Mutuwa rigar kowa; Allah Ya jikan Musulmi.
Daga darussan wannan janazar akwai cewa gawarwakin Musulmi ne Ahlussunnah, amma kun ga irin akwatun da aka musu makara da shi. Sannan aka dora musu tutar Nigeria a kansu. Kuma dai malamai ne suka sallace su, sannan ba wata surutai ko Ai' batawada mutane ke yi.
Wannan ya kamata ya kawo karshen sukan da ake wa yan Shi'a, almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky kan yin makara da akwati da suke yi, ko saka fulawa ko Tuta mai dauke da sunan Allah ga mamatansu a yayin janaza.
Musamman ma da yake duk ba ana bizne su da makara (akwatun) bane, kawai yana matsayin makara ne, wanda shi kuma kawai al'ada ne ya zo mana da irin makaran da muka fi sani a kasar Hausa, amma a kasashe da dama akwati ne na katako ko na karfe ba na Asabari ko Azara ko Itace ba.
Har ila yau, idan kun duba makabartan sojojin, za ku ga yadda ake gyara shi, a jere yake, sannan ana gini a kansa me kyau tare da barin tazara a tsakaninsu da shaida da sauransu. Ba wanda zai ji tsoron ya je wajen. Kuma dai duk Musulmi ne da fatawar Malaman Sunnah hakan ya halatta har ake yi a Nijeriya.
Wannan ma ya kamata ya yayewa wasu subuhohin da suke rayawa kansu dangane da makabartan yan uwa Shahidai almajiran Shaikh Zakzaky da ke Darur Rahma da yake a gyare tsaf, a jere cike da tsafta wanda hakan ya ba kowa damar ziyarar su a ko da yaushe ba tare da tsoro ba.
Kuma haka ne makabartu suke a duk kasashen Musulmi da suka ci gaba, wadanda al'ada bai danne su sun dauka cewa in mutum ya mutu ya gama amfani, ya zama abin gudu da mantawa ba.
Har ila yau, ku kalli matar Marigayi Attahiru mana, ana ce ta zo tai bankwana da gawar mijinta sai ta sako baƙaƙen kaya ƙirin ta taho tana kuka, ba ta saka farare ba. Kuma ita dai ba Shi'a bace. Wanda hakan ke nuna maka bakin kaya ko a hankalce da ma ilmamce yana nuni ne da alamar damuwa da jimami a wani lokaci, ba Shi'a kawai ke sakawa ba. Kuma idan Shi'a sun saka don nuna juyayi ko bakin ciki bai dace su zama abin zargi ko izgili ba.
Mun ga ma dai har fareti aka yi da gawarwakin nasu a matsayin su na gwaraza ko? Kuma Musulmi ne su Ahlussunnah, sannan a gaban malamai ko? Tohm.
Matan mamatan sojojin nan da iyalansu su godewa Allah, su sun ga gawarwakin yan uwansu har sun musu janaza, mu mata da yan uwanmu suna nan yau shekara fiye da biyar da sojoji suka kashe yan uwansu da mazajensu kusan 1000 har yau ba su samu gawar ko mutum daya ba. Sojojin bisa shawarar Gwamna Elrufai sun je sun haka rami a Mando da ke Kaduna sun bizne duk gawarwakin mutanen, cikinsu har da wadanda da ransu basu karisa ba. 😭
Allah Ya mana sakayya a kan azzalumai.