BASU YARDA CEWA ANNABI (S. A. W. W) YA HANA UMAR YIWA MUTANE SALLAH BA, AMMA SUN YARDA CEWA UMAR YA HANA ANNABI (S. A. W. W) BARIN MATANSA SUNA YAWO BABU HIJABI !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Idan anyi irin wannan magana sai wasu suga kamar qarya ne, amma kuma aikin wadanda ake magana a kan nasu ya tabbatar da hakan.
Cikin rubutunmu na baya mun kawo nassi wanda ya nuna cewa Annabi (S. A. W.W) ya hana Umar yiwa mutane sallah don rashin cancantar jagorncinsa sai mutane suka yi caaaaa a kanmu suna fadar munanan maganganu da rashin jin dadin hakan. Kuma suke ta kumfar baki don su nuna Umar mai wata daraja ce ba tare da hangen rashin cancantarsa ba.
Ga riwayoyin da muka kawo
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
4662- حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ مُحَمَّدٍ النُّفَيْلِيُّ حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ سَلَمَةَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ إِسْحَاقَ قَالَ: حَدَّثَنِي الزُّهْرِيُّ حَدَّثَنِي عَبْدُ الْمَلِكِ بْنُ أَبِي بَكْرِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ الْحَارِثِ بْنِ هِشَامٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ زَمْعَةَ قَالَ لَمَّا اسْتُعِزَّ بِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَنَا عِنْدَهُ فِي نَفَرٍ مِنَ الْمُسْلِمِينَ دَعَاهُ بِلاَلٌ إِلَى الصَّلاَةِ فَقَالَ مُرُوا مَنْ يُصَلِّي لِلنَّاسِ. فَخَرَجَ عَبْدُ اللَّهِ بْنُ زَمَعَةَ فَإِذَا عُمَرُ فِي النَّاسِ وَكَانَ أَبُو بَكْرٍ غَائِبًا فَقُلْتُ يَا عُمَرُ قُمْ فَصَلِّ بِالنَّاسِ فَتَقَدَّمَ فَكَبَّرَ فَلَمَّا سَمِعَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَوْتَهُ وَكَانَ عُمَرُ رَجُلاً مُجْهِرًا قَالَ: ((فَأَيْنَ أَبُو بَكْرٍ يَأْبَى اللَّهُ ذَلِكَ وَالْمُسْلِمُونَ يَأْبَى اللَّهُ ذَلِكَ وَالْمُسْلِمُونَ)). فَبَعَثَ إِلَى أَبِي بَكْرٍ فَجَاءَ بَعْدَ أَنْ صَلَّى عُمَرُ تِلْكَ الصَّلاَةَ فَصَلَّى بِالنَّاسِ.
Abdullahi Bn Muhammad Annufailiy ya bamu labari, Muhammad Bn Sulaiman ya bamu labari daga Muhammad Bn Ishaq yace: Zuhriy ya bamu labari, Abdul-Malik Bn Abubakar Bn Abdurrahman Bn Harith Bn Hishaam ya bamu labari daga babansa daga Abdullahi Bn Zam'ata yace;
" Yayin da (jinya) ta tsananta ga Manzon Allah (S. A. W. W) ni kuma ina tare dashi cikin wasu jama'a daga musulmai sai Bilal ya kiraye Shi zuwa ga sallah. Sai yace; " KU UMARCI WANDA ZAI YIWA MUTANE SALLAH. " Sai Abdullahi Bn Zam'ata ya fita, sai yaga Umar cikin mutanen, Abubakar kuma ba ya nan. Sai nace, " Yaa Umar, ka tashi ka yiwa mutane sallah. Sai ya wuce yayi kabbara. Yayin da Manzon Allah (S. A. W. W) yaji sautinsa, da ma Umar ya kasance mutum mai bayyanar (da karatu ne yadda mutane daga nesa suna jin muryarsa), sai (Manzon Allah) yace;
" INA ABUBAKAR YAKE ! ALLAH YA DA MUTANE SUNQI HAKA (basu yardar da sallar Umar ba), ALLAH DA MUTANE SUNQI HAKA. "
Sai aka aika zuwa ga Abubakar, sai yazo bayan har Umar ya riga yayi wannan sallah. Sai (Abubakar) ya yiwa mutane (sabuwar) sallah. "
4663- حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ صَالِحٍ حَدَّثَنَا ابْنُ أَبِي فُدَيْكٍ قَالَ: حَدَّثَنِي مُوسَى بْنُ يَعْقُوبَ عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ إِسْحَاقَ عَنِ ابْنِ شِهَابٍ عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُتْبَةَ أَنَّ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ زَمْعَةَ أَخْبَرَهُ بِهَذَا الْخَبَرِ قَالَ لَمَّا سَمِعَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَوْتَ عُمَرَ قَالَ ابْنُ زَمَعَةَ خَرَجَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَتَّى أَطْلَعَ رَأْسَهُ مِنْ حُجْرَتِهِ ثُمَّ قَالَ: ((لاَ لاَ لاَ لِيُصَلِّ لِلنَّاسِ ابْنُ أَبِي قُحَافَةَ)). يَقُولُ ذَلِكَ مُغْضَبًا.
Ahmad Bn Sahih ya bamu labari, Ibn Abiy Fudaik ya bamu labari yace; Musa Bn Ya'aqub ya bani labari Abdurrahman Bn Ishaq, daga Ibn Shihaab, daga Ubaidullahi Bn Abdullahi Utbabata, cewa Abdullahi Bn Zam'ata ya bashi labari irin wannan labari, yace; " Yayin da Annabi (S. A. W. W) yaji sautin Umar. Ibn Zam'ata yace, sai Annabi (S. A. W. W) ya fita har ana ganin kansa daga cikin dakinsa, sa'an nan yace;
" A'A ! A'A !! A'A !!! IBN QUHAFATA NE ZAI YIWA MUTANE SALLAH (ba Umar ba) !"
Yana fadar haka a fusace (inji Ibn Zam'ata)
(SUNAN ABU DAWUD, BABUN ISTIKHLAFI ABUBAKAR, HADISI MAI LAMBA 4662-4663)
Wannan magana bata yiwa wasu dadi ba saboda su a fahintarsu so ake a qasqantar da Umar, amma kuma sun yarda Annabi ya qasqanta matuqar za a samarwa Umar wata falala ta qarya.
Ga misali nan kamar haka
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
146 - حدثنا يحيى بن بكير قال: حدثنا الليث قال: حدثنا عقيل، عن ابن شهاب، عن عروة، عن عائشة:
أن أزواج النبي صلى الله عليه وسلم كن يخرجن بالليل إذا تبرزن إلى المناصع، وهو صعيد أفيح، فكان عمر يقول للنبي صلى الله عليه وسلم: احجب نساءك، فلم يكن رسول الله صلى الله عليه وسلم يفعل، فخرجت سودة بنت زمعة، زوج النبي صلى الله عليه وسلم، ليلة من الليالي عشاء، وكانت امرأة طويلة، فناداها عمر: ألا قد عرفناك يا سودة، حرصا على أن ينزل الحجاب، فأنزل الله آية الحجاب
وحدثنا زكرياء قال: حدثنا أبو أسامة عن هشام بن عروة عن أبيه عن عائشة، عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: (قد أذن أن تخرجن في حاجتكن)
Yahya Bn Bukhairi ya bamu labari yace; Laithee yace: Aqeelu ya bamu labari daga Ibn Shihab, daga Urwata, daga A'isha cewa;
Lalle matan Annabi (S. A. W. W) sun kasance suna fita da daddare idan suka yi nufin fita zuwa wasu gurare (na biyan buqatunsu), shi kuma wani guri ne a sarari (yadda kowa zai iya ganinka). Shi kuma Umar ya kasance yana fadawa Annabi (S. A. W. W) cewa;
" KA TSARE MATANKA (kamar yadda muke tsare namu, don bai dace ace kana barinsu suna fita kowa na kallonsu ba). Amma Manzon Allah (S. A. W. W) ya qi ya aikata (abinda Umar ke fada masa in ji A'ishatu) . Sai Saudatu Bnt Zam'ata matar Annabi (S. A. W. W) ta fita cikin dare daga darare . Kuma ta kasance mata ce doguwa, sai Umar (ya ganta) ya kirata cewa;
" LALLE NA GANE KI FA YAA SAUDATU ! Yana kwadayin a saukar da Hijabi, sai Allah ya saukar da ayar Hijabi. "
Kuma Zakariyyah ya bamu labari yace; Baban Usamata ya bamu labari daga Hishaam Bn Urwata daga babansa daga A'isha, daga Annabi (S. A. W. W) yace;
" HAQIQA ANYI IZNI CEWA KU FITA SABODA BUQATUNKU. "
(SAHIHUL-BUKHARI, KITABUL WUDHU'I, BABUN KURUUJUN-NISA'I ILAL BARAAZ, HADISI NA 146)
ABIN LURA
----------------------
Abinda ake nuna mana cikin wannan hadisi shine Umar ya fi Annabi (S. A. W. W) tunani da sanin ya kamata, domin shi ya tsare matansa amma Annabi (S. A. W. W) na barin nasa suna aikata abinda bai dace ba. Yayi qoqarin nunawa Annabi wannan matsala amma ya qi yabi, sai da Allah ya fada masa da kansa kafin ya yarda.
Abin tambaya anan shine, shi Umar din a ina yasan hukuncin Hijabi har yake kwadayin a saukar da aya kan haka.
Dukkan mai imani dai ya san duk wata shari'a ta muslimci an santa ne ta hanyar Annabi (S. A. W. W), amma kuma anan ana nuna cewa ta hanyar Umar ake sanin wasu hukunci na addini, kuma ma Allah yana koyi dashi ne.
To, da shike wannan hadisi na goyon bayan Umar ne sai suna kafa hujja da shi cewa ta dalilinsa ne aka saukar da ayar Hijabi. Amma kuma ba sa la'akari da cewa suna tozarta Annabi (S. A. W. W) tunda shi bai san daidai ba, kuma ko an gaya masa gaskiya ba ya dauka.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
22nd May, 2021/ 11th Shawwal, 1442.