@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
RANA CE WACCE JAYAYYAR MASU JAYAYYA BA ZAI AMFANAR DASU KOMAI BA
Na san zuwa yanzu da nake rubutun nan ko kake karanta wannan rubutu babu wani mutum daya (1) wanda zai iya bugun qirji yace Buhari adali ne, imma bai ce ba a taba yin azzalumi, mugu, maqetaci kamarsa ba cikin tarihin kafuwar wannan qasa tamu Nigeria.
Ba kamar yadda mutane suka zata ba, a tsammaninsu shine idan ya hau kujerar mulki al'ummar wannan qasa za ta shiga cikin ni'ima, walwala da kuma wadata, sai kuma ya kasance ta fada cikin musifa, bala'i da quncin rayuwa wacce ba a taba yin irinta ba cikin wannan qasa.
To, gaskiya har yanzu ba ka makara ba, domin za ka iya tuba kuma Allah ya karba maka, sannan kuma za ka iya yi masa tawaye kan miyagun ayyukansa da jagorancin da yake yi na zalunci bisa yinyar ba za ka qara daukarsa a matsayin masoyi, jagora ko shugaba adali ba.
Wannan kuwa ita ce damar da kake da ita a yanzu kafin lokaci ya qure maka. Akwai wata rana nanan tafe wacce idan kai ba kayi masa tawaye daga nan duniya ba, to, shi kuma ba zai ji kunyar yi maka ba a ranar alqiyama.
Za kuyi jayayya dashi har ma da zazzarewa juna idanuwa amma jayayyar taku ba za tayi muku amfanin komai ba, domin sai kun gama sannan ace muku dukkanku ku shiga wuta baki daya.
Allah (S. W. A) na fada cikin littafi mai tsarki;
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
" إِذۡ تَبَرَّأَ ٱلَّذِينَ ٱتُّبِعُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُواْ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَ وَتَقَطَّعَتۡ بِهِمُ ٱلۡأَسۡبَابُ." (٦٦١)
" YAYIN DA WADANDA AKA BI (a duniya) ZA SU BARRANTA DAGA WADANDA SUKA BI SU, KUMA SUGA AZABA (qarara ta tunkare su) KUMA (dukkan) WASU HANYOYI (da za su bi su tsira) TA TOSHE MUSU ."
" وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُواْ لَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةٗ فَنَتَبَرَّأَ مِنۡهُمۡ كَمَا تَبَرَّءُواْ مِنَّاۗ كَذَٰلِكَ يُرِيهِمُ ٱللَّهُ أَعۡمَٰلَهُمۡ حَسَرَٰتٍ عَلَيۡهِمۡۖ وَمَا هُم بِخَٰرِجِينَ مِنَ ٱلنَّارِ." (٧٦١)
" SAI WADANDA SUKA BI (masu biyayya ga azzalumai a duniya) SUCE, " DA DAI ACE AKWAI (yiwuwar) KOMAWARMU (duniya) DA MUNYI TAWAYE GARE SU KAMAR YADDA SUKE YI MANA TAWAYE (a yanzu). KAMAR HAKANE ALLAH KE NUNA MUSU (miyagun) AYYUKANSU WANDA SUKA YI HASARA A KANSU, KUMA SU BASU KASANCE MASU FITA DAGA WUTA BA. "
(Suratul-Baqarata :166-167)
A wani guri kuma yake cewa,
" ولو ترى إذ الظالمون موقوفون عند ربهم يرجع بعضهم إلى بعض القول يقول الذين استضعفوا للذين استكبروا لولا أنتم لكنا مؤمنين قال الذين استكبروا للذين استضعفوا أنحن صددناكم عن الهدى بعد إذ جاءكم بل كنتم مجرمين وقال الذين استضعفوا للذين استكبروا بل مكر الليل والنهار إذ تأمروننا أن نكفر بالله ونجعل له أندادا وأسروا الندامة لما رأوا العذاب وجعلنا الأغلال في أعناق الذين كفروا هل يجزون إلا ما كانوا يعلمون »
" KUMA DA ZA KA GANI YAYIN DA AZZALUMAI (shugannin zalunci da mabiyansu) KE TSAYAWA A GABAN UBANGIJINSU SASHENSU NA MAYARWA SASHE MAGANA, RAUNANA (mabiya) NA CEWA MAKANGARA (shugabanninsu), DA BA DON KU BA DAI (wallahi) DA MUN KASANCE MUMINAI. WADANDA SUKA YI GIRMAN KAI (shugabannin) SUKA CEWA RAUNANA (mabiyansu a duniya), " SHIN, MUNE MUKA KANGE KU DAGA (bin) SHIRIYA BAYAN TA ZO MUKU (kuma kun san gaskiyar ce)? KU DAI KAWAI KUN KASANCE MUJIRIMAI (masu laifi).
" KUMA WADANDA AKA RAUNATA (mabiya) SUKA CEWA MAKANGARA (shugabannin nasu), " A'A, BA KUN RIQA (qulla mana) MAKIRCI CIKIN DARE DA RANA KUNA UMARYARMU DA MU KAFIRCEWA ALLAH (ta hanyar halasta jinanan da ya haramta sheqar dashi in ba da wani haqqi ba) KUMA MU SANYA MASA WANI ABIN TARAYYA (wanda shi zai riqa bamu umarni muna bi mu bar nasa ba) ? KUMA SUKA BOYE NADAMA (dukkansu) YAYIN DA SUKA GA AZABA (wacce babu makawa sai sun shige ta). KUMA MUKA SANYA QUQUMI A CIKIN WUYAN WADANDA SUKA KAFIRTA, SHIN, AN SAKA MUSU FACE DA ABINDA SUKA KASANCE SUNA AIKATAWA. "
Kunga anan za ku gama jayayyar taku ta neman kubutar da kai, amma sai kun gama sannan a nuna muku cewa jayayyar taku ta banza ce ! Sannan a kora ku wuta baki dayan ku, kenan jayayyar lahira ko tawayen lahira ba ya amfanar da masu yinsa.
Yayin da kuke ta yin wannan jayayya tsakaninku, a gefe guda kuma Shaidan na sauraronku yana ta yi muku dariyar qeta, domin shi yayi muku sanadin wannan makoma.
Idan aka kai ku wutar sai shi kuma Shaidan din ya fito yana yi muku dariya da maganar ban haushi da qara cusa muku baqin ciki yana cewa ;
" وَقَالَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَمَّا قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ إِنَّ ٱللَّهَ وَعَدَكُمۡ وَعۡدَ ٱلۡحَقِّ وَوَعَدتُّكُمۡ فَأَخۡلَفۡتُكُمۡۖ وَمَا كَانَ لِيَ عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنٍ إِلَّآ أَن دَعَوۡتُكُمۡ فَٱسۡتَجَبۡتُمۡ لِيۖ فَلَا تَلُومُونِي وَلُومُوٓاْ أَنفُسَكُمۖ مَّآ أَنَا۠ بِمُصۡرِخِكُمۡ وَمَآ أَنتُم بِمُصۡرِخِيَّ إِنِّي كَفَرۡتُ بِمَآ أَشۡرَكۡتُمُونِ مِن قَبۡلُۗ إِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ ." (٢٢)
" KUMA SHAIDAN YAYIN DA AKA QARE AL'AMARI (na hukunci tsakaninku da su Bukharin) SAI YACE, " AI LALLE ALLAH YAYI MUKU ALQAWARIN GASKIYA (kan cewa duk wanda yayi zalunci da wanda ya bi azzaluman wuta za a kai su), SAI KUMA NI NAYI MUKU IRIN NAWA ALQAWARIN (na qarya da rudu) SAI NA SABAR MUKU. AMMA FA (ku sani) NI BANI DA WANI IKO A KANKU (na tilastawa) SAI DAI KAWAI NA KIRA KU NE (kan bata) KU KUMA KUKA AMSA MIN (bisa zabin kanku ba bisa tilasci ba). SABODA HAKA KADA KU ZARGI NI (kan kiran da nayi muku), KU ZARGI KANKU (kawai da kuka bi son zuciyarku ta hanyar yimin biyayya kuka bar wanda ya halicce ku). NI BAN KASANCE MAI AMFANAR DAKU (a wannan rana ba) KUMA KU MA BAKU KASANCE MASU AMFANAR DANI BA, (ai dama) NI NAYI MUKU TAWAYE KAN ABINDA KUKE HADAWA DANI TUN KAFIN WANNAN LOKACI, LALLE GARE SU AKWAI AZABA MAI RADADI !"
(Suratul-Ibrahim:22)
Wannan dai shine sakamakon ku dasu a lahira matuqar ba kuyi musu tawaye kuma kun tuba ga Allah ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
5th May, 2021/ 23rd Ramadan, 1442.