Yan uwa almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Ahlul-Duthur sun raba kayan abinci ga Iyalan Shahidai da sauran al'ummar gari mabuƙata a Jahar Adamawa Jiya Asabar 1/May/2021.
Wakilin Mu'assasatu Shahada na yankin Adamawa shine ya raba kayan ga Iyalan Shahidai, sannan kuma aka raba wasu ga al'umman gari mabuƙata domin taimakawa a cikin wannan wata na Ramadan. An raba kayan ne a madadin Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da gwamnatin Najeriya take cigaba da tsarewa sama da shekaru 5. Allah ya sakawa Sheikh Zakzaky da Alkairi.
Tags:
Labaran Duniya