@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
IMAMANCIN IMAM ALI (A. S) DAGA ALLAH NE DA MANZONSA (S. A. W. W)
Kalmar wasiyyah tana daukar fuska biyu ne a mahangar muslimci, domin takan iya zama ta hanyar furuci ko rubutu. Idan mutum ya furta maka a baki cewa dan Allah bayan raina ka kula min da 'ya'yana ko kuma ka gani a rubuce bayan wafatinsa, to, wannan shi ake kira wasiyyah.
Malaman Sunnah sun tafi ne kan cewa wai Annabi (S. A. W. W) bai yi wasiyya da wanda zai gaje shi a bayansa ba sai dai ishara, kuma wannan ishara akan Abubakar aka yi ta. Sai dai abinda wasu basu gane ko fahinta ba shine, sun tafi kan wannan fahinta ta rashin yin wasiyyah ne domin sunqi bin wasiyyar da Annabi (S. A. W. W), domin idan suka yarda za a tuhume su cewa me yasa basu bi wannan wasiyyar ba?
ANNABI (S. A. W. W) YAYI WASIYYA
Duk da wannan tsaurin ido nasu da suka yi bai hana sun rubuta cikin littafansu irin wasiyyoyin da Annabi (S. A. W. W) yayi kan Imam Ali (A. S) ba.
Bari dai mu shiga kai tsaye cikin riwayoyi daga littafan nasu.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
(1)
{إنما وليكم الله ورسوله والذين آمنوا}.
(MA'IDA, AYA 54)
وأخرج الخطيب في المتفق عن ابن عباس قال: تصدَّق علي بخاتمه وهو راكع، فقال النبي صلى الله عليه وسلم للسائل «من أعطاك هذا الخاتم؟» قال: ذاك الراكع، فأنزل الله: {إنما وليكم الله ورسوله}.
Khadib ya fitar cikin Muttafaqun daga Ibn Abbas (R. A) yace : " Aliyu yayi sadaqa da Zobe alhali yana ruku'u sai Annabi (S. A. W. W) yace mabaracin;
" WANENE YA BAKA WANNAN ZOBE ?" Yace, " Wancan mai ruku'in nan . " Sai aka saukar;
" ABIN SANI MAJIBINCIN AL'AMARINKU SHINE ALLAH DA MANZONSA DA KUMA MUMINAN NAN DAKE TSAIDA SALLAH KUMA SUNA BAYAR DA ZAKKAH ALHALIN SUNA RUKU'U. "
وأخرج عبد الرزاق وعبد بن حميد وابن جرير وأبو الشيخ وابن مردويه عن ابن عباس في قوله: {إنما وليكم الله ورسوله} الآية.
قال: نزلت في علي بن أبي طالب.
Abdurrazaq da Abdu Bn Humaid da Ibn Jarir ('Dabari) da Abu Shaikh da Mardawaihi sun fitar daga Ibn Abbas (R. A) cikin fadinSa :
" LALLE ABIN SANI MAJIBINCIN AL'AMARINKU SHINE ALLAH DA MANZONSA.... " Aya.
Yace, " Ta sauka ne kan Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S). "
وأخرج الطبراني في الأوسط وابن مردويه عن عمار بن ياسر قال: «وقف بعلي سائل وهو راكع في صلاة تطوّع، فنزع خاتمه فأعطاه السائل، فأتى رسول الله صلى الله عليه وسلم فاعلمه ذلك، فنزلت على النبي صلى الله عليه وسلم هذه الآية {إنما وليكم الله ورسوله والذين آمنوا الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة وهم راكعون} فقرأ رسول الله صلى الله عليه وسلم على أصحابه، ثم قال: من كنت مولاه فعلي مولاه، اللهم وال من والاه وعاد من عاداه».
'Dabarani ya fitar cikin As-Saadiq da Ibn Mardawihi daga Ammar Bn Yasir (R. A) yace :
" Mabaraci ya tsaya a wajen Aliyu alhali yana cikin ruku'u cikin sallah ta tadawwi'i, sai ya cire Zobensa ya bada ita ga mai bara. Sai ya jewa Manzon Allah (S. A. W. W) ya sanar da shi (abinda ya faru na sadaqar da aka ba shi), sai aka saukar akan Annabi (S. A. W. W) wannan ayar;
" ABIN SANI MAJIBINCIN AL'AMARINKU SHINE ALLAH DA MANZONSA DA MUMINAN NAN DAKE TSAIDA SALLAH SUNA BAYAR DA ZAKKAH KUMA SUNA (cikin) RUKU'U ."
Sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya karanta akan Sahabbansa sannan yace;
" DUK WANDA NA KASANCE MAJIBINCINSA TO, ALIYU MAJIBINCINSA NE. YAA ALLAH KA JIBINCI (al'amarin) WANDA YA JIBINCE SHI, KUMA KAYI ADAWA DA WANDA YAYI ADAWA DA SHI. "
(DURRUL-MANSUR NA IMAM SUYUDI)
Wannan aya nassi ce daga Allah kan cewa Imam Ali shine majibincin kowanne mumini bayan Allah da Manzonsa (S. A. W. W). Idan kaga wani ya riqi wani a matsayin majibincinsa koma bayan Imam (A. S) bayan wafatin Annabi (S. A. W. W), to, ba mumini bane.
Wannan kalma ta wilaya ita ce Manzon Allah (S. A. W. W) ya qara jaddada ta ga al'ummarsa a ranar Ghadeer kan hanyarsa ta dawowa daga Makkah, domin a lokacin saukar ayar musulmi basu yawaita ba .
Amma sai ya zamana cewa mutane sun juya baya kan wannan wasicci, shine Imam Ali (A. S) yake kafawa mutane hujja ta hanyar hadasu da Allah cewa basu ji Annabi (S. A. W. W) yace shine Shugabansu ba ? Ga dai maganar cikin Musnad na Imam Ahmad Bn Hambal.
926- حَدَّثَنَا عَبْد اللَّهِ ، حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ حَكِيمٍ الْأَوْدِيُّ ، أَنْبَأَنَا شَرِيكٌ ، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ ، عَنْ سَعِيدِ بْنِ وَهْبٍ ، وَعَنْ زَيْدِ بْنِ يُثَيْعٍ ، قَالَا : نَشَدَ عَلِيٌّ النَّاسَ فِي الرَّحَبَةِ : مَنْ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ يَوْمَ غَدِيرِ خُمٍّ إِلَّا قَامَ ، قَالَ : فَقَامَ مِنْ قِبَلِ سَعِيدٍ سِتَّةٌ ، وَمِنْ قِبَلِ زَيْدٍ سِتَّةٌ ، فَشَهِدُوا أَنَّهُمْ سَمِعُوا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ لِعَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ يَوْمَ غَدِيرِ خُمٍّ : " أَلَيْسَ اللَّهُ أَوْلَى بِالْمُؤْمِنِينَ ؟ " ، قَالُوا : بَلَى ، قَالَ : " اللَّهُمَّ مَنْ كُنْتُ مَوْلَاهُ فَعَلِيٌّ مَوْلَاهُ ، اللَّهُمَّ وَالِ مَنْ وَالَاهُ ، وَعَادِ مَنْ عَادَاهُ " ، حَدَّثَنَا عَبْد اللَّهِ ، حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ حَكِيمٍ ، أَنْبَأَنَا شَرِيكٌ ، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ ، عَنْ عَمْرٍو ذِي مُرٍّ ، بِمِثْلِ حَدِيثِ أَبِي إِسْحَاقَ ، يَعْنِي عَنْ سَعِيدٍ وَزَيْدٍ وَزَادَ فِيهِ : " وَانْصُرْ مَنْ نَصَرَهُ ، وَاخْذُلْ مَنْ خَذَلَهُ " ، حَدَّثَنَا عَبْد اللَّهِ ، حَدَّثَنَا عَلِيٌّ ، أخبرنا شَرِيكٌ ، عَنِ الْأَعْمَشِ ، عَنْ حَبِيبِ بْنِ أَبِي ثَابِتٍ ، عَنْ أَبِي الطُّفَيْلِ ، عَنْ زَيْدِ بْنِ أَرْقَمَ ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، مِثْلَهُ .
Abdullahi ya bamu labari, Aliyu Bn Hakeem ya bamu labari, Shareek ya bamu labari daga baban Ishaq, daga Sa'eed Bn Wahbin, da kuma daga Zaid Bn Yuthai'i, suka ce : " Aliyu ya hada mutane da Allah a Haraba (cewa);
" WANENE DAGA CIKINKU YA JI MANZON ALLAH (S. A. W. W) NA FADA A RANAR GHADEER KHUM YA MIQE !"
Yace, sai mutane shida (6) ta bangaren Sa'eed suka miqe, ta bangaren Zaid ma mutane shida (6) suka miqe suka yi shaida cewa lalle su sun ji Manzon Allah) S. A. W. W) yana fada ga Aliyu (R. A) ranar Ghadeer cewa;
" YAA ALLAH DUK WANDA NA KASANCE SHUGABANSA TO, ALIYU MA SHUGABANSA NE . YAA ALLAH KA JIBINCI WANDA YA JIBINCE SHI, KUMA KAYI ADAWA DA WANDA YAYI ADAWA DASHI. "
Abdullahi ya bamu labari, Aliyu Bn Hakeem ya bamu labari, Shareek ya bamu labari daga baban Ishaq, daga Amru Zee Murri da irin misalin hadisin baban Ishaq, abin nufi daga Sa'eed da Zaid, suka qara a cikinsa;
" KUMA KA TAIMAKI WANDA YA TAIMAKE SHI, KUMA KA TABAR DA WANDA YA TABAR DASHI !"
Abdullahi ya bamu labari, Aliyu ya bamu labari, Shareek ya bamu labari daga A'amashi, daga Habeeb Bn Abiy Thaabit, daga baban 'Dufail, daga Zaid Bn Arqaam, daga Annabi (S. A. W. W) misalinsa. "
(Mudnad Ahmad, Musnad KHULAFA'AR-RAASHIDEEN, Musnad Aliyu Bn Abiy 'Dalib )
Mutane sunyi ta yin tawili don su kawar da wannan matsayi kan Imam Ali (A.S) da cewa wai kalmar MAULA na da ma'anoni da yawa kamar haka:-
Aboki,
Masoyi,
Magaji, D. S. Amma abinda ya kamata su duba shine, a wanne muhalli Annabi (S. A. W. W) yayi amfani da wannan kalma? Kuma da me kalmar tafi dacewa cikin maganar tasa ?
(2)- Idan muka koma cikin Qur'ani aya ta 7 cikin suratul -Ra'ad za muga inda Allah (T) ke cewa;
" وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦٓۗ إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرٞۖ وَلِكُلِّ قَوۡمٍ هَادٍ."( ٧)
" KUMA KAFIRAI NA CEWA, " DON MENENE BA A SAUKAR MASA DA AYA A KANSA BA DAGA UBANGIJINSA ?" KACE, " ABIN SANI SANI DAI KAI MAI GARGADI NE, KUMA CIKIN KOWACCE JAMA'A AKWAI MAI SHIRYAR DA ITA. "
15313 - حدثنا أحمد بن يحيى الصوفي، قال: ثنا الحسن بن الحسين الأنصاري، قال: ثنا معاذ بن مسلم، ثنا الهروي، عن عطاء بن السائب، عن سعيد بن جبير، عن ابن عباس، قال: لما نزلت {إنما أنت منذر ولكل قوا هاد} وضع صلى الله عليه وسلم يده على صدره، فقال: "أنا المنذر ولكل قوم هاد " ، وأومأ بيده إلى منكب علي، فقال: "أنت الهادي يا علي، بك يهتدي المهتدون بعدي " .
Ahmad Bn Yahya As-Sufiy ya bamu labari yace : Hassan Bn Hussain Al-Ansariy ya bamu labari yace : Mu'azu Bn Muslim ya bamu labari, Hurriyyu ya bamu labari daga Adda'u Bn Thaa'eb ,daga Sa'eed Bn Jubair, daga Ibn Abbas (R. A) yace : " Yayin da aka saukar;
" ABIN SANI KAI MAI GARGADI NE, KUMA KOWACCE JAMA'A AKWAI MAI SHIRYAR DA ITA. "
Manzon Allah (S. A. W. W) ya dora hannunsa kan qirjinsa yace; " NINE MAI GARGADI, KUMA GA KOWACCE JAMA'A AKWAI MAI SHIRYAR DA ITA ."
Sannan kuma ya miqa hannunsa zuwa ga kafadar Aliyu yace;
" KAI NE MAI SHIRYARWA YA ALIYU ! DA KAI NE DUKKAN WANI MAI SHIRYUWA ZAI SHIRYU A BAYANA. "
(TAFSIR 'DABARI, QARQASHIN AYA TA 7 CIKIN SURATUL RA'AD)
Kuma bayani yazo cikin
-Mustadrak Haakeem Annaisaburiy, J:3, SH:129
- Khadibul-Baghdaad, J:12, SH:372
- Mu'ujamus-Sageer na 'Dabarani, Harafin B, J:1, SH:162 (Bugu na biyu)
D. S
(3)- Yazo cikin Sahihul-Bukhari kamar haka :
(4416) - حدثنا مسدد: حدثنا يحيى، عن شعبة، عن الحكم، عن مصعب ابن سعد، عن أبيه: أن رسول الله صلى الله عليه وسلم خرج إلى تبوك، واستخلف عليا، فقال: أتخلفني في الصبيان والنساء؟ قال: (ألا ترضى أن تكون مني بمنزلة هارون من موسى؟ إلا أنه ليس نبي بعدي) وقال أبو داود: حدثنا شعبة، عن الحكم: سمعت مصعبا
Musaddadu ya bamu labari, Yahya ya bamu labari daga Shu'ubata, daga Hakaam, daga Mus'ab Ibn Sa'ad, daga babansa : Annabi (S. A. W. W) ya fita zuwa Tabuka sai ya halifantar da Aliyu (ya zauna a garin Madinah don bata kariya), sai Aliyu yace;
" Yanzu za a barni cikin yara da mata (alhali za a fadi fagen fama don bayar da rai)? " Sai (Annabi) yace;
" ASHE BAI YI MAKA DADI BA MATSAYIN A WAJENA YA KASANCE KAMAR MATSAYIN HARUNA WAJEN MUSA SAI DAI KAWAI DON BABU ANNABI A BAYANSA ?"
Abu Dawud yace, Shu'ubata ya bamu labari daga Hakaam : Na ji Mus'ab
(BUKHARI, KITABUL-MAGAAZEEY, BABUN GAZWATUT-TABUKA, HADISI MAI LAMBA 4416))
Sanin haqiqanin wannan hadisi sai ka san yadda ta kasance ga Annabi Haruna (A. S) yayin da Annabi Musa (A. S) ya Halifantar dashi cikin jama'arsa yayin da ya tafi miqati ga Ubangijinsa. Yayin da Annabi Musa (A. S) zai tafi miqati sai ya bar jagoranci a hannun Annabi Haruna (A. S), amma mutane suka qi bin Annabi Haruna (A. S) suka zabi 'Dan Maraqi .
To, kamar hakane yayin da Annabi (S. A. W. W) ya koma ga Ubangijinsa yabar Imam Ali (A. S) sai aka yi masa kamar yadda aka yiwa Annabi Haruna (A. S).
(4)- Cikin Sunan na Tirmidhi
«4085» حدثنا إسماعيل بن موسى حدثنا شريك عن أبي إسحاق عن حبشي بن جنادة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((علي مني وأنا من علي ولا يؤدي عني إلا أنا أو علي)).
قال أبو عيسى: هذا حديث حسن غريب صحيح.
Ismael Bn Musa ya bamu labari, Shuraik ya bamu labari daga baban Ishaq, daga Habshiy Bn Junadata yace: Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" ALIYU DAGA GARE NI YAKE KUMA NI DAGA ALIYU NAKE, KUMA BABU MAI TSAYAWA A MADADINA SAI DAI NI (da kaina) KO ALIYU. "
Abu Isah Al-Tirmidhi yace, wannan hadisi mai kyau ne baqo, kuma ingantacce.
(SUNAN TIRMIDHI, KITABUL-FADHA'IL, BABUN MANAQIBU ALIYU, HADISI MAI LAMBA 4085)
Yanzu duk wanda bayani na Ma'aiki (S. A. W. W) ace ba wasiyya bace ?
(5)- Annabi (S. A. W. W) ya san ba za subi wannan wasiyyar tasa ba
837- حَدَّثَنَا أَسْوَدُ بْنُ عَامِرٍ ، حَدَّثَنِي عَبْدُ الْحَمِيدِ بْنُ أَبِي جَعْفَرٍ يَعْنِي الْفَرَّاءَ ، عَنْ إِسْرَائِيلَ ، عَنْ أَبِي إِسْحَاقَ ، عَنْ زَيْدِ بْنِ يُثَيْعٍ ، عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، قَالَ : قِيلَ : يَا رَسُولَ اللَّهِ ، مَنْ نُؤَمَّرُ بَعْدَكَ ؟ قَالَ : " إِنْ تُؤَمِّرُوا أَبَا بَكْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، تَجِدُوهُ أَمِينًا ، زَاهِدًا فِي الدُّنْيَا ، رَاغِبًا فِي الْآخِرَةِ ، وَإِنْ تُؤَمِّرُوا عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ تَجِدُوهُ قَوِيًّا أَمِينًا ، لَا يَخَافُ فِي اللَّهِ لَوْمَةَ لَائِمٍ ، وَإِنْ تُؤَمِّرُوا عَلِيًّا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، وَلَا أُرَاكُمْ فَاعِلِينَ ، تَجِدُوهُ هَادِيًا مَهْدِيًّا ، يَأْخُذُ بِكُمْ الطَّرِيقَ الْمُسْتَقِيمَ " .
Aswad Bn Ameer ya bamu labari, Abdulhameed Bn Abiy Ja'afar ya bamu labari, abin nufi shine Farra'a, daga Isra'il, daga baban Ishaq, daga Zaid Bn Yuthai'i, daga Aliyu (R. A) yace : Aka ce, yaa Ma'aikin Allah (S. A. W. W), wanene zai yi shugabanci a bayanka ? Yace;
" IDAN KUKA SHUGABANTAR DA ABUBAKAR ZA KU SAME SHI AMINTACCE MAI GUDUN DUNIYA, MAI KWADAYIN LAHIRA. IDAN KUMA KUKA SHUGABANTAR DA UMAR ZA KU SAME SHI TSAYAYYE AMINTACCE, BA ZAI JI TSORON ZARGIN MAI ZARGI CIKIN AL'AMARIN ALLAH BA. KUMA IDAN KUKA SHUGABANTAR DA ALIYU (R. A), KO DA SHIKE NA SAN BA ZA KUYI HAKA BA, TO, DA KUWA ZA KU SAME SHI SHIRYAYYE MAI SHIRYARWA. ZAI RIQI MIQAQQIYAR HANYA TARE DA KU ."
Yanzu dan Allah bisa wannan magana ta Manzon Allah (S. A. W. W) in dai dama shiriya ake nema ba bata ba wa za a riqa a matsayin jagora ? Ko da shike ya fada musu cewa ya san ba za su aikata ba, kuma hakan ne ta faru.
To, saboda sani da tunanin cewa ba za su bashi ba shine yake fadawa dan'uwan nasa,
645- حَدَّثَنَا خَلَفٌ ، حَدَّثَنَا قَيْسٌ ، عَنِ الْأَشْعَثِ بْنِ سَوَّارٍ ، عَنْ عَدِيِّ بْنِ ثَابِتٍ ، عَنْ أَبِي ظَبْيَانَ ، عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " يَا عَلِيُّ ، إِنْ أَنْتَ وُلِّيتَ الْأَمْرَ بَعْدِي ، فَأَخْرِجْ أَهْلَ نَجْرَانَ مِنْ جَزِيرَةِ الْعَرَبِ " .
Khalaf ya bamu labari, Qais ya bamu labari daga Ash'ath Bn Da'awar, daga Adiyyi Bn Thaabit, daga baban Zabyan, daga Aliyu (R. A) yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" YAA ALIYU ! IN DAI KAINE KA JIBINCI AL'AMARI A BAYANA TO, KA FITAR DA MUTANEN NAJRAN DAGA YANKIN LARABAWA ."
Musnad Ahmad
Daga wannan hadisi ma za ku qaryata cewa Annabi (S. A. W. W) bai ce Abubakar ne Khalifansa a bayansa ba, domin da ace ya yi wannan magana da ba zai fadawa Imam Ali wannan magana ba. Amma saboda Ali ne wasiyyinsa kuma yana kokonton cewa ba za su bashi ba saboda sanin halinsu da yayi shine yake fadawa Imam Ali haka.
GARGADIN DA YA YIWA QANINSA IMAM ALI (A. S)
Da shike ya san fitinar da za ta faru a bayansa tunda yaga sunqi su tafi yaqi qarqashin Usamatu Bn Zaid da kuma qin bashi abin rubutu shine yake ce masa ,
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
677- حَدَّثَنَا عَبْد اللَّهِ ، حَدَّثَنِي مُحَمَّدُ بْنُ أَبِي بَكْرٍ الْمُقَدَّمِيُّ ، حَدَّثَنَا فُضَيْلُ بْنُ سُلَيْمَانَ يَعْنِي النُّمَيْرِيَّ ، حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ أَبِي يَحْيَى ، عَنْ إِيَاسِ بْنِ عَمْرٍو الْأَسْلَمِيِّ ، عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " إِنَّهُ سَيَكُونُ بَعْدِي اخْتِلَافٌ ، أَوْ أَمْرٌ ، فَإِنْ اسْتَطَعْتَ أَنْ تَكُونَ السِّلْمَ ، فَافْعَلْ " .
Abdullahi ya bamu labari, Muhammad Bn Abiy Bakri Al-Muqdamiy ya bamu labari, Fudhil Bn Sulaiman ya bamu labari, wato Numair, Muhammad Bn Abiy Yahya ya bamu labari, daga Iyaas Bn Amruu Al-Aslamiy, daga Aliyu Bn Abiy 'Dalib (R. A) yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace;
" LALLE DA SANNU WANI SABANI ZAI AUKU A BAYANA, KO KUMA WANI AL'AMARI. TO, IDAN HAR ZAI YIWU KA SAMAR DA ZAMAN LAFIYA, TO, KA AIKATA. "
(Musnad Ahmad, Hadisi mai lamba 677)
Saboda haka da aka sami wannan sabani na juyawa Annabi Muhammad (S. A. W. W) baya kan umarninsa, kuma Imam Ali (A. S) ya tuna musu abinda suka sani suka kawar da kai da gangan saboda bin son zuciya sai ya dau wannan mataki wanda yayansa (S. A. W. W) ya fada masa.
Saboda haka ne yasa bai yaqe su ba don kaucewa wannan fitina , amma dai ya riqa nuna musu shiriya cikin hukunce-hukuncen da suka riqa zartarwa ba daidai ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
25th May, 2021/ 14th Shawwal, 1442.