Matuqar Aliyu Na Raye Babu Mai Tsayawa A Madadin Annabi In Ba Shi Ba.. !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MUNAFUKI BA ZAI TABA SON IMAM ALI (A. S) BA 


Abu ne wanda kake gani kamar da mamaki ace musulmi ya nuna cewa ba ya son Imam Ali (A. S), domin idan an tashi ambaton makusantan Annabi (S. A. W. W) za kaji an sa Imam Ali (A. S) cikin jerin mutane hudu (4).


Lalle ba anan Gizo ke saqar ba, wata siyasa ce kawai mutane ke yi wajen sako Imam Ali (A. S) cikin mutanen kirki wadanda suka rayu da Annabi (S. A. W. W), amma a haqiqa shi maqiyi ne a wajensu don kuwa ya kashe iyaye da kakanninsu a guraren yaqoqi mabambanta. 


Za ka iya fahintar maqiyinsa ne kawai yayin da ka ambaci wani matsayi nasa wanda Allah da Manzonsa (S. A. W. W. W) ya fifita shi kan kowa daga cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) .



Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


.«4083» حدثنا واصل بن عبد الأعلى حدثنا محمد بن فضيل عن عبد الله بن عبد الرحمن أبي النصر عن المساور الحميري عن أمه قالت دخلت على أم سلمة فسمعتها تقول كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: ((لا يحب عليا منافق ولا يبغضه مؤمن)).

قال: وفي الباب عن علي. وهذا حديث حسن غريب من هذا الوجه. وعبد الله بن عبد الرحمن هو أبو نصر الوراق وروى عنه سفيان الثوري.



Wasil Bn Abdul-A'alah ya bamu labari, Muhammad Bn Fudhail ya bamu labari daga Abdullahi Bn Abdurrahman baban Nadhari, daga Masawiri Al-Humairiy, daga Babarsa tace, " Na shiga wajen Ummus-Salamata sai na jita tana cewa, Manzon Allah (S. A. W. W) ya kasance yana cewa; 


" MUNAFUKI BAI ZAI SO ALIYU BA, SANNAN KUMA MUMINI BA ZAI QI SHI BA ."


..........................................


Cikin wannan hadisi za mu fahinci cewa ashe duk inda ka sami masoyin Imam Ali (A. S), to mumini ne. Sannan kuma duk inda munafuki yake komai qanqantarsa ko girmansa ba zai taba son Imam Ali (A. S). Saboda haka ne a duk lokacin da aka kawo wata falala tasa sai ta sosa zuciyar wane, to, wannan mutumin munafuki ne. 


4084» حدثنا إسماعيل بن موسى الفزاري ابن بنت السدي حدثنا شريك عن أبي ربيعة عن ابن بريدة عن أبيه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((إن الله أمرني بحب أربعة وأخبرني أنه يحبهم)). قيل يا رسول الله سمهم لنا. قال: ((علي منهم يقول ذلك ثلاثا وأبو ذر والمقداد وسلمان أمرني بحبهم وأخبرني أنه يحبهم)). قال: هذا حديث حسن غريب لا نعرفه إلا من حديث شريك.


Isma'il Bn Musa Al-Fazaariy Ibn Bnt Saddiy ya bamu labari, Shuraiku ya bamu labari daga baban Rabi'ata daga Ibn Buraidata daga babansa yace; Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" LALLE ALLAH YA UMARCENI DA NASO MUTANE HUDU (4), KUMA YA BANI LABARI CEWA SHI MA YANA SONSU. " Aka ce, yaa Ma'aikin Allah (S. A. W. W), ka ambata mana su (don mu sansu mana). Yace; 


" ALIYU NA DAGA CIKINSU. " Sau uku yana fadin haka. 


" DA ABU ZARR, DA MUQDAAD, DA KUMA SALMANU. YA UMARCE NI DA SONSU, KUMA YA BANI LABARI CEWA SHI MA YANA SONSU. "


Tirmidhi yace, wannan hadisin mai kyau ne, saidai baqo ne, domin bamu san shi ba sai ta hanyar Shuraiku. 


Cikin wannan hadisi kuma za muga cewa wadannan bayin Allah guda hudu (4) muminai ne wadanda suka sami shaida daga Annabi (S. A. W. W) ta hanyar mai komai mai duka (Allah). 


Kuma za muga wadannan tafiyar tare suka riqa yinta, domin suna daga cikin wadanda suka qi yiwa Abubakar Mubaya'a bisa hujjarsu ta cewa ba shi Annabi (S. A. W. W) yace subi a bayansa ba. 


4085» حدثنا إسماعيل بن موسى حدثنا شريك عن أبي إسحاق عن حبشي بن جنادة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((علي مني وأنا من علي ولا يؤدي عني إلا أنا أو علي)).

قال أبو عيسى: هذا حديث حسن غريب صحيح.


Isma'il Bn Musa ya bamu labari, Shuraiku ya bamu labari daga baban Ishaq, daga Habshiy Bn Junadata yace; Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" ALIYU DAGA GARE NI YAKE, NIMA DAGA GARE SHI NAKE, KUMA BABU MAI TSAYAMIN (a matsayina) SAI DAI NI (da kaina) KO KUMA ALIYU. "


Baban Isah Attirmidhi yace, wannan hadisi mai kyau ne baqo (saboda ba a kawo shi ta hannayen mutane da yawa ba) kuma ingantacce ne (a chain of transmission nasa). 



(SAHIHUL-TIRMIDHI, KITABUL FADHA'IL, BABUN MANAQIBUL-ALIYU)


Za mu iya fahintar haka, domin a shekara ta 9 Bayan Hijra yayin da Annabi (S. A. W. W) ya tura Sahabbansa zuwa aikin Hajji kuma yace Abubakar ya jagorance su tare da karanta musu ayoyin Bara'ah, sai daga baya ya tura Imam Ali (A. S) akan yaje duk inda ya same shi ya karbi wadannan takardu ya karanta su ga Mahajjata, domin mai tsarki ne ke haramta shirka da kafirci. 


YAA ALLAH KA QARA MASA SOYAYYAR WANDA KAKE SO IMAM ALI (A. S). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


15th May, 2021/ 4th Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post