Muna Bin Gwamnatin Goodluck Jonathan Bashin Jinin Yan Uwanmu 33



 A ranar wata Juma'a 28 ga watan Ramadan wanda wannan Juma'ar itane Juma'ar ƙarshe a Shekarar 1435 Gwamnatin Nijeriya Karkashin Jagorancin shugabanta a lokacin Goodluck Ebele Jonathan ta afka mana a wannan ranar a garin Zaria a daidai lokacin da ake gabatar da Muzaharar kin amincewa da kashe Al'ummar kasar Palestine da Isra'ila keyi tsawon Shekaru masu yawa da kuma bayyanawa duniya cewa Masallacin Qudus na Musulmi ne. Idan Allah ya kaimu ranar Litinin 28 ga watan Ramadan shine yake alamta shekaru 7 kenan dai-dai da wannan ta'addancin na Gwamnatin Goodluck Jonathan akan almajiran Sheikh Zakzaky.


 Gwamnatin Goodluck Jonathan ta afka mana ne ta hanyar turo sojojinta karkashin Kwamandansu Laftanar Kanal Samuel Oku (S.O) a dai-dai lokacin da Muzaharar ke gudana a garin Zaria, inda suka yi kwanton ɓauna a cikin wata gonar Rake ba tare da masu Muzaharar sun sani ba kawai su fara sake ruwan wuta da harsasai masu rai akan yan uwan mu masu Muzaharar. A wannan ranar suka Shahadantar da yan uwanmu da daman gaske ciki har da 'ya'yan Jagoranmu Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) guda uku (Ahmad, Hamid, Mahmud) wanda dukkansu suna karatun Degree ne a kashen waje, da kuma wasu yan uwa mutum 30 ciki har da wani Kirista mai suna Julios Anyawou da ya fito yana tuhumarsu akan dalilin da yasa suke harbinmu.


 An gabatar da Jana'izarsu kamar yanda addinin Muslunci ya tanada a ranar 29/Ramadan/1435 dai-dai da 26/7/2014 a garin na Zaria bayan an karbo sauran gawarwakin da Jami'an tsaron suke tafi dasu barikinsu na Soja. An Kuma biznesu a Darur-Rahama dake Dembo a garin Zaria. Yanzu haka kabarinsu yana wajen duk da cewa Gwamnatin Buhari ta rushe muhallin a Shekarar 2015 bayan harin Ta'addanci da gwamnatin Buharin ta kai itama a ranar 12/12/2015, inda ta kashe al'umma almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky fiye da dubu tare da rushe duk wani wurare mallakin Harka Islamiyya. 


 Kusan shekara ɗaya ne da watanni 4 da yin wannan ta'addancin na Qudus sai gwamnatin Jonathan ta sauka daga karagar mulki ta mikawa gwamnati mai ci a halin yanzu (gwamnatin Buhari), ita kuma a ƙarshen wannan shekarar ranar 12/12/2015 ta dira da kisan kiyashi akan almajiran Sheikh Zakzaky bayan sun tsara yanda zasu nunawa al'umma cewa basu da laifi. Sun afka mana ne da sunan mun tare hanya ga kwamandan Soji a lokacin inda har su fitar da wani bidiyo na ƙarya domin kare kansu, daga baya kuma al'umma su fahimci ba haka bane dama da wata manufar aka dirar mana.


 Don haka muna bin bashi jinin yan uwanmu mutum 33 da Gwamnatin Jonathan ta kashe mana ciki har 'ya'yan Malaminmu wanda sun kasance hazikai a bangaren karatu. Allah ya dauka mana fansar yan uwanmu da gwamnatocin Nijeriya ke kashe mana tun farkon wannan da'awa har zuwa yanzu, ya kuma tabbatar mana da dawowar addini a wannan Nahiya tamu dama Duniya baki daya. Idan Allah ya kaimu gobe almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky ɗin zasu fito a garuruwa daban-daban domin nuna rashin amincewa da kisan da ake yiwa Musulumin Falasɗinu kamar yanda ake yi a sauran sassa na Duniya.


Daga Wakilinmu

 - Ibrahim Almustapha Saminaka

 - 24/Ramadan/1442
 


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post