Shin, Umar shugaban samarin aljanna ne ko na dattawan cikin su??


 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


AMSA DAGA BAKIN ANAS BN MALIK 


Yana da kyau irin wadannan tambayoyi, domin na san da za a jefa wannan tambaya cikin mutane a matsayin jarrabawa da kuwa za ka ji amsoshi ne mabambanta kamar haka :-


(1)- Wani zai iya cewa na Samarin Aljannah ne.


(2)- Wani kuma zai ce na Dattawa ne. 


(3)- Wani kuma ce maka zai yi ai ba shi cikin 'yan Aljannah.


(4)- Wani kuma zai ce maka ne, a Aljannah ana samun Dattawa ne ballantana har a sami Shugabansu? D. S


Mafita anan ita ce bin umarnin Allah (T) inda yake cewa; 


" KU TAMBAYI MA'ABOTA SANI IDAN KU BA KU SANI BA. "


Saboda haka yau mun zabi malam Anas ne ya zama wanda zai raba mana wannan gardamar. 


BISMILLAH MALAM ANAS 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



3364 - «دخلت الجنة فإذا أنا بقصر من ذهب فقلت: لمن هذا القصر؟ قالوا: لشاب من قريش فظننت أني أنا هو فقلت: ومن هو؟ قالوا: عمر بن الخطاب فلولا ما علمت من غيرتك لدخلته» .

(صحيح) ... [حم ت حب] عن أنس [حم ق] عن جابر [حم] عن بريدة ومعاذ. الصحيحة 1405، 1423.


(Malam Anas ya bada amsa da ) cewa ; " Na shiga Aljannah sai ga ni kusa da wani Beni (upstairs) na Zinari, sai nace, wannan Benin na wanene ?" (Sai 'yan Aljannan) suka ce, " NA WANI MATASHI (youth) NE DAGA CIKIN QURAISHAWA ." Sai nayi tsammanin nine shi, sai nace, To, wanene shi ?"


Suka ce, " UMAR BN KHADDAB NE ."


(Anas) yace, " Da ba don na san irin kishin ka ba (yaa Umar), da na shige shi ."


(SAHIHU JAMI'US-SAGEER)


Amsar da tazo mana anan daga bakin malam Anas ita ce, Umar dai wani matashi shi wanda akayi masa tanadin gida a Aljannah. 


 AKRAMAKALLAHU GA WATA TAMBAYA 


Shin, wato Umar dai wani matashi ne kuma a matashinsa zai shiga Aljannah kenan ko kuma dai akwai wani qarin bayani ?



حدثنا الحسن بن الصباح البزار حدثنا محمد بن كثير العبدي عن الأوزاعي عن قتادة عن أنس قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لأبي بكر وعمر هذان سيدا كهول أهل الجنة من الأولين والآخرين إلا النبيين والمرسلين قال هذا حديث حسن غريب من هذا الوجه


Hassan Bn Salih Al-Bazariy ya bamu labari, Muhammad Bn Katheer Al-Abdiy ya bamu labari daga Awzaa'iy, daga Qatadata, daga Anas yace, Manzon Allah (S. A. W. W) ya cewa Abubakar da Umar; 


" WADANNAN BIYUN SUNE SHUGABANNIN DATTAWAN 'YAN ALJANNAH TUN DAGA NA FARKO HAR NA QARSHE IN KA CIRE ANNABAWA DA MANZANNI (A. S) ."


(JAMI'US-SAHIH LI TIRMIDHI, KITABUN MANAQEEB, BABUN MANAQIBUL ABUBAKAR WA UMAR)


To malam mun gode, amma gaskiya wadannan amsoshi naka sun daure min kai, domin cikin hadisin farko ka nuna cewa Umar matashi ne, kuma har gida aka tanadar masa na musamman.


Amma kuma cikin hadisi na biyu sai ka nuna cewa wai Annabi yace Umar da Abubakar shugabannin Dattawa ne a Aljannah. 


Idan hakane ya nuna cewa waccan gida na matashin Quraishawan ba nasa bane kenan ko tunda dai shi Dattijo ne ?


Sannan kuma ma ai an sami hadisai ingantattu da suka nuna cewa cikin Aljannah gaba daya matasa ne babu Dattawa, in kuwa hakane ya zama babu su cikin Aljannah kenan ko kuma ya al'amarin yake ?


SAI MUN QARA JI DAGA GARE KA 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


          (08137925034)


7TH MAY, 2021/ 25TH RAMADAN, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post