Idan Kuna Son Kasashen Larabawa Suyi Faɗa Da Isra’ila, Ku Faɗa Musu Isra’ila Ta Koma Zuwa Shi’a, Cewar Malamin Ahlus-Sunnah Ɗan Ƙasar Labanon


 

Wani malamim Ahlus-Sunnah dan Kasar Labanon mai suna Sheikh Maher Hammoud ya bayyana cewa, "idan kuna son Kasashen Larabawa suyi fada da Isra’ila, ku fada musu Isra’ila ta koma zuwa Shi’a".


Wannan ya biyo bayan hare-hare da Isra'ila ke ta kaiwa kan raunanan Falastinawa, amma ƙasashen Larabawa sunyi gum da bakunansu. Sai kasar Shi'a ne, ƙasar Iran ke tallafa musu hadi da sauran ƙasashen duniya masu kishin ɗan adamtaka.


Malamim ya fadi haka ne domin ya wayar da kan mutane kan damuwar kasashen larabawa, sufa damuwarsu har yanzu na qungiyanci ne.


Ba tare da duba cewa, ita Isra'ila ba yana fada da kowa bane sai musulunci. Palastinawa ba Yan Shi'a ne zalla ba, akwai Kiristoci, Musulmi Ahlus-Sunnah, da Kuma Shi'a, duk akwaisu a kasar.


Amma basu kai duba ga hakan ba, don sun gina kansu akan qabilanci.




Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post