Ka Shagaltu Da Ganin Laifin Kanka, Akan Ganin Na Wani !


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


WANDA KE MU'AMALA DA MA'ABOTA ILIMI DA HIKIMA YA RABAUTA 


Cikin kwadaitarwa da Manzon Allah (S. A. W. W) ke yi mana don mu sami rabo a duniya da lahira ya kwadaitar damu abubuwa guda hudu (4) wadanda za mu ambata cikin wannan hadisi dake tafe. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



 قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ‏ طُوبَى لِمَنْ شَغَلَهُ عَيْبُهُ عَنْ عُيُوبِ غَيْرِهِ وَ 

أَنْفَقَ مَا اكْتَسَبَ فِي غَيْرِ مَعْصِيَةٍ وَ رَحِمَ أَهْلَ الضَّعْفِ وَ الْمَسْكَنَةِ وَ خَالَطَ أَهْلَ الْفِقْهِ وَ الْحِكْمَةِ



بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 206


Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa; 


" DADI YA TABBATA GA WANDA AIBOBINSA SUKA SHAGALTAR DASHI DAGA (ganin) AIBOBIN WANINSA, KUMA YA CIYAR DA ABINDA YA TARA BA TA HANYAR SABO BA, KUMA YA TAUSAYAWA MA'ABOTA RAUNI (weak) DA TALAUCI (poors), SANNAN KUMA YA CUDANYA DA MA'ABOTA ILIMI DA HIKIMA. "


            (Biharul-Anwar )


                     DARASI

               ------------------------


(1)- Wanda ya shagaltu da kallon kura-kuransa fiye da hangen laifin wani zai kasance mai gyara su tare da aikata abinda ake so ya aikata don neman lahirarsa. Hangen laifin wani ko gazawarsa a kullum bai cika amfanar da mai hangen ba, domin zai riqa ganin kansa tamkar wanda yake kan daidai ne a kullum. 


(2)- Neman halal da ciyar da ita ta hanyar da Allah ke sa kawar da fushin Allah akan mutum, sannan kuma yana sanya albarka cikinta komai qanqantarta.


(3)-Duk wanda ke tausayawa raunana (weeks) da ma'abota talauci Allah zai tausaya masa fiye da yadda yake tausaya musu. Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa; 


" KU TAUSAYAWA WADANDA KE DORON QASA SAI WANDA KE CIKIN SAMA (Allah) YA TAUSAYA MUKU. "


(4)-Duk wanda ke kasancewa tare da ma'abota ilimi da hikima zai kasance cikin alkhairori a kullum, domin shi ilimi yana kira ne zuwa ga aikata alkhairi.


YA ALLAH KA DATAR DAMU WAJEN KALLON GAZAWARMU FIYE DA KALLON GAZAWAR WASUNMU 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


         (08137925034)


28th May, 2021/ 17th Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post