@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KU TAMBAYI MA'ABOTA SANI IDAN KU BAKU SANI BA
" فَسْئَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لا تَعْلَمُونَ ."
Addini ba ya taba yiwuwa sai da ilimi, kuma shi ilimi ba a samunsa dole sai an neme shi. Kamar dai yadda aka san kudi ne ba a samunsa sai an neme shi, ko da kuwa hanyar neman bata tsawaita ba, domin wasu in sun tashi neman sukan same su ilimi/kudi cikin sauqi.
Sannan ba zunzutun karatu ne neman ilimi ba, a'a, ta hanyar tambaya ko saurare ma mutum kan sami ilimi. Ba kuma ina nufin mutum ya dogara da tambaya ko saurare kadai bane, ya kasance mai sanya littafi a gaban malami na haqiqa yana yin karatu, domin wasu malaman yin karatu a gabansu wata mummuniyar guba (poison) ne, domin za su iya dora ka zuwa ga halaka, ko kuma su karantar da kai qarya da sunan baka karatu.
Na ambaci qarya ne saboda akwai mutane da dama wadanda suka dade suna karatu, amma yanzu sai ana fitar da wasu karatuka cikin abinda suka karanta amma basu gano haka ba, wannan kuwa na da alaqa ne da irin gurbataccen karatun da aka basu.
Ya zo cikin riwayoyi kamar haka;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
(1)- الخصال ابْنُ الْمُغِيرَةِ بِإِسْنَادِهِ عَنِ السَّكُونِيِّ عَنْ جَعْفَرٍ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ: الْعِلْمُ خَزَائِنُ وَ الْمَفَاتِيحُ السُّؤَالُ فَاسْأَلُوا يَرْحَمُكُمُ اللَّهُ فَإِنَّهُ يُؤْجَرُ فِي الْعِلْمِ أَرْبَعَةٌ السَّائِلُ وَ الْمُتَكَلِّمُ[1] وَ الْمُسْتَمِعُ وَ الْمُحِبُّ لَهُمْ.
Daga Khisaal na Ibn Mugeerata, da isnadinsa daga Sakuniyyi, daga Ja'afar, daga babansa yace :
" SHI ILIMI WATA TASKA CE, KUMA MABUDINTA SHINE TAMBAYA. KUYI TAMBAYA SAI ALLAH YAYI MUKU RAHMA, DOMIN CIKIN ILIMI MUTUM HUDU (4) KAN SAMI LADA.
(1)- MAI TAMBAYA.
(2)- DA MAI YIN MAGANA (malamin).
(3)- DA MAI SAURARE.
(4)- DA MAI SONSU. "
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 197
Saboda haka dole ya zamana cewa mun nemi ilimi kuma mu kasance masu tambaya don inganta addininmu.
Zama ba tare da neman ilimi ko yawan tambaya kan al'amran addini ba ya zama babbar hasara da halaka. Kuma ya zama lazim muna karatu da tambaya wajen masana na haqiqa ba wadanda suka yi karatun Sarakuna biya musu buqatunsu ba.
ALLAH YASA MU DACE
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
19th May, 2021/ 8th Shawwal, 1442.