Kun harbe gwamanatin ku, tun ranar da ku ka harbi Malam Zakzaky (H) - Inji Shaikh Yakubu Yahaya Katsina.


 

“...Ba Muzahara suke tsoro ba? To ko dokar Najeriya ta zarartar ina ji ko tu'o'o nawa ne...suka zarartar da hukuncin cewa ba buƙatar ma ka tambayi Ɗan sanda in zaka yi Muzahara abinda ke nasa shi ne ya rakaka ya gani kar ka yi ɓarna...Ko wani abu mai kama da haka, shi ne haƙƙin Ɗan sanda. Amma na miye ku amshi kuɗi ƙasar waje dan ku kashe al'ummar ƙasar ku? Sa'udiyyar nan da ta'ke yaƙar Shi'a da ’yan Shi'a a ɗabib, da Ihsa da madina cike ta'ke da 'yan Shi'a, bilhasali ma duk man fetur ɗin da saudiyya ke da shi daga ƙasar 'yan Shi’a ta’ke haƙo shi... to ku sai a baku kuɗi ku kashe na ƙasar ku? wannan wane irin rashin wayau ne? To yanzu mi yage rage maku duka shekara biyu ta rage maku ku sauka... Tunda KUN HARBE GWAMNATINKU TUN RANAR DA KUKA HARBI MALAM ZAKZAKY (H), Gwamnatin Ta Watse Ba'ta Kawai Sai Bisa Takarda.


Har Amerika da ta saku, tunda magana ɗaya ne, Amerika, Isra'ila, Saudiyya duk abu ɗaya ne, to har ita sai da ta dawo tayi ribas amma ku kuna nan akan bakanku. Amerika tayi ribas ta ce “Malam (Zakzaky) is a Political Prissoner” ba mai laifi bane siyasa ce ta sa aka tsare shi kwanan na haka John Biden ya faɗa (Malam Fursunan siyasa ne ba mai laifi bane, ba criminal ba ne) kuma suka fito ƙarara suka ce; Najeriya ba 'yancin addini, amma mutane sun ɗaukar ma kansu, da yake ba mai taka masu burki ba mai komai.


To shi ke nan akwai jan layi ai, kuna ta tarawa ranar da kuka taka jan layi, Allah Ya kwance maku zani a kasuwa a ganku yadda kuke kuma kusa ta’ke...”


jawabinsa bayan kammala karatun Tafseer zama na 23 a ranar Talata 22/9/1442-4/5/2021.


Daga shafin Bin Yaqub Katsina✍🏾

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post