Na Dade Ina Nazarin Ayoyin Kafin in Yanke Wannan Hukunci !!!

Ku Qara Juriya Ƴan Shi'ah, Don Ku Kuke Kan Gaskiya..!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


NA DADE INA NAZARIN AYOYI KAFIN YANKE WANNAN HUKUNCI


Ganin yadda kiraye-kiraye yayi yawa cikin addinin muslimci daga bakunan malamai ko naje jagororin cikinsu yasa na tsunduma wajen bincike da nazarin wacce murya ce tafi zuwa daidai da muryar da'awar Manzon Allah (S. A. W. W). 


Dalili kuwa shine, kowacce muryar na da'awar ita ce mafificiya cikin dukkan wata da'awa ta muslimci. Ni kuma a matsayina na musulmi me neman gaskiya nada ya dace na nazacin dukkan wadannan da'awowi tare da suna su da ayoyin Alqur'ani da Hadisi a matsayin hanya mafi girma ta gane inda gaskiya take. 


Ayoyin dana ci karo dasu kuma na nazarce su sannan na auna su da wadannan muryoyi na musulmi sune inda Allah (T) ke cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تَدْخُلُواْ الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَأْتِكُم مَّثَلُ الَّذِينَ خَلَوْاْ مِن قَبْلِكُم مَّسَّتْهُمُ الْبَأْسَاء وَالضَّرَّاء وَزُلْزِلُواْ حَتَّى يَقُولَ الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ مَعَهُ مَتَى نَصْرُ اللّهِ أَلا إِنَّ نَصْرَ اللّهِ قَرِيبٌ."


" KO KUNA TSAMMANI KU SHIGA ALJANNAH NE (haka kawai) BA TARE DA MISALIN ABINDA YA SAME WADANDA KE GABANKU BAI SAME KU BA ? WAHALOLI DA CUTARWA TA SUN SHAFE SU, KUMA AKA TSORATAR DASU (ta kowacce irin fuska) HAR MANZONSU DA WADANDA SUKA YI IMANI TARE DASHI SUKE CEWA, " YAUSHE TAIMAKON ALLAH ZAI ZO NE ?" KU SAURARA, LALLE TAIMAKON ALLAH NA KUSA ."


          (BAQARA:214)


To, cikin wannan bayanai dake cikin wannan aya sai ya fassara min irin abinda ke faruwa ga 'yan Shi'ah yafi kama da abinda ya faru ga wadannan magabatan da ake bamu misalinsu. 


Kwatsam ! Sai naci karo da wannan hadisi kamar haka; 


جاء في الحديث الصحيح عن خباب بن الأرت قال قلنا يا رسول الله ألا تستنصر لنا الا تدعو الله لنا فقال إن من كان قبلكم كان أحدهم يوضع الميشار على مفرق رأسه فيخلص إلى قدميه لا يصرفه ذلك عن دينه ويمشط بأمشاط الحديد مابين لحمه وعظمه لا يصرفه ذلك عن دينه ثم قال والله ليتمن الله هذا الأمر حتى يسير الراكب من صنعاء إلى حضرموت لا يخاف إلا الله والذئب على غنمه ولكنكم قوم تستعجلون."


Ya zo cikin ingantacce hadisi daga Kabbab Bn Arrat yace, " muka ce yaa Ma'aikin Allah! Yanzu ba za ka roqa mana Allah ba (don samun sauqi daga wannan cutarwar da gallazawar) ? Sai yace; 


" LALLE WADANDA SUKA ZO GABANINKU SUN KASANCE ANA 'DORA ZARTO AKAN TSAKIYAR KANSA 'DAYANSU A RABA SHI (gida biyu) ZUWA DUDDUGENSA, AMMA HAKAN BAI JUYAR DASHI DAGA ADDININSA BA. SANNAN KUMA ANA TSEFE ABINDA KE TSAKANIN NAMANSA DA QASHINSA DA MATAJIN QARFE, AMMA HAKAN BAI JUYAR DASHI DAGA ADDININSA BA ." Sannan yace; 


" WALLAHI ALLAH ZAI CIKA WANNAN AL'AMARI (addini) HAR SAI MAHAYI (rider) YAYI TAFIYA DAGA SAN'A'A ZUWA HADHARAR-MAUT BA TARE DA YANA JIN TSORON KOMAI BA SAI ALLAH, DA KUMA KERKECI AKAN DABBOBINSA. SAI DAI KU MUTANE NE MASU GAGGAWA ."


😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭


Wallahi dana kalli wannan hadisi kawai sai ya hasko min yadda ake zazzage qwaqwalwar 'yan Shi'ah ta hanyar amfani da Bindigogi. Kullum roqon Allah suke ya kawo qarshen al'amarin amma bai qaddara zuwan lokacin ba, kuma su ma basu fasa abinda suke yi ba. 


Sai kawai na qara nutsewa cikin Qur'ani don ganin hujjoji bayyanannu domin na qara samun yaqini kan wadannan mutane 'yan Shi'ah. Sai naci karo da wadannan ayoyi kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



الٓمٓ ( ١)


 أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ (٢ )


وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ (٣)



(1) " ALIF LAAMEEEEEM !"



(2) " SHIN, MUTANE NA TSAMMANIN MU BARSU (haka kawai) SUCE, " MUNYI IMANI (a baka) BA TARE DA MUN JARRABA SU BA ?"


(3)- " HAQIQA MUN JARRABCI WADANDA KE GABANINKU, DOMIN ALLAH YA SAN WADANDA SUKA YI GASKIYA (kan abinda suke yi) KUMA YA SAN MAQARYATA (kan abinda suke yi) ."


(SURATUL-ANKABUT :1-3)


Ganin wadannan ayoyi sai na kalli dukkan da'awowi amma wallahi banga wadanda suka siffantu da ayoyin nan nan sai 'yan Shi'ah.



Ban tsaya anan ba har sai da binciken nawa ya kaini kan wadannan ayoyi masu bayanin yadda Annabi (S. A. W. W) da Sahabbansa suka ci karo da Alqawarin da Allah yayi musu cewa jarrabawa nanan. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" إِذۡ جَآءُوكُم مِّن فَوۡقِكُمۡ وَمِنۡ أَسۡفَلَ مِنكُمۡ وَإِذۡ زَاغَتِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَبَلَغَتِ ٱلۡقُلُوبُ ٱلۡحَنَاجِرَ وَتَظُنُّونَ بِٱللَّهِ ٱلظُّنُونَا۠ ( ٠١)


 هُنَالِكَ ٱبۡتُلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَزُلۡزِلُواْ زِلۡزَالٗا شَدِيدٗا (١١)


 وَإِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ مَّا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ إِلَّا غُرُورٗا (٢١)


            (AHZAB:10-13)



" YAYIN DA SUKA ZO MUKU TA SAMANKU DA KUMA TA QASANKU, YAYIN DA IDANUWA SUKA YI TURU-TURU (don ganin bala'i daga maqiya), KUMA ZIKATA SUKA KAI MAQOSA (kamar za su fashe saboda razana), KUMA KUKA YI TA ZACE-ZACE GA ALLAH. "


" A CAN MUKA JARRABCI MUMINAI (kamar yadda akayi alqawari) KUMA MUKA GIRGIZA SU GIRGIZAWA !"


" KUMA A LOKACIN DA MUNAFUKAI DA KUMA WADANDA AKWAI WATA CUTA CIKIN ZUCIYARSU SUKE CEWA, " BABU WANI ABINDA ALLAH DA MANZONSA YAYI MUSU ALQAWARI (na cewa za a taimake su) SAI DAI RUDI (a fahintarsu) !"



" وَلَمَّا رَءَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلۡأَحۡزَابَ قَالُواْ هَٰذَا مَا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَصَدَقَ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥۚ وَمَا زَادَهُمۡ إِلَّآ إِيمَٰنٗا وَتَسۡلِيمٗا." (٢٢)


" KUMA A LOKACIN DA MUMINAN (cikinsu) SUKA GA WANNAN RUNDUNA (ta maqiya wacce tazo musu ta samunsu da qasarsu) SAI SUKA CE, " WANNAN SHINE ABINDA ALLAH DA MANZONSA YAYI MANA ALQAWARIN (zai same mu), ALLAH DA MANZONSA YAYI GASKYA. KUMA (ganin wannan runduna) BAI QARA MUSU (komai ba) FACE IMANI DA SALLAMAWA. "



            (AHZAB:22)


Wallahi babu abinda wadannan ayoyi suka nuna min face haqiqanin abinda ya faru cikin Waqi'ar Zaria yadda azzalumai suka dirar musu ta ko'ina. 


Wasu sunyi ta gunaguni, wasu sun tsere, wasu kuma suka dake tare da imanin cewa alqawarin Allah da Manzonsa (S. A. W. W) kawai ake cika musu, domin Jagoransu bai boye musu komai ba. Yace haka hanyar take cikin da muggan jarrabawowi, kuma idan an dake an jure nasara za ta zo a qarshe. 


Kuma har yanzu basu fada abinda suke yi ba don ganin wannan azaba. Tun daga nan nasan wallahi babu masu aikata irin abinda Magabata suka aikata kamar 'yan Shi'ah. Shi yasa irin abinda Allah ya fada cewa zai same yake samun nasu alhali wasunsu sai dai dibar Jar miya a fadar azzalumai. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


8th May, 2021/ 25th Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post