@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
UMAR NE YA FARA GABATAR DA KHUDUBA KAFIN YA HAU MIMBARI
Kamar dai yadda aka san yadda zaben Saqeefah ne ya kasance, anyi mummunan sa-in-sa a tsakanin Sahabbai kafin akai ga yin nasarar tabbatar da Abubakar, domin duk bangare biyu Muhajiruun da Ansar sunso koya ya fitar da shugaba daga cikinsu, yadda ta kai har sai da Umar Bn Khaddab ya kashe Sa'ad Bn Ubadah kafin su kai ga cin nasara.
UHMM, ASHE DAI 'YAN SIYASAR YANZU SUN SAMI WANNAN TAHIRI NE BA A KAIWA KA SAMUN NASARA A ZABE HAR SAI AN ZUBAR DA JINANE.
Allah ya sauwaqa. To, da shike ta hanyar Umar ne yasa Abubakar ya sami wannan matsayi saboda jajircewarsa, sai ya zama Umar din ne ya fara hawa kan Mimbari ya gabatar da Khudubar farko kafin Abubakar ya gabatar da tasa.
Yayi Khuduba mai dauke da Balagha irin tasa wacce duk wanda ya karanta ko yaji sai ya sha mamaki, domin bai taba jin Khuduba irinta ba.
KHUDUBAR UMAR BN KHADDAB
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
حَدَّثَنَا ابْنُ حميد، قال: حَدَّثَنَا سلمة، عن محمد بن إِسْحَاقَ، عَنِ الزُّهْرِيِّ، قَالَ: حَدَّثَنَا أَنَسُ بْنُ مَالِكٍ، قَالَ: لَمَّا بُويِعَ أَبُو بَكْرٍ فِي السَّقِيفَةِ، وَكَانَ الْغَدُ، جَلَسَ أَبُو بَكْرٍ عَلَى الْمِنْبَرِ، فَقَامَ عُمَرُ فَتَكَلَّمَ قَبْلَ أَبِي بَكْرٍ، فَحَمِدَ اللَّهَ وَأَثْنَى عَلَيْهِ بِمَا هُوَ أَهْلُهُ، ثُمَّ قَالَ: أَيُّهَا النَّاسُ، إِنِّي قَدْ كُنْتُ قُلْتُ لَكُمْ بِالأَمْسِ مَقَالَةً مَا كَانَتْ إِلا عَنْ رَأْيِي، وَمَا وَجَدْتُهَا فِي كِتَابِ اللَّهِ، وَلا كَانَتْ عَهْدًا عَهِدَهُ إِلَيَّ رَسُولُ اللَّهِ ص، وَلَكِنِّي قَدْ كُنْتُ أَرَى أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ سَيُدبِرُ أَمْرَنَا، حَتَّى يَكُونَ آخِرَنَا، وَإِنَّ اللَّهَ قَدْ أَبْقَى فِيكُمْ كِتَابَهُ الَّذِي هَدَى بِهِ رَسُولَ اللَّهِ، فَإِنِ اعْتَصَمْتُمْ بِهِ هَدَاكُمُ اللَّهُ لِمَا كَانَ هَدَاهُ لَهُ، وَإِنَّ اللَّهَ قَدْ جَمَعَ أَمْرَكُمْ عَلَى خَيْرِكُمْ، صَاحِبَ رَسُولِ اللَّهِ، وثانِيَ اثْنَيْنِ إِذْ هُما فِي الْغارِ، فَقُومُوا فَبَايِعُوا فَبَايَعَ النَّاسُ أَبَا بَكْرٍ بَيْعَةَ الْعَامَّةِ بَعْدَ بَيْعَةِ السَّقِيفَةِ.
Ibn Humaid ya bamu : Salman ya bamu labari, daga Muhammad Bn Ishaq, daga Zuhriy yace : Anas Bn Malik ya bamu labari yace; Yayin da aka yiwa Abubakar Mubaya'ah a Saqeefah, washegari sai Abubakar ya zauna akan Mimbari, Umar ya miqe yayi magana kafin Abubakar. Yayi godiya ga Allah yayi yabo gare shi da irin abinda ya dace dashi, sa'an nan yace;
" YAA KU MUTANE ! LALLE NI HAQIQA NA FADA MUKU DA YAMMA IRIN ABINDA NA FADA MUKU WACCE BATA KASANCE BA FACE RA'AYINA (ba na Allah da Manzonsa ba), KUMA BA A CIKIN LITTAFIN ALLAH NA SAME TA BA HAKA KUMA BA ANNABI NE YAYI MIN WANNAN ALQAWARI BA, NI DAI KAWAI NA GANI NE KAMAR CEWA MANZON ALLAH ZAI BAR MANA AL'AMRANMU (a hannunmu) HAR YA KASANCE NA QARSHENMU (wanda zai yi shaida a kanmu). KUMA LALLE ALLAH YA BAR MUKU LITTAFINSA A CIKINKU WANDA YA SHIRYAR DA MANZON ALLAH DA SHI, IDAN KUKA YI RIQO DA SHI (shi kadai ba tare da wata sunnar Annabi ba) ZA KU SHIRIYA DASHI SABODA DASHI NE YA SHIRYAR DASHI (Manzon Allah).
KUMA LALLE HAQIQA ALLAH YA TATTARA AL'AMRANKU AKAN WANDA YA FI KU ALKHAIRI, ABOKIN MANZON ALLAH, KUMA NA BIYUN-BIYU YAYIN DA SUKE CIKIN KOGO. SABODA HAKA KU TASHI KUYI MASA MUBAYA'A.
Sai mutane suka yiwa Abubakar mubaya'a, mubaya'ah ta kowa da kowa bayan wacce akayi masa a Saqeefah.
🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
Daga nan sai ya zauna Abubakar ya miqe.
KHUDUBAR ABUBAKAR BN QUHAFATA
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
ثُمَّ تَكَلَّمَ أَبُو بَكْرٍ، فَحَمِدَ اللَّهَ وَأَثْنَى عَلَيْهِ بِالَّذِي هُوَ أَهْلُهُ، ثُمَّ قَالَ:
أَمَّا بَعْدُ أَيُّهَا النَّاسُ، فَإِنِّي قَدْ وُلِّيتُ عَلَيْكُمْ وَلَسْتُ بِخَيْرِكُمْ، فَإِنْ أَحْسَنْتُ فَأَعِينُونِي، وَإِنْ أَسَأْتُ فَقَوِّمُونِي الصِّدْقُ أَمَانَةٌ، وَالْكَذِبُ خِيَانَةٌ، وَالضَّعِيفُ فِيكُمْ قَوِيٌّ عِنْدِي حَتَّى أُرِيحَ عَلَيْهِ حَقَّهُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ، وَالْقَوِيُّ مِنْكُمُ الضَّعِيفُ عِنْدِي حَتَّى آخُذَ الْحَقَّ مِنْهُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ لا يَدَعُ أَحَدٌ مِنْكُمُ الْجِهَادَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، فَإِنَّهُ لا يَدَعُهُ قَوْمٌ إِلا ضَرَبَهُمُ اللَّهُ بِالذُّلِّ، وَلا تَشِيعُ الْفَاحِشَةُ فِي قَوْمٍ إِلا عَمَّهُمُ اللَّهُ بِالْبَلاءِ أَطِيعُونِي مَا أَطَعْتُ اللَّهَ وَرَسُولَهُ، فَإِذَا عَصَيْتُ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَلا طَاعَةَ لِي عَلَيْكُمْ قُومُوا إِلَى صَلاتِكُمْ رَحِمَكُمُ اللَّهُ!
Sa'an nan Abubakar yayi magana, ya godewa Allah kuma yayi yabo gare Shi da irin abinda yafi dacewa da shi, sa'an yace;
" YAA KU MUTANE ! LALLE NI AN SHUGABANTAR DANI A KANKU AMMA BA WAI NA KASANCE MAFI ALKHAIRI A KANKU (kamar yadda Umar ya fada ba). SABODA HAKA IDAN NA KYAUTATA KU TAIMAKE NI, IDAN KUMA NA MUNANA KA QARFAFE NI, ITA GASKIYA ITA CE AMANA, QARYA KUWA HA'INCI CE. RARRAUNA A CIKINKU SHINE MAI QARFI A WAJENA HAI SAI NA QWATO MASA HAQQINSA INSHA ALLAH, KUMA QARQARFA A CIKINKU SHINE RARRAUNA NE A WAJENA HAR SAI NA KARBO HAQQI DAGA GARE SHI INSAH ALLAH !
KADA WANI DAGA CIKINKU YA BAR JIHADI A HANYAR ALLAH, DOMIN MUTANE BA ZA SU BARSHI BA FACE ALLAH YA SAUKAR MUSU DA QASQANCI KUMA ALFASHA BA ZA TA YADU CIKIN JAMA'A BA FACE ALLAH YA GAME SU DA BALA'I. KUYI MIN BIYAYYA MATUQAR INA YIWA ALLAH DA MANZONSA BIYAYYA, KUMA IDAN NA SABAWA ALLAH DA MANZONSA KADA KUYI MIN BIYAYYA.
KU TASHI ZUWA GA SALLAH. !!!
(TARIKUL-'DABARI)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
Tarikh 'Dabari