA BIYU, MAI MAGANA DA MARAR MAGANA. "


Suka ce mai magana cikin Qur'ani, shiru kuma mutuwa. Duk da cewa qarya ce, amma in da ma ace ya inganta cewa mutuwa ita ce wa'azi mai shiru, to, me yasa idan an mutu ba za abar mutuwar tayi aikinta ba (wa'azi) sai dai kawai kaji wani yana yin lecture a maqabarta maimakon aikata abinda Annabi (S. A. W. W) yace ayi, shine addu'ah? 


Abinda Annabi (S. A. W. W) ke fada idan an gama bisne mutum shine, " KU NEMAWA 'DAN'UWANKU GAFARA DA TABBATUWA, DOMIN A YANZU HAKA ANA YI MASA TAMBAYA ."


A tarihin muslimci ko nace sunnar Annabi (S. A. W. W) babu yin lecture a Maqabarta. Saboda haka wannan ita ce babban bidi'ah mai lasisi wacce mutane da dama ke kwaikwaya daga wadanda suka qirqirota. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


         (08137925034)


12th May, 2021/ 1st Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post