@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ANNABI (S. A. W. W) YA AIKATA HAKA (IN JI) UMMUL-MUMININA A'ISHA
Shi bayyanar da tsiraici haramun ne ga wanda ba muharraminka ba, kuma ko da muharramin ne bai kamata a riqa bayyanar da tsiraicin juna ana kallo ba. Kallon tsiraici ko da naka ne yana da illa, domin na ji Imam Ali (A. S) na cewa, " KALLON TSIRAICI YANA RAQE QARFIN IDO 👀. "
Sannan kuma babban dalilin da yasa akayi umarnin yin sallama da neman izni kafin shiga gida shine don gujewa kallon tsiraici (dukkan wani abinda mai shi ba ya so a gani) . Saboda haka ko da iyalinka ne ke cikin daki kuma ka san tana tsirara bai dace ka shiga cikin dakin kai tsaye ba tare da yin sallama ba, domin akwai yiwuwar ka ganta cikin wani hali wanta ita kanta ba za taso ka ganta a haka ba.
Za mu iya ganin haka cikin wannan hadisi kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
حدثنا قتيبة حدثنا بن لهيعة عن عبيد الله بن أبي جعفر عن أبي عبد الرحمن الحبلي عن أبي ذر قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم من كشف سترا فأدخل بصره في البيت قبل أن يؤذن له فرأى عورة أهله فقد أتى حدا لا يحل له أن يأتيه لو أنه حين أدخل بصره استقبله رجل ففقأ عينيه ما غيرت عليه وإن مر الرجل على باب لا ستر له غير مغلق فنظر فلا خطيئة عليه إنما الخطيئة على أهل البيت وفي الباب عن أبي هريرة وأبي أمامة قال أبو عيسى هذا حديث غريب لا نعرفه مثل هذا إلا من حديث بن لهيعة وأبو عبد الرحمن الحبلي اسمه عبد الله بن يزيد
Qutaibata ya bamu labari, Ibn Luhai'ata ya bama labari daga Abdullahi Bn Abiy Ja'afar, daga Abiy Abdurrahman Al-Habliy, daga Abu Zarr yace, Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" WANDA YA YAYE SITIRA YA SHIGAR DA GANINSA (👀) CIKIN GIDA KAFIN AYI MASA IZNI , SAI YAGA TSIRAICIN MAI SHI (gidan), TO, HAQIQA YA JEWA IYAKAR DA BATA HALASTA GARE SHI YA JE MATA BA. KUMA DA ACE YAYIN DA YA KALLI (cikin gidan) SAI WANI MUTUM YA GAN SHI YA JEFI IDANUWANSA, TO, DA BA ZAN CANZA (wannan hukunci) DA YAYI (na jefe masa ido) BA . KUMA DA ACE MUTUM ZAI WUCE TA QOFA WACCE BA TA DA SITIRA WACCE BA A KULLE BA, SAI YA KALLI (cikinsa), TO, BABU LAIFI A KANSA, LAIFIN YANA KAN MASU GIDAN NE ."......
Wannan hadisi na nuna mana haramcin ganin tsiraicin wani ne, ko kuma shi yaga naka.
To, idan kuwa Annabi (S. A. W. W) zai haramta wannan ba za mu taba tsammanin shi kuma da kansa zai bayyanar da tsirecinsa (S. A. W. W) ga wani ba, domin hakan zai zama tamkar mai yin hani ga mummunan aiki ne shi kuma yana aikatawa.
Amma dai ku biyo mu cikin wannan hadisi dake tafe.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
(2951)- حدثنا محمد بن إسماعيل حدثنا إبراهيم بن يحيى بن محمد بن عباد المدني حدثني أبي يحيى بن محمد عن محمد بن إسحاق عن محمد بن مسلم الزهري عن عروة بن الزبير عن عائشة قالت قدم زيد بن حارثة المدينة ورسول الله صلى الله عليه وسلم في بيتي فأتاه فقرع الباب فقام إليه رسول الله صلى الله عليه وسلم عريانا يجر ثوبه والله ما رأيته عريانا قبله ولا بعده فأعتنقه وقبله قال أبو عيسى هذا حديث حسن غريب لا نعرفه من حديث الزهري إلا من هذا الوجه
Muhammad Bn Isma'il ya bamu labari, Ibrahim Ibn Yahaya Bn Muhammad Bn Muhammad ya bamu labari, baban Yahya Bn Muhammad ya bamu labari daga Muhammad Bn Ishaq, daga Muhammad Bn Muslim Al-Zuhriy, daga Urwata Bn Zubair , daga A'ishatu tace;
" ZAID BN HAARITHATA YA ZO MADINAH, MANZON ALLAH (S. A. W. W) KUWA NA GIDANA (a wannan lokaci), SAI YAZO MASA YA QWANQWASA QOFA. SAI MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA MIQE TSIRARA (babu sitira a jikinsa) ZUWA GARE SHI YANA JAN TUFAFINSA (a qasa). WALLAHI BAN TABA GANINSA TSIRARA KAFIN WANNAN LOKACI BA, HAKA MA BAYAN WANNAN LOKACI, YA RUNGUME SHI KUMA YA SUMBACE SHI (haka tsirara) "
Tirmidhi yace, wannan hadisi mai kyau ne (bisa Rijal dake cikinsa), sai dai baqo ne, domin bamu san shi cikin hadisin Zuhri ba sai dai ta wannan fuska.
(JAMI'US-SAHIH LI TIRMIDHI, KITABUN ISTI'IZAAN, BABUN MAA JAA'A FEE TANAQQU'I WAL QUBLATA)
Ni dai dana karanta wannan hadisi ya tayar min da hankali, domin har na kasa fahintar abinda ake son fitarwa cikinsa, domin aiki ne na muni wanda ake son tabbatar mana cewa Manzon Allah (S. A. W. W) ya aikata shi da kansa, alhali kuwa mu an haramta mana bayyanar da tsirecinmu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
10th May, 2021/ 28th Ramadan, 1442.