Quds 2014: Abinda Ya Faru Da Ya'yan Sayyid Zakzaky (H), A Barikin Basawa

 


DAGA IMAM SAMARU


A lokacin da muka isa barikin basawa an sauke mu kofan asibitin barikin bayan ansakkomu sai naga ansakko da abokina mujahid daga wata motan dake bayan tamu, aka zubarda mu akasa mu bakwai (7) yaya Ahmad, yaya Hamid, Aliy Haidar, Ayuba, Mujahid, ni imam, sai wani da bansanshi ba amma shi tun kafin a dakkomu yayi shahada. Bayan Sun zubemu sai wani soja yace akwashe wayoyin mu, sai suka kwashe. Sai ga wani yazo babba yasa faran shadda sai ya tambayi sojojin "daga ina suka dakko mu " sai suka ce daga pz "sai yace ina driver din ambulance " yazo sai yace sudauke mu su kaimu asibitin shika.


ANSAKA MU A AMBULANCE ZUWA ASIBITIN SHIKA 


Anfara saka Aliy haidar akan kujera, yaya Ahmad da sauran suna kwance Nikuma ina daga bakin kofa sai wani soja ya kalleni yace "dubi wannan ma student ne daga makaranta yake saboda nasa bakin wando da riga light blue, sai wani soja yace aini student din makarantan barikin ne saboda ya sanni yana ganina a ciki, sai suka shiga dukana wai ni nake daukan report din sojoji ina kawowa, suka ce min "shegiya 'yar iska "dayake basujin hausa sosai sai babban sojannan yace a tafi damu sai suka kulle motan sai ta fara tafiya Munkai gab da bakin gate sai naji motan ta tsaya. Kafin abude motan sai naga Aliy haidar yasa hannu ya ciro wani kashi a wurinda aka harbeshi akwaurin sa, saboda kashin yana sukanshi sai nace masa yamaida za'a gyara idan munje asibity, sai bai maida kashinba ya ajeshi akan kujera sai akabude mu Wani babban soja ne yazo shi kuma yasa shadda light blue sai yace ina yaran Zakzakin suke? Sai suka nuna masa su Yaya Ahmad,Hamid,Aliy haidar. Shi kuma yana rubuta sunayen mu kuma yana video covering dinmu, sai suka saukemu daga Ambulance din. Sai wani ya nuna yaya Ahmad yace "this one is dead "sai yaya Hamid yace "no he is unconscious "sai wannan babban sojan ya kara tanbayan ina yaran zakzaky suke sai suka kara nuna mishi.. Sai ya nuna mu yace mukuma suwaye sai Aliy haidar yace masa mu Abokan sune alokacin shi wannan sojan yanata rubutu akanmu.sai suka kwaso jakunkunan mu suka aje su atare damu suta mana photo dasu kaman wasu barayi sai akace musu kada sudauki hoto da wani soja, ko kafansa sai wannan babban sojan ya tafi sai ya ranshi sukaci gabada bugunmu da zaginmu,da bakaken maganganu gashi muna cikin mawuyacin hali na kishirwa, yunwa, jini yanata zuba.. Sai wani cikinsu yace "Abasu mu su kashe mu"sai wani yace a'a adauke mu akaimu dajin birnin gwari akashe mu "sai wani tsinanne ya fara zagin Abba (H) yana cewa "Uban naku ba nan abacha ya kamashi ya kulle a keji kamar kaza ba? Wai kuma ko shi akasa ya kamo Abba (H) zai iya "sai Aliy haidar yace mishi "karya kakeyi kare kawai sai abin yayima sojan zafi sai yaje da sauri zai bugi Aliy haidar dayake muna kwance akasane sai yaya Hamid ya ya rike kafanshi sai tsinannen sojan nan bugama yaya Hamid kanbindiga da yakeda wuka ajiki sau biyu ya bugamasa agoshi😭😭😭wanda yasa yaya Hamid baikara motsi mai karfiba. Sai sojan yakecema wani sojan wai yaya hamid zaiyi fada dashi ne, sai wancan yace ai suna son masu asiri irin mu sai yace mana muna jin labarin kashe kashen da akeyi a maiduguri to sune sukeyi suna kuma kama mutum suci naman shi danye ko gasashshe. Sai wani acikin su ya kunna waka a wayansa yace mana "wannan wakan itace wakan da zamuji na karshe a duniya , gobe zasu kaimu dajin birnin gwari su harbemu, ko kuma su barmu ciwon da yace jikin mu ya karasa mu to ni alokacin Alhmdll nafi kowa lafiya acikinmu, anyi min harbi daya ne akafa kuma harbin bai taba kashiba ya fasa nama ne ya fita kuma ana harbina na danne gurin da hannuna sai yazama jinina bai zuba sosai ba kuma koda suna dukan na nakwanta akan kafanda takeda harbinne sai yazama suna dukan marar harbinne shiyasa ma marar harbin yafi mai harbin ciwo. Da misalin karfe 6:30pm sai akace su dauko ambulance din su wanke saboda jininmu ya bata shi sai suka dauko yaya Ahmad. Suna dakko shi naga yayi shahada😭😭😭saboda bakinshi a bude kuma idonshi a rufe daman shi yaya Ahmad tun a inda suka kamamu sunruga sungama dashi dan sun karya hannunsa biyu da kafansa dan dasuka harbe shi akafa sai da kafan yajuya kuma ko motsi bayayi shiyasa yaya Hamid ya damu sosai akan sukai shi asibitiy Ya Allah..

Bayan Sun ciroshi daga ambulance din sai suka sakoshi akan kafan Aliy haidar da suka harbeshi alokacin yaya Hamid ya suma dan yasha duka Sosai kuma yanata zuban jini mujahida ma ya zubarda jini sosai gashi kudaje sunata binmu...

Gabda magrib sai naga yaya hamid ya bude ido yana kallon sama kuma idonsa yana rawa yana fadin wani abu ahankali wanda bamu san meyake cewaba. Shikenan yaya Hamid yayi shahada😭😭😭Ya Allah 

Daga nan baikara motsiba.. Kowani soja yana fadin albarkacin bakinsa na wulakanci sai aka kira sallan magrib sai sukace "bara suje susha ruwa, mu kuma zasu kawo mana giya musha dan munyi azumi sai wani yace dubesu duk yarane sai wani yace masa kai kake ganinsu yaya adai dai lokacin kafan Aliy haidar yanamasa ciwo saboda Sun dora masa yaya Ahmad akan kafan, sai Aliy haidar yace "yaya Ahmad, yaya Ahmad ka daga mun kafana kadaga mun kafana mana"😭😭😭to shi baisan yaya Ahmad yayi shahada ba sai wani soja yace aciremaka shi ne sai Aliy haidar yace masa eh dan Allah kataimaka kacire mun shi sai sojan yace sai dai unnaku yazo ya cire maka shi sai suka watse lokacin magriba ce duhu ya shiga sai Aliy Haidar yace ma mujaheed ka shakeni inmutu sai mujaheed yace masa bazan iyaba sai Aliy yakara ce masa nace ka shakeni in mutu sai mujaheed ya kara cewa nace maka bazan iyaba sai Aliy haidar yace Min Imam sai nace na am sai yace babu wata hanya da zamu gudu?? Sai nace mishi eh babu wata hanya dama ta can kasane da zamu iya fita, amma anan wurin babu hanya saboda anan parade ground dinsu yake, kuma anan gared room dinsu ma anan yake, Shannan Anna manyan ofisoshinsu yake suna kuma akwai flowers kuma nasan suna cikin flowers din sai kawai ga wasu sojoji sunzo, to dama idan suna so sugane mutum yanada rai ko ya mutu dukanmu sukeyi sai kawai suka shiga dukanmu wanda sukaga ya cika sai suce "this one dead" wanda sukaga bai cikaba sai suce "this one is alive"wani ya rubuta atakarda "four of thems are alive, and theer of thems dead" sai suka tafi sai Aliy haidar take min babu wanda ya'iya du'a'u tawassul ne ya karanta sai kowadai yayi abunda yayi sai suka sake dawowa Suka kara dubamu suganmu dai yanda suka barmu sai suka tafi 


da misalin 8:30/9:00pm sai ga wasu mahaukatan sojoji (gallant) sun shigo da tankokin yaki guda biyu, da hellux hellux suka zagayemu akace sukunna fitulun motocin suka haskemu sunada yawa sosai sai suka fara tambayan sunayen mu suna video covering suma suka kara tanbayan ina 'ya'ya malam? Sai aka nuna masa sai suka tafi anan nasan albarkacin du'a'u ne yasa basu iya yimana komai ba dan wa 'yannan zasu iya cinyemu danye wasuma bazasu samuba.. 


Bayan kaman 30mint saiga wannan babban sojan na farko mai fararan shadda wanda yace sukai mu asibiti basukai muba yazo ya kara cewa su dauke mu su kaimu asibitiy daman akwai wasu sojoji da zasuje change duty sai yace su tafi damu su kai mu amergency, in sunkai mu sai su wuce, sai aka fara dora wannan wanda nace bansan kowayeba amota sai yaya Ahmad kan mutumin sai yaya Hamid akan yaya Ahmad sai akasaka Ayuba sai mujaheed sai Aliy haidar sai kuma ni akarshe sai shi wannan babban sojan yajaddada musu sukaimu asibiti yazo yayi mana addua take take Allah tsare ya kiyaye gaba sai sauran sojojin suka hau motan zamufara tafiya sai nima nace mishi "mungode Allah ya saka da alkhairy"Muka tafi motan tana gudu sosai..


ALOKACIN DA AKA KAIMU ASIBITIN SHIKA


Ankarusa damu kofan emergency room suka tsaya.daman nine a bakin kofa sai sojan yace insakko sai nace bazan iya sakkowa ba sai ya fallamun zazzafan mari sai da na fado kasa, suka sakko da sauran ina zaune na tokare hannuna a kasa ta baya sai wani sojan ya takamin yatsu da karfi nai sauri na janye hannun sai yasa takalmin sa(boot) ya bugeni a fuska sai da kaina ya hadu da kasa sai suka koma kan Aliy haidar suka dukeshi sosai duka mai sunan duka Suka koma kan mujaheed shima sukamai nashi dukan sai Ayuba shi yasha duka sosai sai suka kara dukana sosai har wani soja yace fire him sai wani yace kyalesu ciwon da ke jikinsu ya karusa su sai suka hau mota suka tafi suka barmu anan. ALLAH YAISA 


Munan sai Nurses din asibitin sukazo amma kaman suna jin tsoran sutaba mu alokacin nasan yaya Ahmad yayi shahada amma ban yadda yaya Hamid yayi shahada ba sai na taba cikin yaya Ahmad sai naji dimi kadan sai kafansa kuma yayi sanyi har ta fara fitowa ajikin safan sa sai nacema wani ya taba mun yaya Hamid yaji sai ya Kama hannun sa yaji yayi karfi sai yace min yayi ya mutu (shahada)! Sai wata nurse tace kunada number wani naku akira sai na tambayi sayyid Aliy haidar "kanada number Abba(H)sai yace baidashi nace na umma fa yakara cewa baidashi sai na amshi wayan matan na saka number Abban mu ko dai dai ne ko ba dai dai bane bansani ba nakira bai shigaba sai na saka na ummi na sai naji yashiga sai nace mata dan Allah tasan yanda za'ayi aje a dakko ambulance azo a daukemu mu na asibitin shika sai tace an harbeka ne?sai nace ehh 

Sai naji tafara salati sai na kashe wayan sai Allah yasa natuna da number ummi doguwa sai na kirata sai nace tasan yanda za'ayi azo da mota a dauke mu. Muna asibitn shika sai tace waye kai? sai nace mata kawai muna tare dasu yaya Ahmad ne, ina fada mata haka sai ta rude tace yaya Ahmad! Yaya Ahmad! Sai na kashe wayan. Sai naga oga Ali ne dan ina ganin number nagane sai nadauka nace oga sai yace waye kai sai nace imam naka sai Imamu! Sai Ali haidar ya karbi wayan sai oga ya tambayesa inasu yaya Ahmad sai yace masa mutu! Ba jimawa sai umma (malama) takira wayan sai haidar ya dauka sai tace ina su Ahmad sai haidar yace mata sunyi barci,sai tace ka fadamun gaskiya. Kaga ga Mahmud nanma yayi shahada, ko mai nene kagayamun zan daure sai haidar yace mata Sun mutu!😭😭😭 sai nai sauri nace mai haba Ali bai kamata ka fada ma umma haka ba sai yace min kaine zaka gayamun abunda ya kamata na fada mata? Sai nayi shiru sai unman ta kashe way and. 


To anan ne haidar yayi kuka mai tsanani duk abunda ya faru tun daga filin wakia zuwa bariki da nan asibiti da shahadan su yaya Ahmad bai sa haidar kuka ba sai da yaji Sayyid Mahmud yayi shahada..ya Allah 😭😭😭 

Dalilin kukanshi shine duk wannan wahada da azabtarwan da yasha yayi burin idan ya koma gida yaba ma yayanshi sayyid Mahmud labarin duk abunda ya faru damu . Sai kawai umma tace mai shima yayi shahada ya shiga damuwa matsananci yayi kuka da ihu kamar ransa zai fita Yace daman Allah ya bar nine dan in rama kuma insha Allah sai na rama! nurse din sunata bama haidar hakuri alokacin mujaheed jininshi ya zuba sosai kamar zai mutu sai din sukai sauri suka kaimu cikin emergency room suka kwantar damu, lallai naji tsoron kar sojojin su dawo, sai ga doctor shuaibu ya shigo, sai yasa suka fara dubamu, shikuma ya fara duba Aliy haidar da kanshi. Ansama kowa ruwa amma banda mujahid saboda shi jikinshi yayi tsanani, don ya suma a lokacin. Su yaya Ahmad, Hamid da wanda bansan shiba aka kaisu mutuware sai ga Abban mu da ummi na da uncle shobe sun shigo can sai ga doctor mustapha yazo alokacin doctor mustafa ya dauki mujaheed ya tafi dashi saboda babu isassun kayan aiki a asibitin soboda suna yajin aiki nadan samu barci warin 12Am na farka naga Ali hiadar yana amai sai na tambaya maiyasashi amai sai akace alluranda akai masane kuma da maltina yasha shiyasa da gari ya waye na bukaci zuwa toilet sai akasani a wheelchair aka kaini dazan dawo sai Allah yaban iko na iya da wowa da kafana sai Ali yace daman baka karyeba? sainace eh ban karyeba anzo za'a canza mana asibiti sai akace ga sojoji can Suna harbi a hussainiyya Kuma da yu wuwan sudawo gunmu ta baya shi Kuma Ali aka sashi amota aka fita dashi ta baya. 


A'azamallahu ujurana wa ujurakum bi musabi sayyidina wa maulana Abi Abdullah Husain(As)

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Ya kasaka musu Allah gafartamusu
    Sukuma .allah tsine musu

    ReplyDelete
Previous Post Next Post