@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KUN KARBI MULKI DAGA ANSAR BISA KUSANCI, MU KUMA KUKA KARBE SHI DAGA HANNUNMU BISA QWACE
Bayan Imam Ali (A. S) da makusantarsa sun gama jana'izar Manzon Allah (S A. W. W) yayin da Manyan Sahabbai suka yi watsi dashi suka shagala da al'amarin duniya an buqaci Imam Ali (A. S) ya yiwa Abubakar mubaya'a.
Ga yadda ta kaya tsakaninsu
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
هُنَاكَ مِنْ بَنِي هَاشِمٍ وَ مَضَوْا بِجَمَاعَتِهِمْ إِلَى أَبِي بَكْرٍ فَلَمَّا حَضَرُوا قَالُوا بَايِعُوا أَبَا بَكْرٍ فَقَدْ بَايَعَهُ النَّاسُ وَ ايْمُ اللَّهِ لَئِنْ أَبَيْتُمْ ذَلِكَ لَنُحَاكِمَنَّكُمْ بِالسَّيْفِ فَلَمَّا رَأَى ذَلِكَ بَنُو هَاشِمٍ أَقْبَلَ رَجُلٌ رَجُلٌ فَجَعَلَ يُبَايِعُ حَتَّى لَمْ يَبْقَ مِمَّنْ حَضَرَ إِلَّا عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ ع فَقَالَ لَهُ بَايِعْ أَبَا بَكْرٍ فَقَالَ عَلِيٌّ أَنَا أَحَقُّ بِهَذَا الْأَمْرِ مِنْهُ وَ أَنْتُمْ أَوْلَى بِالْبَيْعَةِ لِي أَخَذْتُمْ هَذَا الْأَمْرَ مِنَ الْأَنْصَارِ وَ احْتَجَجْتُمْ عَلَيْهِمْ بِالْقَرَابَةِ مِنْ رَسُولِ اللَّهِ وَ تَأْخُذُونَهُ مِنَّا أَهْلَ الْبَيْتِ غَصْباً أَ لَسْتُمْ زَعَمْتُمْ لِلْأَنْصَارِ أَنَّكُمْ أَوْلَى بِهَذَا الْأَمْرِ مِنْهُمْ لِمَكَانِكُمْ مِنْ رَسُولِ اللَّهِ ص فَأَعْطَوْكُمُ الْمَقَادَةَ وَ سَلَّمُوا لَكُمُ الْإِمَارَةَ وَ أَنَا أَحْتَجُّ عَلَيْكُمْ بِمِثْلِ مَا احْتَجَجْتُمْ عَلَى الْأَنْصَارِ أَنَا أَوْلَى بِرَسُولِ اللَّهِ حَيّاً وَ مَيِّتاً وَ أَنَا وَصِيُّهُ وَ وَزِيرُهُ وَ مُسْتَوْدَعُ سِرِّهِ وَ عِلْمِهِ وَ أَنَا الصِّدِّيقُ الْأَكْبَرُ أَوَّلُ مَنْ آمَنَ بِهِ وَ صَدَّقَهُ وَ أَحْسَنُكُمْ بَلَاءً فِي جِهَادِ الْمُشْرِكِينَ وَ أَعْرَفُكُمْ بِالْكِتَابِ وَ السُّنَّةِ وَ أَفْقَهُكُمْ فِي الدِّينِ وَ أَعْلَمُكُمْ بِعَوَاقِبِ الْأُمُورِ وَ أَذْرَبُكُمْ لِسَاناً وَ أَثْبَتُكُمْ جِنَاناً فَعَلَامَ تُنَازِعُونَّا هَذَا الْأَمْرَ أَنْصِفُونَا إِنْ كُنْتُمْ تَخَافُونَ اللَّهَ مِنْ أَنْفُسِكُمْ وَ اعْرِفُوا لَنَا مِنَ الْأَمْرِ مِثْلَ مَا عَرَفَتْهُ الْأَنْصَارُ لَكُمْ وَ إِلَّا فَبُوءُوا بِالظُّلْمِ وَ أَنْتُمْ تَعْلَمُونَ فَقَالَ عُمَرُ أَ مَا لَكَ بِأَهْلِ بَيْتِكِ أُسْوَةٌ فَقَالَ عَلِيٌّ ع سَلُوهُمْ عَنْ ذَلِكَ فَابْتَدَرَ الْقَوْمُ الَّذِينَ بَايَعُوا مِنْ بَنِي هَاشِمٍ فَقَالُوا مَا بَيْعَتُنَا بِحُجَّةٍ عَلَى عَلِيٍّ ع وَ مَعَاذَ اللَّهِ أَنْ نَقُولَ إِنَّا نُوَازِيهِ فِي الْهِجْرَةِ وَ حُسْنِ الْجِهَادِ وَ الْمَحَلِّ مِنْ رَسُولِ اللَّهِ ص فَقَالَ عُمَرُ إِنَّكَ لَسْتَ مَتْرُوكاً حَتَّى تُبَايِعَ طَوْعاً أَوْ كَرْهاً فَقَالَ عَلِيٌّ ع احْلُبْ حَلْباً لَvكَ شَطْرُهُ اشْدُدْ لَهُ الْيَوْمَ لِيَرُدَّ عَلَيْكَ غَداً إِذاً وَ اللَّهِ لَا أَقْبَلَ قَوْلَكَ وَ لَا أَحْفِلَ بِمَقَامِكَ وَ لَا أُبَايِعَ فَقَالَ أَبُو بَكْرٍ مَهْلًا يَا أَبَا الْحَسَنِ مَا نُشَدِّدُ عَلَيْكَ وَ لَا نُكْرِهُكَ فَقَامَ أَبُو عُبَيْدَةَ إِلَى عَلِيٍّ فَقَالَ يَا ابْنَ عَمِّ لَسْنَا نَدْفَعُ قَرَابَتَكَ وَ لَا سَابِقَتَكَ وَ لَا عِلْمَكَ وَ لَا نُصْرَتَكَ وَ لَكِنَّكَ حَدَثُ السِّنِّ وَ كَانَ لِعَلِيٍّ ع يَوْمَئِذٍ ثَلَاثٌ وَ ثَلَاثُونَ سَنَةً وَ أَبُو بَكْرٍ شَيْخٌ مِنْ مَشَايِخِ قَوْمِكَ وَ هُوَ أَحْمَلُ لِثِقَلِ هَذَا الْأَمْرِ وَ قَدْ مَضَى الْأَمْرُ بِمَا فِيهِ فَسَلِّمْ لَهُ فَإِنْ عَمَّرَكَ اللَّهُ لَسَلَّمُوا هَذَا الْأَمْرَ إِلَيْكَ وَ لَا يَخْتَلِفُ عَلَيْكَ اثْنَانِ بَعْدَ هَذَا إِلَّا وَ أَنْتَ بِهِ خَلِيقٌ وَ لَهُ حَقِيقٌ وَ لَا تَبْعَثِ الْفِتْنَةَ قَبْلَ أَوَانِ الْفِتْنَةِ قَدْ عَرَفْتَ مَا فِي قُلُوبِ الْعَرَبِ وَ غَيْرِهِمْ عَلَيْكَ فَقَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع يَا مَعَاشِرَ الْمُهَاجِرِينَ وَ الْأَنْصَارِ اللَّهَ اللَّهَ لَا تَنْسَوْا عَهْدَ نَبِيِّكُمْ إِلَيْكُمْ فِي أَمْرِي وَ لَا تُخْرِجُوا سُلْطَانَ مُحَمَّدٍ مِنْ دَارِهِ وَ قَعْرِ بَيْتِهِ إِلَى دُورِكُمْ وَ قَعْرِ بُيُوتِكُمْ وَ تَدْفَعُوا أَهْلَهُ عَنْ حَقِّهِ وَ مَقَامِهِ فِي النَّاسِ يَا مَعَاشِرَ الْجَمْعِ إِنَّ اللَّهَ قَضَى وَ حَكَمَ وَ نَبِيَّهُ أَعْلَمُ وَ أَنْتُمْ تَعْلَمُونَ إِنَّا أَهْلَ الْبَيْتِ أَحَقُّ بِهَذَا الْأَمْرِ مِنْكُمْ أَ مَا كَانَ مِنَّا الْقَارِئُ لِكِتَابِ اللَّهِ الْفَقِيهُ فِي دِينِ اللَّهِ الْمُضْطَلِعُ بِأَمْرِ الرَّعِيَّةِ وَ اللَّهِ إِنَّهُ لَفِينَا لَا فِيكُمْ فَلَا تَتَّبِعُوا الْهَوَى فَتَزْدَادُوا مِنَ الْحَقِّ بُعْداً وَ تُفْسِدُوا قَدِيمَكُمْ بِشَرٍّ مِنْ حَدِيثِكُمْ فَقَالَ بَشِيرُ بْنُ سَعْدٍ الْأَنْصَارِيُّ الَّذِي وَطَّأَ الْأَمْرَ لِأَبِي بَكْرٍ وَ قَالَتْ جَمَاعَةُ الْأَنْصَارِ يَا أَبَا الْحَسَنِ لَوْ كَانَ هَذَا الْكَلَامَ سَمِعَتْهُ الْأَنْصَارُ مِنْكَ قَبْلَ الِانْضِمَامِ لِأَبِي بَكْرٍ مَا اخْتَلَفَ فِيكَ اثْنَانِ فَقَالَ عَلِيٌّ ع يَا هَؤُلَاءِ أَ كُنْتُ
أَدَعُ رَسُولَ اللَّهِ ص مُسَجًّى لَا أُوَارِيهِ وَ أَخْرُجُ أُنَازِعُ فِي سُلْطَانِهِ وَ اللَّهِ مَا خِفْتُ أَحَداً يَسْمُو لَهُ وَ يُنَازِعُنَا أَهْلَ الْبَيْتِ فِيهِ وَ يَسْتَحِلُّ مَا اسْتَحْلَلْتُمُوهُ وَ لَا عَلِمْتُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ ص تَرَكَ يَوْمَ غَدِيرِ خُمٍّ لِأَحَدٍ حُجَّةً وَ لَا لِقَائِلٍ مَقَالًا فَأَنْشُدُ اللَّهَ رَجُلًا سَمِعَ النَّبِيَّ ص يَوْمَ غَدِيرِ خُمٍّ يَقُولُ مَنْ كُنْتُ مَوْلَاهُ فَهَذَا عَلِيٌّ مَوْلَاهُ اللَّهُمَّ وَالِ مَنْ وَالاهُ وَ عَادِ مَنْ عَادَاهُ وَ انْصُرْ مَنْ نَصَرَهُ وَ اخْذُلْ مَنْ خَذَلَهُ أَنْ يَشْهَدَ بِمَا سَمِعَ قَالَ زَيْدُ بْنُ أَرْقَمَ فَشَهِدَ اثْنَا عَشَرَ رَجُلًا بَدْرِيّاً بِذَلِكَ وَ كُنْتُ مِمَّنْ سَمِعَ الْقَوْلَ مِنْ رَسُولِ اللَّهِ ص فَكَتَمْتُ الشَّهَادَةَ يَوْمَئِذٍ فَذَهَبَ بَصَرِي قَالَ وَ كَثُرَ الْكَلَامُ فِي هَذَا الْمَعْنَى وَ ارْتَفَعَ الصَّوْتُ وَ خَشِيَ عُمَرُ أَنْ
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج28، ص: 186
Banu Hashim da jama'arsu sun shude zuwa ga Abubakar, a yayin da suka isa sai aka ce musu,
" KU YIWA ABUBAKAR MUBAYA'A DOMIN MUTANE SUN RIGA SUNYI MASA MUBAYA'AH. KUMA IDAN HAR KUKA QI ZA MU HUKUNTA KU DA TAKOBI. "
To, yayin da Banu Hashim suka ga haka sai wannan mutum ya kalli wannan mutum daga cikinsu, suka yi mubaya'ah har ya zama Aliyu Bn Abiy 'Dalib ne kadai ya rage daga cikin wadanda ke gurin , sai aka ce masa;
" KA YIWA ABUBAKAR MUBAYA'A !"
Sai Aliyu yace;
" NI NAFI CANCANTA DA WANNAN AL'AMARI FIYE DA SHI, KUMA KU KUKA FI CANCANTA DA YIMIN MUBAYA'AH, KUN KARBI WANNAN AL'AMARI NE DAGA HANNUN ANSAR KUKA KAFA MUSU HUJJA DA KUSANCINKU DA MANZON ALLAH, SANNAN KUMA KUKA KARBE SHI DAGA HANNUNMU AHLUL-BAIT BISA QWACE ! ASHE BA KU RIYA GA ANSAR CEWA KU KUKA FI CANCANTA DA WANNAN AL'AMARI FIYE DASU BA SABODA KUSANCINKU DA MANZON ALLAH , SAI SUKA BA KU MULKI SUKA SALLAMA MUKU JAGORANCI. TO, NIMA INA KAFA MUKU DA IRIN HUJJAR DA KUKA KAFAWA ANSAR. NINE MAFI CANCANTA DA MANZON ALLAH A RAYE DA MACE, KUMA NINE WASIYYINSA KUMA WAZIRINSA KUMA MA'ADANAR SIRRINSA DA ILIMINSA, KUMA NINE SIDDIQU MAFI GIRMA ! FARKON WANDA YA FARA YIN IMANI DASHI YA GASKATA SHI KUMA MAFIFICINKU WAJEN JARRABAWOWI CIKIN YAQAR MUSHIRIKAI KUMA MAFIFICINKU WAJEN SANIN LITTAFIN ALLAH DA SUNNAH, KUMA WANDA YA FI KU FAHINTAR ADDINI KUMA MAFIFICINKU WAJEN SANIN AL'AMRA KUMA MAFIFICINKU WAJEN KAIFIN HARSHE KUMA MAFIFICINKU WAJEN TABBATUWA, TO, TA YAYA ZA KU FITAR DAMU DAGA WANNAN AL'AMARI ? KUYI MANA ADALCI IN DAI KUN KASANCE MASU TSORON ALLAH DAGA KAWUKANKU. KU SALLAMA MANA WANNAN AL'AMARI KAMAR YADDA ANSAR SUKA SALLAMA MUKU, IDAN KUWA BA HAKA BA KU JUYA DA ZALUNCI ALHALI KUNA SANE !
Sai Umar yace; " ME YASA KAI BA ZA KAYI KOYI DA IYALAN GIDANKA BA ?"
Sai Aliyu yace masa; " KA TAMBAYE SU GAME DA HAKA. "
Sai wadanda suka yi mubaya'a daga cikin Banu Hashim suka bijiro suna cewa;
" BA WAI MUNYI BAI'A BISA HUJJA BACE AKAN ALIYU (A.S) , MUNA NEMAN TSARIN ALLAH DA MU CE MU MUNA JAYAYYA DASHI KAN HIJRA DA KUMA KYAN JIHADI BA, KO KUMA DA MATSAYI WAJEN MANZON ALLAH (S. A. W. W) BA. "
Sai Umar yace; " TO, MU DAI BA ZA MU BARKA BA DOLE SAI KAYI MUBAYA'A BISA SON RAI KO DOLE !
Sai Aliyu (A. S) yace; " KA TACE MADARA DOMIN KANKA, KA QARFAFE SHI A YAU (wajen shugabancinsa) DOMIN YA MAYAR MAKA SHI A GOBE. WALLAHI BA ZAN KARBI MAGANARKA BA KUMA BA ZANYI LA'AKARI DA MUQAMINKA (na girman shekaru don bin qarya ba), KUMA BA ZANYI MUBAYA'A BA. "
Sai Abubakar yace ; " ALLAH SARKI YAA BABAN HASSAN, BA ZA MU TSANANTA MAKA (cewa dole sai ka yi min mubaya'a ba), BA ZA MU TILASKA BA. "
Sai Abu Ubaidata Bn Jarraaha ya miqe zuwa ga Aliyu yace;
" YAA 'DAN AMMI NA ! BA WAI MUNA TUNKUDE WANNAN KUSANTAKAR TAKA BACE, KO KUMA RIGAYENKA CIKIN MUSLIMCI BA, KO KUMA ILIMINKA KO KUMA TAIMAKONKA (a muslimci ba), SAI DAI KAI YARO NE. "
A wannan lokaci Aliyu yana da shekaru 33 ne, Abubakar kuma tsoho ne daga tsofin manyan mutanenka, shi zai fi iya daukar nauyin wannan al'amari, kuma al'amari ya riqa ya shiga hannunsa, saboda haka ka sallama masa wannan al'amari, da sannu Allah zai miqa shi (wata rana) gare ka, kuma ko da mutane biyu ne ba za suyi sabani a kanka ba bayan haka. Ai dominka akayi ta, kuma yana da haqqi (wajen binka), kada ka nemi tayar da wata fitina gabanin wata fitina. Haqiqa fa ka san abinda ke cikin zukatan larabawa (na fushi da kai don kai ka karkashe iyayensu da kakanninsu ) da kuma qiyayyarsu a kanka. "
Sai Amirul-muminina (A. S) yace;
" YAA KU TARON MUHAJIRAI DA ANSAR ! INA HADA KU DA ALLAH, INA HADA KU DA ALLAH KADA KU MANTA ALQAWARIN ANNABINKU GARE KU CIKIN AL'AMARINA, KUMA KADA KU FITAR DA IKON MUHAMMADU DAGA GIDANSA DA KUMA TSAKAR GIDANSA ZUWA GIDAJENKU DA TSAKAR GIDANKU. KUMA KU TUNKUDE IYALINSA DAGA HAQQINSA DA MUQAMINSA CIKIN MUTANE.
YAA KU WADANNAN TARO ! LALLE ALLAH YA YA QADDARA KUMA YA HUKUNTA , KUMA ANNABINSA YANA SANI , KUMA KU MA KUNA SANI CEWA MU AHLUL-BAIT MUNE MAFI CANCANTA DA WANNAN AL'AMARI FIYE DA KU MATUQAR DAI CIKINMU AKWAI MAI KARANTA LITTAFIN ALLAH, MASANI CIKIN ADDININ ALLAH, MASANI GAME DA AL'AMARIN JAGORANCI. KUMA WALLAHI AKWAI WADANNAN A CIKINMU BA A CIKINKU BA, KADA KUBI SON ZUCIYA SON ZUCIYA SAI KUYI NISA DA GASKIYA, SAI KU BATA DADEWARKU (cikin muslimci) DA SHARRI DAGA ZANTUKANKU. "
Sai Bashir Bn Sa'ad Ansariy wanda ya sallama al'amari ga Abubakar yace, da kuma sauran jama'a daga Ansar suka ce:
" YAA BABAN HASSAN ! DA DAI ACE MUTANEN ANSAR SUNJI WANNAN MAGANA DAGA GARE KA KAFIN SU YIWA ABUBAKAR MUBAYA'A, TO, DA KUWA BA A SAMI MUTUM BIYU DA ZA SUYI SABANI A KANKA BA. "
Sai Aliyu (R. A) yace;
" YAA KU WADANNAN! YANZU KUNA GANI ZAN IYA BARIN MANZON ALLAH KWANCE (kamar yadda kuka barshi) BA TARE DA NAYI JANA'IZARSA BA ? NA FITO INA YIN JAYAYYA CIKIN IKONSA ? WALLAHI BANA TSORON WANI DA YAJI DAGA GARE SHI SANNAN KUMA YANA JAYAYYA DAMU AHLUL-BAIT CIKINSA, KUMA YANA HALATTA ABINDA YA HALATTA BA, KUMA BAN SAN CEWA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA BAR WANI ABU NA HUJJA RANAR GHADEER KHUM BA, KO KUMA WATA MAGANA DAGA MAI MAGANA BA.
YANZU DAN ALLAH BABU WANI MUTUN 'DAYA (1) DAGA CIKINKU WANDA YA JI MANZON ALLAH (S. A. W. W) A RANAR GHADEER YANA CEWA; " DUK WANDA NA KASANCE SHUGABANSA TO, ALIYU SHUGABANSA NE ? YAA ALLAH KA JIBINCI WANDA YA JIBINCE SHI, KUMA KAYI ADAWA DA WANDA YAYI ADAWA DASHI, KA TAIMAKI WANDA YA TAIMAKE SHI, KUMA KA TABAR DA DUK WANDA YA TABAR DA SHI. " YA ZO YAYI SHAIDA KAN ABINDA YA JI.
Sai Zaid Bn Arqaam yace, sai aka sami mutane goma sha biyu (12) suka bayar da shaida daga cikin wadanda suka yi yaqin Badr. Ni ma ina daga cikin wadanda suka ji wannan magana daga Manzon Allah (S. A. W. W) sai na boye shaidar a wannan rana, sai Idanuwa suka makance. "
Yace, " Sai maganganu suka yi yawa cikin wannan ma'ana, kuma aka daga murya, kuma Umar ya ji tsoro kada su juya zuwa ga maganar Aliyu (A. S), sai ya tarwatsa masallacin ! Kuma yace;
" LALLE ALLAH (T) NA JUYA ZUKATA DA GANI (su karkata zuwa ga halaka) , KUMA BA ZAI GUSHE BA YAA BABAN HASSAN YANA KWADAYIN MAGANAR MUTANE. " To, sai suka juya a haka (ba tare da sun bi gaskiya ba).
KU BIYO MU CIKIN RUBUTUNMU NA GABA INSHA ALLAH.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
25th May, 2021/ 14th Shawwal, 1442.