Umarnin ubana ko na Manzon Allah zan bi, Inji Ibn Umar


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


TUHUMAR DA YAKE YI KAN MASU GANIN UMARNIN BABANSA YA FI NA ANNABI (S. A. W. W) 


Cikin karatuka da dama za ka riqa cin karo da abubuwa wadanda Manzon Allah (S. A. W. W) ya halasta ko yayi umarni da a aikatawa, amma kuma sai kaga an sami Umar Bn Khaddab ya fito qarara ya haramta ba ya ko yin shakka ko tunanin abinda zai iya biyowa baya, yin hakan kuwa qoqarin ruguje/rushe ginin da Manzon Allah (S. A. W. W) yayi shekaru 23 yana ginawa ne. 


Ba zai zama abin mamaki ba don an sami wadanda suka fito suka goya masa baya, domin da yawa sun karbi muslimci ba bisa son ransu ko ganin lalle ya kamata addinin Allah ya zama shine addinin gaskiya ba. Saboda haka kuwa dole su goya masa baya ta kowacce fuska don ganin burinsu ya cika. 


Sai dai kuma duk da hakan ba za a rasa masu tsayuwa kan aikata gaskiya da binta ba, domin alqawarin Allah ne da Manzonsa (S. A. W. W) cewa ba za a rasa al'umma wacce za ta tsaya kan gaskiya ba har tashin alqiyama. 


Abinda muke son kawowa anan shine batun TAMATTU'I na aikin Hajji. Bisa umarni da aikin Manzon Allah (S. A. W. W) aka soma yin TAMATTU'I, wato hada aikin Umra tare da Hajji, kuma har Annabi (S. A. W. W) ya bar duniya akan wannan halaccin ake. 


Zuwa lokacin da Umar ne ya zama Sarki sai yace shi ya haramta abinda Annabi (S. A. W. W), kuma zai hukunta dukkan wanda ya aikata, ka san kowanne Sarki da irin nasa salon mulkin. 


Bari dai mu kawo muku riwayar don ganewa da idanuwanku. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


(1)- ...أنه سمع سعد بن أبي وقاص والضحاك بن قيس وهما يذكران التمتع بالعمرة إلى الحج فقال الضحاك بن قيس لا يصنع ذلك إلا من جهل أمر الله فقال سعد بئس ما قلت يا بن أخي فقال الضحاك بن قيس فإن عمر بن الخطاب قد نهى عن ذلك فقال سعد قد صنعها رسول الله صلى الله عليه وسلم وصنعناها معه قال هذا حديث صحيح



...Cewa ya ji Sa'ad Bn Abiy Waqqas da Dhahaak Bn Qais suna ambaton Tamattu'i da Umra zuwa Hajji, sai Dhahaak Bn Qais yace, " Ai babu mai aikata haka sai dai Wanda ya jahilci umarnin Allah ."


Sai Sa'ad yace, " TIR DA ABINDA KA FADA YAA 'DAN 'DAN'UWA !" Sai Dhahaak Bn Qais yace, " To, ai Umar Bn Khaddab yayi hani kan haka. "


Sai Sa'ad yace, " TO, HAQIQA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA AIKATA, KUMA MUMA MUN AIKATA TARE DASHI. "


Mai riwayar yace, wannan hadisi ingantacce ne. 


(2)- أنه سمع رجلا من أهل الشام وهو يسأل عبد الله بن عمر عن التمتع بالعمرة إلى الحج فقال عبد الله بن عمر هي حلال فقال الشامي إن أباك قد نهى عنها فقال عبد الله بن عمر أرأيت إن كان أبي نهى عنها وصنعها رسول الله صلى الله عليه وسلم أأمر أبي نتبع أم أمر رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال الرجل بل أمر رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال لقد صنعها رسول الله صلى الله عليه وسلم قال وفي الباب عن علي وعثمان وجابر وسعد وأسماء بنت أبي بكر وابن عمر قال أبو عيسى حديث بن عباس 


حديث حسن



Cewa shi ya ji wani mutum daga mutanen Sham yana tambayar Abdullahi Bn Umar game da Tamattu'i da Umra zuwa Hajji, sai Abdullahi Bn Umar yace, " ITA HALAL CE !"


Sai shi mutumin Sham din yace, " Amma ai Ubanka yayi hani game da hakan. "


Sai Abdullahi Bn Umar yace, " SAI MENENE KUMA DON UBANA YA YAYI HANI A KANTA ALHALI MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA AIKATA. SHIN, UMARNIN UBANA ZAN BI KO KUMA UMARNIN MANZON ALLAH (S. A. W. W) ?"


Sai wani mutum yace, " A'a, umarnin Manzon Allah (A. A. W. W) za ka bi. "


Sai (Ibn Umar) yace, " HAQIQA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA AIKATA TA ! "



(JAMI'US-SAHIH LI TIRMIDHI, KITABUL-HAJJ, BABUN MAA JAA'A FI TAMATTU'I)


Kunga wannan abinda Ibn Umar yayi shine daidai, domin ba yin biyayya ga wani Qato wajen saba umarnin Allah ko na Manzonsa (S. A. W. W) ko shi wanene kuwa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


6TH MAY, 2021/ 24TH RAMADAN, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post