Menene matsalarku game da ayyukan magabata, alhali ba za a tambaye ku a kansu ba ??


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


TAMBAYAR DA MUKE SON JIN AMSARTA DAGA BAKIN 'YAN SHI'AH


Abu ne mai sauqi wanda bai kamata ace mutum na wahalar da kansa kan abinda gobe Qiyama ba za ayi masa tambaya a kansa ba. Abinda yafi muhimmanci shine mutum ya shagaltu kawai wajen aikata abinda zai amfanar dashi a lahirarsa. 


Wani abinda yake bamu mamaki game da 'yan Shi'ah shine, a ko da yaushe za kaji suna yawan magana kan abinda ya faru cikin magabata game da sha'anin Khalifanci, kisan Hussaini ko kuma sanin wanene yafi girman matsayi cikin abokan Annabi (S. A. W. W).


Har ma kaji suna qoqarin nuna cewa wane yana da laifi ko kuma suce wane ya aikata kaza wanda a qarshe sukan kai su wuta. Mu kuma sai muna ganin irin wannan tone-tonen nasu ba zai amfanar dasu komai ba, domin su magabatan sun riga sun sude, kuma su masu wannan aiki ba za a tambaye su aikin magabatan ba. 


Allah madaukakin Sarki na cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



" تِلۡكَ أُمَّةٞ قَدۡ خَلَتۡۖ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَلَكُم مَّا كَسَبۡتُمۡۖ وَلَا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ."( ٤٣١)


" WADANCAN AL'UMMU NE DA SUKA RIGA SUKA GABA TA, TANA DA ABINDA TA AIKATA (na alkhairi ko sharri) KUMA KU MA KUNA DA (sakamakon) ABINDA KUKA AIKATA. SANNAN KUMA BA ZA A TAMBAYE KU GAME DA ABINDA SUKA KASANCE SUNA AIKATAWA BA. "


(Suratul-Baqarata, aya ta 134)


Saboda haka mu bamu ga wata hujja daga gare ku ('yan Shi'ah) ku damu da yawan maganganu ko rubuce-rubuce kan abinda ya shude cikin al'ummar da ba za a tambaye ku akan ayyukansu ba.


      AMSAR TAMBAYARKA 


Munji tambayarka yaa Ustaz, kuma mun fahinci bayanan da kayi, sannan mun yarda da ayar daka kafa mana hujja da ita.


Sai dai abu na farko da muke so ka fahinta shine, wannan gargadi na cikin ayar da ka kawo ana yinta ne ga Yahudawa da kuma mushirikan zamanin Manzon Allah (S. A. W. W) game da al'ummun da suka gabata. Wato al'ummar su Annabi Ibrahim, Isma'il, Ishaq da irin su Annabi Ya'aqub (A. S). 


Mu kuma al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) ce, tun daga kan Sahabban da suka rayu da Annabi (S. A. W. W) har zuwa kan wadanda za suzo nan gaba a qarshen zamani . Domin Annabinmu daya ne, littafinmu daya ne, saqon da aka zo mana dashi kuma aka barmu a kansa daya ne, sannan kuma mu da su duk a kansa za a tambaye mu. Saboda haka duk wani abinda za mu ambata a kansu ba wai muna magana kan wata al'umma bace.


Annabin da aka aiko mana mu da su ya tafi ya barmu kan wani tsari na jagoranci qarqashin Khalifofi 12 wandanda yace mu bi su cikin komai namu na rayuwa. Wannan abu kuwa nanan rubuce cikin littafan wannan zamanin namu kuma cikin wannan al'umma tamu, sai kuma ya zama abinda ake yi ko ake bi na zahiri ya sha bamban da abinda ke rubuce cikin littafan dake gabanmu.


Saboda haka ya zama haqqi a kanmu mu bayyanar da gaskiyar yadda addini yake da kuma sanin suwaye haqiqanin addini, domin an riga an cakuda qarya da gaskiya cikin muslimci kuma a haka ake so a tafiyar dashi.


To, lalle haka ba zai taba yiwuwa a gare mu muyi shiru ba tare da bayyanar da gaskiya da kuma ahlinta ba, domin idan muka yi shiru sai Allah ya tambaye mu gobe qiyama. Domin kuwa Allah (T) na cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" وَلَا تَلۡبِسُواْ ٱلۡحَقَّ بِٱلۡبَٰطِلِ وَتَكۡتُمُواْ ٱلۡحَقَّ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ." (٢٤)


" KUMA KADA KU LULLUBE GASKIYA DA QARYA , SANNAN KU BOYE GASKIYA ALHALI KUNA SANE ."


      (Baqara, aya ta 42)


Yanzu Kai a tunaninka kana ga ya dace mubar al'umma su tafi cikin wannan rudani na yin addini baibai sannan kuma ace mu sami mafita wajen Allah ? Anya idan muka yi haka ba za mu shiga cikin sahun masu boye ilimin da Allah ya ba su ba? 


Ya zo cikin sharhin wannan aya kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


يقول تعالى ناهيا لليهود عما كانوا يتعمدونه من تلبيس الحق بالباطل وتمويهه به وكتمانهم للحق وإظهارهم الباطل « ولا تلبسوا الحق بالباطل وتكتموا الحق وأنتم تعلمون » فنهاهم عن الشيئين معا وأمرهم بإظهار الحق والتصريح به ولهذا قال الضحاك عن ابن عباس « ولا تلبسوا الحق بالباطل » لا تخلطوا الحق بالباطل والصدق بالكذب وقال أبو العالية « ولا تلبسوا الحق بالباطل » يقول ولا تخلطوا الحق بالباطل وأدوا النصيحة لعباد الله من أمة محمد صلى الله عليه وسلم ويروى عن سعيد بن جبير والربيع بن أنس نحوه وقال قتادة « ولا تلبسوا الحق بالباطل » ولا تلبسوا اليهودية والنصرانية بالإسلام وأنتم تعلمون أن دين الله الإسلام وأن اليهودية والنصرانية بدعة ليست من الله وروي عن الحسن البصري نحو ذلك وقال محمد بن إسحاق حدثني محمد بن أبي محمد عن عكرمة أو سعيد بن جبير عن ابن عباس «وتكتموا الحق وأنتم تعلمون » أي لا تكتموا ما عندكم من المعرفة برسولي وبما جاء به وأنتم تجدونه مكتوبا عندكم فيما تعلمون من الكتب التي بأيديكم


Allah (T) na fada wajen hani game da Yahudawa bisa abinda suke yi na lullube gaskiya da qarya da kuma murguda shi da boye shi daga gaskiya, da kuma bayyanar dashi bisa qarya. 


" KUMA KADA KU LULKUBE GASKIYA DA QARYA KUMA KU BOYE GASKIYA ALHALI KUNA SANE ."


Sai ya hane su daga irin wannan lullubewar kuma ya umarce su bayyanar da gaskiya da kuma aiwatar da ita. Saboda haka ne ma Dhahaak ya kawo daga Ibn Abbas; 


" KUMA KADA KU LULLUBE GASKIYA DA QARYA "


Kada ku cakuda gaskiya da qarya (ta yadda za a kasa bambance tsakaninsu) kuma ku riqa gaskata qarya (da sanin ku). Abu Aliyata yace; 


" KUMA KADA KU LULLUBE GASKIYA DA QARYA " 


Yana cewa kada ku cakuda qarya da gaskiya kuma ku bar yin nasiha ga bayin Allah daga cikin al'ummar Muhammad (S. A. W. W). 


Sannan aka riwaito daga Sa'eed Bn Jubair da Rabi'a Bn Anas misalin wannan magana (ta sama), kuma Qatadata yace; 


" KUMA KADA KU LULLUBE GASKIYA DA QARYA " 


Kuma kada Yahudawa da Nasara su lullube muslimci alhali suna sane cewa addinin Allah shine muslimci, kuma Yahudanci da Nasaranci Bid'ah ce ba daga Allah ba. Sannan an riwaito daga Hassanul-Basariy misalin haka.


Muhammad Bn Ishaq yace; Muhammad Bn Abiy Muhammad ya bani labari daga Ikramata ko Sa'eed Bn Jubair, daga Ibn Abbas (R. A) 


" KUMA KU BOYE GASKIYA ALHALI KUNA SANE ."


Abin nufi shine, kada ku boye abinda ke tare da ku na sanin Manzon Allah (S. A. W. W), da kuma (boye) abinda yazo dashi alhali ku din kun same shi rubuce a wajenku cikin abinda abinda kuka sani na daga littattafan dake hannayenku. 


(TAFSIR NA IBN KATHEER) 


Saboda haka muma cikin Littafan dake hannayenmu akwai wasiyyar Manzon Allah (S. A. W. W) cewa Khalifofinsa shiryayyu masu shiryarwa a bayansa su 12 ne, kuma koyi dasu shine addini. 


To, sai ya zama ba wadannan 12 ne ake nunawa al'umma a matsayin jagorori ba, wasu dabam ake danqarawa mutane kuma muna sane. Sannan kuma an shan wadanda suka yi wannan mugun aiki, amma bisa irin tunaninka kana ga ya dace ace muyi shiru kenan ?


Sannan kuma kana kwatanta su da wata al'umma kana cewa ba za a tambaye mu abinda suka aikata ba. To, su ka cire su daga al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) ne ?


IDAN KU KUNCI AMANAR ADDINI NE MU BA ZA MUCI BA !


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda daga.


       (08137925034)


1st May, 2021/ 19th Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post