Rumbun tattara wutar Lantarki na Najeriya ya lalace, don haka za a fuskanci matsalar wutar lantarki mafi muni



Rumbun samar da wutar lantarki a Najeriya ya sake lalacewa, abin da zai sake ta’azzara ƙarancin wutar a jihohin ƙasar.


Lalacewar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Laraba, kamar yadda kamfanin rarraba lantarki na Transmission Company of Nigeria (TCN) ya tabbatar cikin wata sanarwa.


“Transmission Company of Nigeria na bayyana cewa da misalin ƙarfe 11:01 na saffiyar Laraba, 12 ga watan Mayu, an samu lalacewar layin lantarki gaba ɗaya sakamakon lalacewar wani rumbu daga cikin layukan,” a cewar TCN.


Su ma kamfanonin dillancin wutar na KEDCO da Kaduna Electric sun tabbatar da faruwar matsalar, inda suka bai wa kwastomominsu haƙuri.


“Muna mai baƙin shaida muku cewa an samu ɗaukewar lantarki yanzu haka a kamfaninmu na rarraba wutar – a jihohin Kaduna da Sokoto da Kebbi da Zamfara – sakamakon lalacewar rumbun lantarki na ƙasa,” in ji Kaduna Electric cikin wata sanarwa a shafinsa na Twitter.


TCN ya ce nan take ya shiga aikin shawo kan matsalar, sai dai bai bayyana tsawon lokacin da gyaran zai ɗauka ba.


Daga Ahmad Aminu Kado

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post