Qalubale ko Nasara?:-Matashiyar Tayi Kira Akan Matasa !!!

 MATASA !!! 




Sune kashin bayan kowane al'umma, idan muka raini/tada matasan mu suka zama masu tarbiyya, tausayi, taimako, jinkan junansu, ilimi da aikin yi, to tabbas mun dauko hanya ne ta gyara goben yaranmu da zasu samu anan gaba.


A ko'ina ka gifta ko ka wuce a cikin gari, zaga matasa nata huldodinsu, matasan kuwa maza da mata, daya daga cikin abinda yake bani sha'awa a garinmu shine, duk sanda zan fita daga gida naje wani wuri sai naga abubuwan da zasu koyar dani darasin rayuwa, daga wurin matasan mu, kama daga yanayin ayyukan su, yadda suke kasuwancin su da yadda suke gudanar da ma'amalar su.  Nikansha mamaki sosan gaske idan naga yadda wasu matasan ke aiki tukuru wurin neman halal dinsu, basa sarewa idan zaka wuce sai dubu to zaka ganshi sau dubu, saidai idan rashin lafiya ko wani dalili ya hanashi fitowa, abin yana bani sha'awa idan naga sun aji girman kai, ba kamar yadda wasu keyi ba, suna sana'a kala_kala  hada wacce baka tunanin zasuyi din.


Dana danyi duba da nazari ga wasu abubuwan, sai nagano banbanci karara na matasan dana sani da dakuma na yanzu, ada matasanmu ko sallah aka kira indai shadda ne jikinsa ko yayi wankansa to ba lallai yayi sallahn a wannan lokacin ba, saboda karya Bata karin gugan shaddansa koya bata gayunsa shi dan gayu, amma a yanzu duk tsadan abinda ya saka da an kira sallah zaya nade hannun riga yayi alwala ya shiga masallaci, iri daya ne da sana'a, ada idan kabawa matashi jari na naira dubu arba'in zuwa hamsin, zaya fada maka sunyi masa kadan ne, mema zaya siyo ya saida da wa'yannan kudin ai bazasu isaba, kuma a lokacin komi yana sauki ne, ababen bukata basuyi tsada kamar yanzu ba, sannan babu tsadar rayuwa, amma a yanzu zaka iske matashi a zaune ma yana tsare shago, da kayan da basu wuce na naira dubu ashirin ba, kuma kaga bai mutu ba yana rayuwarsa cikin rufin asiri.


Yanzu duk wannan daukan duniyar da zafi matasa sun barshi ba kamar da ba, sun samawa kansu mafita da kansu, saura dai_daikun matasa suka rage masu irin wannan ra'ayin, amma sauki kam Alhamdulillah an sameshi daga matasanmu.


Matasa kashin bayan al'ummah, inajin dadi naga wa'yannan kashin bayan da ake magana sun zama na gari wallahi, Allah kasa mu zama daya daga cikin na garin, ya rabb.



✍️_ Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post