Idan Alkawarin Allah yazo Za Mu Zo Daku Jama'a-Jama'a ..!!

 


YAHUDU ZA SU MAMAYE YANKIN PALESTINE  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


IDAN ALQAWARIN ALLAH YAZO ZA MU ZO DAKU JAMA'A-JAMA'A 


Yankin Palestine guri ne mai daraja wanda Allah (T) ya fifita shi ta hanyar fitar da Annabawa (A. S), sannan kuma ya tara su gaba dayansu bayan mutuwarsu domin fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W) ya jagorance su sallah. 


Nan ne alqiblar musulmi ta farko wanda Allah (T) ya umarci Annabi (S. A. W. W) da masu Imami su fuskance shi wajen sallah, sannan daga baya aka juyar dasu zuwa ga Masjidul-Haram. 


Akwai riwaya wacce ke cewa Yahudawa zasu hade bayan rarrabuwar da suka yi, kuma za su taru gaba dayansu su hada qarfinsu a Palestine  domin tunkarar muslimci da musulmi. 


Sanin wannan tarihi dake cikin littafansu yasa dukkan Yahudawa na kowanne yanki yake qaunar yankin Palestine da kuma qoqarin kawar da duk wanda ba Bayahude bane daga yankin don su sami gurin zama su mamaye yankin. 


Bayan hadewarsu za a fafata yaqi tsakaninsu da musulmai inda musulmi za su taru a gabar gabas,  Yahudawa kuma suna akan gabar yamma daga kogin Urdun. Anan guri ne za fafata yaqi wanda zaiyi sanadin shafe Yahudawa, ko da Bayahude ya buya a bayan Bishiya ne za ta kira musulmi tace ga wani Bayahude ya buya a bayana. 


A wannan lokaci ne musulmi za su dawo cikin 'yanci bayan korar da akayi musu daga yankin. Wannan kuwa na daga cikin alamomin tashin alqiyama. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" وَقُلۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ لِبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱسۡكُنُواْ ٱلۡأَرۡضَ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ ٱلۡأٓخِرَةِ جِئۡنَا بِكُمۡ لَفِيفٗا." ٤٠١


" KUMA DAGA BAYANSA  MUKA CE GA BANI ISRA'ILA , " KU ZAUNA CIKIN QASAR. SA'AN NAN IDAN WA'ADIN QARSHE YAZO ZA MU JE DAKU JAMA'A-JAMA'A. "


(SURATUL-ISRA'I, 104)



Duk abinda kuke gani Yahudawa na yi kan raunanan musulmin yankin Palestine suna yi ne bisa iliminsu na sanin wannan tarihin dake cikin littafinsu. Su kuma musulmi sun kasa fahintar wannan al'amari sai suke gani kamar wani abin wasa ne , sai dai kawai qalilan daga cikinsu wadanda suka san hakan.


Palestine haqqi ne kuma mallaki na dukkan musulmi wanda ya kamata ace sunyi fafutukar riqe kayansu da bashi kariya daga shiga hannun Yahudawa, amma sai ya zama kamar wani abu ne wanda ya kebanta ga wani bangare na musulmi. Saboda haka aka bari ana ta karkashe su ba bisa wani haqqi ba. 


Wajibin da ya hau kanmu shine mu taimakawa wadannan raunana mazauna yankin Palestine wadanda ake karkashesu ba bisa wani laifi da suka aikata ba. Su kuma suka dake suna yin aiki a madadinmu baki daya  !


Ta kowacce hanya za a iya taimaka musu, masu qarfin makamai su aika musu, wasu su taimaka musu ta bangaren aika musu da abinci, wasu kuma ta hanyar tura musu kudi ta hanyar amintaccen account wanda zai je gare su. 


Tura kudi ta account ba zai zama abin mamaki ba ga dan Nigeria, domin sun riqa tura shi a banza ma don taimakawa azzalumi Buhari yayin campaign nasa a zangon farko. 


Taimakonsu ta hanyar addu'a ma ba qaramar hanya bace, domin ko Annabawa (A. S) da suke yaqi sun riqa yin addu'o'i don neman taimakon Allah. Rubutu ma zai iya zama hanyar taimaka musu, domin suna gani kuma yana qara musu qwarin gwiwa na cewa ashe akwai wadanda zuciyarsu na tare dasu, kamar dai yadda Yahudawa ke jin haushi in sunga wani rubutu ko gangami wanda ke nuna zakuncinsu akan Palastinawa. 


YAA ALLAH KA TAIMAKI MUSULMI DA MUSLIMCI A DUK INDA SUKE.


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


22nd May, 2021/  11th Shawwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post