Mahdin Musulmi Cikin Littafin Ahlus-Sunnah, Ku Kuma Yan Shi'ah Ina Naku Mahdin??


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Abu ne sananne cikin duniyar muslimci an hadu kan cewa akwai Mahdi wanda zai zo a qarshen zamani don 'yanto da addinin muslimci ya mayar dashi tamkar yadda yazo zamanin Manzon Allah (S. A. W. W). 


Sabanin da aka samu shine 'yan Shi'ah na ambaton wani Mahdin da suke cewa shine wanda Annabi (S. A. W. W) yayi magana a kansa. Su kuma Ahlus-Sunnah suka ce ba shi bane, su nasu ba a haife shi ba, saboda haka ba asan asalinsa ba, sai dai kawai ansan sunansa iri daya ne dana Manzon Allah (S. A. W. W) . Kan haka suke tsinewa wanda 'yan Shi'ah ke ambata a matsayin Mahdin Muslimci, idan ka nemi qarin bayani kan nasu Mahdin sai su kasa kawowa saboda basu san shi a karatu ba. 


To, yau za mu taimake su wajen kawo musu wanene wannan Mahdin cikin littafansu, su kuma 'yan Shi'ah sai su nuna mana nasu. 


MAHDI CIKIN LITTAFAN SUNNAH 


Wasu riwayoyi ne za mu kawo cikin SAHIH NA IBN MAJAH daya daga cikin manyan ingantattun littafan sunnah guda shida. Ga su kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


4223- حدثنا عثمان بن أبي شيبة حدثنا أبو داود الحفري حدثنا ياسين عن إبراهيم بن محمد ابن الحنفية عن أبيه عن علي قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((المهدي منا أهل البيت يصلحه الله في ليلة)). 


Usman Bn Abiy Shaibata ya bamu labari, Abu Dawud Al-Hafriy ya bamu labari, Yaseen ya bamu labari daga Ibrahim Bn Muhammad Ibn Hannafiyyah, daga babansa daga Aliyu yace; Manzon Allah (S. A. W. W) yace, 


" SHI MAHDI DAGA GARE MU AHLUL-BAIT YAKE, ALLAH ZAI YI GYARE DASHI CIKIN DARE (daya). "


Wannan hadisi na nuna mana ne cewa ashe Mahdi daga iyalan gidan Manzon Allah (S. A. W. W) yake. 


4224- حدثنا أبو بكر بن أبي شيبة حدثنا أحمد بن عبد الملك حدثنا أبو المليح الرقي عن زياد بن بيان عن علي بن نفيل عن سعيد بن المسيب قال: كنا عند أم سلمة فتذاكرنا المهدي فقالت سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: ((المهدي من ولد فاطمة))


Abubakar Bn Abiy Shaibata ya bamu labari, Ahmad Bn Abdulmalik ya bamu labari, baban Mulaih Ar-Raqqiy ya bamu labari daga Ziyaad Bn Bayyana, daga Aliyu Bn Nufail, daga Sa'eed Bn Musayyib yace; " Mun kasance zaune wajen Ummus-Salamata muna ambaton Mahdi, sai tace, " Na ji Manzon Allah (A. A. W. W) na cewa; 


" SHI MAHDI DAGA 'YA'YAN FADIMATU YAKE ."


Wannan riwaya tazo da ma'ana iri daya data hadisi na sama. 


4225- حدثنا هدية بن عبد الوهاب حدثنا سعد بن عبد الحميد بن جعفر عن علي بن زياد اليمامي عن عكرمة بن عمار عن إسحاق بن عبد الله بن أبي طلحة عن أنس بن مالك قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: ((نحن ولد عبد المطلب سادة أهل الجنة أنا وحمزة وعلي وجعفر والحسن والحسين والمهدي)). 


Hadiyyata Bn Abdul-Wahhab ya bamu labari, Sa'ad Bn Abdu Al-Humaid Bn Ja'afar ya bamu labari daga Aliyu Bn Ziyaad Al-Yamaniy ya bamu labari daga Ikramata Bn Ammar, daga Ishaq Bn Abdullahi Bn Abiy 'Dalhata, daga Anas Bn Malik yace; " Na ji Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa; 


" MUNE 'YA'YAN ABDUL-MUDALLIB YARDADUN (masu babban rabo na) 'YAN ALJANNAH. NI DA HAMZA DA ALIYU DA JA'AFAR DA HASSAN DA HUSSAINI DA KUMA MAHDI. 


(IBN MAJAH, KITABUL FITANI, BABUN KHURUUJIL MAHDI)


Wannan shine Mahdin da Annabi (S. A. W. W) ya ambaci zuwansa a qarshe duniya don kawar da zalunci da kuma ni'imtar da qasa bayan ta cika da zalunci, qunci da kuma qazanta.


Da nayi nazarin wadannan hadisai sai naga ai shine wanda 'yan Shi'ah ke magana a kansa, domin suna cewa ne Jikan Manzon Allah (S. A. W. W) ne kuma 'Da ga Sayyidah Fatimah (S. A). Sai dai kuma Sunnah suna cewa ba shi bane, kan haka suke tsine masa tare da kafirta masu cewa shine wanda Annabi (S. A. W. W) yayi busharar bayyanarsa. 


Kafin gabatar da wannan rubutu nake cewa 'yan Shi'ah su kawo nasu Mahdin, domin Sunnah sun kawo nasu cikin littafansu. Sai dai kuma da nayi nazari sai naga ai wannan Mahdin da aka kawo cikin littafin Sunnah shine dai wanda 'yan Shi'ah ke maganarsa kuma suke kawo shi har da cikakkiyar nasabarsa wacce take qarewa kan Sayyidah Fatimah (S. A) kamar yadda aka kawo cikin littafin sunnah. 


Daga nan ne kuma tunanina ya canza zuwa tambayar Ahlus-Sunnah cewa ai wannan Mahdin na 'yan Shi'ah suka kawo. To, su ina nasu na Sunnah wanda ya saba da wanda 'yan Shi'ah ke kawowa ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


14th May, 2021/ 3rd Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post