@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KALMAR DA ZA KAJI TAYA YAWAN FITOWA DAGA BAKUNAN MASU KIRAN KANSU MALAMAI
Kun san wasu sun dau addini kamar kayan gidansu ne sai yadda su kaga dama za suyi dashi, sun manta da cewa koda kayan gidansu ne in ba nasu bane basu da ikon yin abinda su kaga dama dashi.
Addinin muslimci addini ne na Allah wanda ya aiko Manzonsa Muhammad (S. A. W. W), kuma ya sharadanta shi dole sai anyi shi kamar yadda Annabi (S. A. W. W) yazo dashi kafin ya zama karbabbe.
Akwai abin takaici maimakon ace ka sami malami yana gargadin almajiransa game da sharri ko illar kafirta 'yan'uwansu musulmi masu furta kalmar shahada sai kaji sune da kansu ke kafirta musulmi. Kuma abin mamakin ma shine ba za ka taba ji suna kawo wani abu game da wadanda kowa yayi shaidar cewa su ba musulmi bane. Ma'ana masu da'awar Kiristanci ko Yahudanci ko Nasarananci.
To, masu wannan hali ku sani cewa Annabi (S. A. W. W) yayi hani game da irin wannan halaye naku, kuma malamanku sun kawo cikin littafansu.
Ga misali nan daga littafan nasu.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
باب ما جاء فيمن رمى أخاه بكفر:
BABI WANDA YAZO KAN WANDA YA JEFI 'DAN'UWANSA DA KAFIRCI.
«2847» حدثنا أحمد بن منيع حدثنا إسحاق بن يوسف الأزرق عن هشام الدستوائي عن يحيى بن أبي كثير عن أبي قلابة عن ثابت بن الضحاك عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: ((ليس على العبد نذر فيما لا يملك ولاعن المؤمن كقاتله ومن قذف مؤمنا بكفر فهو كقاتله ومن قتل نفسه بشيء عذبه الله بما قتل به نفسه يوم القيامة)). وفي الباب عن أبي ذر وابن عمر.
قال أبو عيسى: هذا حديث حسن صحيح.
Ahmad Bn Muni'i ya bamu labari, Ishaq Bn Yusuf Al-Azraq ya bamu labari daga Hishaam Al-Dastuwa'i, daga Yahya Bn Abiy Katheer, daga baban Qilabata, daga Sabit Bn Dhahaak , daga Annabi (S. A. W. W) yace;
" BA HAQQI BANE AKAN BAWA YAYI BAKANCE KAN ABINDA BA MALLAKINSA BA, KO KUMA AKAN MUMINI KAMAR KASHE SHI (yaqarsa). DUK WANDA YA YIWA MUMINI QAZAFI DA KAFIRCI, TO, SHI (mai qazafin) KAMAR MAI YAQARSA NE. KUMA WANDA YA KASHE KANSA DA WANI ABU ALLAH ZAI AZABTAR DASHI DA ABINDA YA KASHE KAN NASA DASHI RANAR ALQIYAMA. "
Abu Isah (Al-Tirmidhi) yace hadisin mai kyau ne kuma ingantacce.
«2848» حدثنا قتيبة عن مالك بن أنس عن عبد الله بن دينار عن ابن عمر عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: ((أيما رجل قال لأخيه كافر فقد باء به أحدهما)). هذا حديث حسن صحيح غريب. ومعنى قوله باء يعني أقر.
Qutaibata ya bamu labari daga Malik Bn Anas, daga Abdullahi Bn Dinaar, daga Ibn Umar, daga Annabi (S. A. W. W) yace;
" DA DAI ACE MUTUM ZAI CEWA 'DAN'UWANSA KAFIRI, TO, DA KUWA 'DAYANSU ZAI DAWO DASHI. "
Imamu Tirmidhi yace, wannan hadisi mai kyau ne kuma ingantacce baqo. Kuma abinda yake nufi da kalmar (BAA'A) dake cikin hadisi shine karmar kafircin za ta tabbata kan wani daga cikinsu.
(SUNAN AL-TIRMIDHI)
Ita furta wannan kalma ya zama shine wani babban makami wajen wasu malaman da suka riqa wanda suke amfani dashi don neman mabiya.
Gaskiya wannan babban kuskure ne, domin don ka kira wani da cewa kafiri ne don kada a fahince shi ba zai hana Allah ya fahintar da mutane abinda yake kira a kansa ba, kuma hakan ba zai sa Allah ya tabbatar dashi kafiri kawai don kai ka kafirta shi ba.
Da ace ra'ayin mutane shine hukunci wajen Allah, to, da ya tabbata cewa Annabi (S. A. W. W) Boka ne Mawaqi kuma Masihirci kamar yadda kafirai suka riqa kiransa da su.
ALLAH YA SHIRYAR DA BATANCE ZUWA KAN TAFARKI MADAIDAICI.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
18th May, 2021/ 7th Shawwal, 1442.